Skip to content

Chapter 107

Chapter 107

Bakar Taada Book One Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

baka ji". Ya bada yaron ya fice ba tare da ya sake ce wa komai ba. Kwana na yi da yini sannan aka sallame mu. Yara lafiyarsu k'alau. Kai tsaye gida aka zarce da mu. A dakin Gwaggo muke yin jego. Hidima kan hidima Tijjani da mahaifiyarsa suke yi. Har sai da Baban Marina ya ce "Ka bi a sannu Tijjani kada ka yi bashi". Tun kafin ranar suna aka lankayawa Yusuf(Hanif). Muhammad Sani kuma (Hamim) Har ranar suna ta zo aka yi taron sunan tagwaye cikin rufin asiri. Na yi kwalliya da leshi, da kuma kyawawan sabbin material din Umm Nihla.... Har kala biyu. Kyaunsu da sau'kinsu ya sanya Tijjani ya siya mini kala biyu. Leshi kuwa a cikin na lefena na dauka na dinka. Fayyace irin kayan da muka samu ni da yan biyu bata lokaci ne. Domin gadajen Gwaggo duka biyu sai da suka cika da kayayyakin barka. Babbar matsalar da ta fara damuna rashin warke wa ta. Tafiya ta a bubbude. Na je asibiti sun ware d'inkin. Suka ce na dinga kama ruwa da ruwan dumi da dan gishiri a ciki zan warke. Sosai Gwaggo take kula da ni. mun warware mun ciko ni da yara. Na murje tamkar ba yara biyu nake shayarwa ba. Matsala biyu ke damuna ta farko kukan yara. Domin idan dare ya fara nisa suka fara kuka, babu me yin barci a k'ofarmu. Da daya ya fara, d'ayan ma zai dauka, su taru su kidamamu. Basa dainawa sai an yi assalatu. Dada kuwa sai fadi take yi "Ai kuka ma basu fara ba, tunda an riga an yi musu sanadin wahala. Waye zai sha mataccen nono ya share k'alau?" Matsalar ta gaba kuma nake jin na bu'de. Ina jin yadda iska ke shigata. Nasan na karu amma ban yi zaton dinkin ba zai ha'de ni ba. Ga shi ban fasa kama ruwa da ruwan zafi ba. Na kasa jin da'din kaina. Na kasa fa'dawa Gwaggo. Yaya Ummi na zuwa na fa'da mata. Ta ce "na sa a kawo sassake da saiwowi kalakala da ake kawo wa daga chadi." A kunya ce na ce "Na gode. Kwana biyu a tskani sai ga ta dawo da kayan. Da kanta ta dafa mini, ta ware mini butar da zan dinga zuba maganin. Dan kama ruwan da na yi da ruwan maganin har na fara jin da'din jikina. Da zata tafi ta hada kan kayanta ta tafi da su. Ina son na ce ta bani koren maganin da na dafa kazar, amma na kasa a dalilin kunya ta yi mini k'awanya. Na tuna ranar sunan Ubaida yadda su Nasiba da su Maijida suke koda kyaun kayan da suke siya daga Kano ta hannun Yaya Ummi. Na tuna sadda ta bani ina amarya na ki kar'ba. *Masu bu'katar kayan gyara na chadi gangariya, su yi mini magana. 08032773332* Amma da yake Yaya Ummi yar'uwa ce ta gaske sai da ta bani kayan nan duka. Kazar ma ta ce zata daho mini idan na kusa arba'in. Cikin dabara na kirgi ku'din da na samu a barka na sawa y'arta mai d'an dama a aljihunta. A haka na kwashe sati hud'u da haihuwa. Tijjani ya fara rawar kai da son na koma gidanmu haka nan. Tunda na warware. Idan ya fara wannan maganar shiriritar da ita nake yi. Da safe an yiwa yara wanka suna ta barci tamkar basu ne masu kwana ido biyu suna kuka mai tsananin gaske ba. Amma da gari ya waye ba za'a sake jin motsinsu ba. Yini suke suna barci. Ranar da muka yi kwanaki talatin ya iso daga Bauchi. Ya zaune kan sallaya a tsakar d'akin Gwaggo. Ya ci abincin da aka kawo masa. Ya kalle ni ya ce "Little ki girmama al'kawari. Ba irin cika bakin da baki yi mini ba akan idan kin haifi namiji suna na mussaman zaki saka mini. Cikin ikon Ubangiji kin haifo har biyu amma har yau ban ji sunan nawa ba. Anya kin yi daidai kuwa?" Na dauke kai ina murmushin kunya. Tare da ce wa "gaggawa ne da kai. Ka bari sai mun koma gidanmu zan fara fa'da maka." Ya yi murmushi ya ce "Gaskiya na matsu fa'da mini na ji kawai". Na yi dariya na yi shiru. Ya zuba mini ido sosai ya ce "So nake ku koma, mu yi kwanaki ka'dan kafin mu fara ha'da kayanmu. Kin san mun kusa cika wa'adin kudinmu. Bazan sake biya ba. Idan na samu dama a Bauchi nake son na samu k'aramin gida mu koma can. Zirga zirgar zata mini yawa ga tsadar ku'din mota. Zan fa'da wa su Baba zamu k'aura zuwa Bauchi." A sanyaye na ce "Allah ya k'ara budi." Domin na shiga zullumin yadda zan rasa jama'ar da nake da ita, tunda bazan samu jama'a a Bauchi kamar yadda na yi shura a Toro ba. Ya ce "Ameen Asiyata! Amma fa ban bar waccar maganar ba. Dai-dai lokacin Haneef ya fara kuka da alamun razana ya yi. Da azama ya dauko shi, ya shiga tofa masa addu'a. Sai kuwa ya yi shiru. Ya bu'de idonsa kirr yana kallon Babansa. Da murmushi Tijjani ya ce "Halo Babana, how you doing today?" Na murmusa na ce "Kana jiran amsa ne?" Ya ce "ko bai amsa ba, ya ji ni. Yasan yana tare da Babansa ba ki ga ya yi shiru ba?" Na ce "Hakane". Daga hakan ya tsoma hannu a baki ya fara tsotso. Tijjani ya ce "shima shan hannu ya fara?" Na ce "Eh! Shi ne ma yake yi kawai. Hamim din da ya fara, yanzu ya gane nono, baya yarda ya sha hannu, wannan yafi shi hakuri". Ya d'aga shi ya ce "To ba shi ya sha kada a dinga amfani da hakurinsa ana barinsa da yunwa." Na karb'e shi na gyara na fara shayar da shi. Tijjani ya tsura mini ido yana kallon yadda k'irjina suka cika, suna tsaye tunda k'ananu ne. Ya kasa hakuri ya dauko Hamim da yake barcinsa ya ce "Ka ji Momi ta ce "Ba ka da hakuri. Baban Marina da ka ci sunansa kuwa hakurinsa mai yawa ne". Shi bai bu'de ido ba. Barcinsa kawai yake yi. Ya ce "Ta shi kai ma ka sha". Na ce "kana shigowa, ina kwantar da shi. A koshe yake." Ya kankace ido ya ce "Ba kya kewata ko little?" Na ji kunya irin sosai. Na kawar da fuskata ba tare da na ce kanzil ba. Ya yi kasa da murya ya ce "Na yi matu'kar gajiya. Na matsu sosai". Na kasa amsa masa. Ya sake ce wa "Yaushe Baba ya ce zaki koma?". Murya babu amo na ce "idan mun yi arba'in mana. Ai yanzu ma saboda kukan yaran nan ne ya barmu da ana yin sati uku zai tattaramu." Ya nisa ya ce "Idan ta kukansu ne ai zan iya da su Asiyata." Na yi dariya na ce "baka san kalar kukan da suke yi ba ne." Ya ce "Da gaske nake yi miki, zan bar komai na ji da su. Kinsan yadda nake jinsu a raina kuwa?" Na girgiza kai na ce "Ina zan sani? Amma ni da su waye a gaba?" Ya tillike da dariya sosai ya ce "Yanzu kishin ki har da y'ay'an ki Asiya?". Na

Table of Contents

Chapters

161 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161