Chapter 139
Chapter 139
yi. Gwaggo ce bata um bata um tunda ta yi jaje cikin rauni da kasala bata sake iya magana ba. Muna kallo da lokacin da suka bamu ya cika suka iza keyarsa hannunsa dauke da ankwa tamkar kasurgumin mai laifi. Ni dai har muka dawo BAUCHI ban iya daina kuka ba. Tun ana bani bakin na yi shiru har aka zuba mini ido. Maimakon mu yada zango a BAUCHI sai Baba ya ce a wuce Toro kawai. A k'ofar gida muka tarar da su Baban Tsakiya. Na kalle su na gasgata ce wa Baban Marina ne kawai ubanmu. Ba wanda ya bi bayan Tijjani ko na ahalinsa a cikinsu. Dukkanmu a gaban Dada muka zube tamkar masu neman gafara. Tana kuka, matan cikinmu muna yi, tamkar dai mutuwar fuju'a Tijjani ya yi. *INA MUKU ALBISHIR AKWAI DUKKAN TSOFAFFIN LITTAFAN MARUBUCIYA HAJIYA SALIHA ABUBAKAR ZARIA* *ZAKU SAME SU SOFT COPIES A HANNUNA. *SABO LITTAFIN TA ZAI ZO BA DA JIMAWA BA* Sai ta dauko salatil fathi sai ta rikice ta dauko ashafa da k'yar dai ta fara karanta casa'a ta sauke ta. Tana yi tana ce wa "Rabbani a saukakawa mai babban suna, a tausayawa wadannan y'aya' nasa". Da k'yar Baban Marina ya hakurkurtar da mu aka daina kukan. A dakin Gwaggo na yada zango. Dakin da nake matukar samun nutsuwa a cikinsa. Amma a yau sai na ji ina cikin matsanancin kunci da zullimi domin sai nake ganin tamkar ana shirin raba ni da Tijjani ne. Na ga tsayin wannan dare tamkar dai ace gawa ce a dakin. Ban yi barci ba. Karfe uku na ga Gwaggo ta fita ta dauro alwallah. Duk yadda na ke cikin zullimi sai da na tuna irin wannan yanayin muka shiga a lokacin da aka zartar mini da hukuncin auren Bulkachuwa. Yau kuma ina kukan bak'in cikin nisanta ni da gidansa da aka yi. Gwaggo tana shigowa da alwalarta, nima na zabura na mik'e na doro alwalar. Muka dinga nafila muna shigar da bukatunmu. Ina kuka hannuwana na sama "Tijjani, Tijjani kawai nake iya fad'a gabad'aya kaina ya kulle. Domin dawo da ni gida ya yi matukar sake tsorata ni. Me yasa za'a raba ni da dakina? Kwanaki biyu kacal a gidan Marina na gane masu farinciki yadda na shiga cikin garari sun rinjayi masu tausayi da rarrashina. A k'ofarmu kam babu wanda yake takura mini ko habaici. Amma da zarar na fita da NIYYAR zuwa wajen Dada sai na samu wanda ya yi mini yarfe ana mini habaicin dama karyar arzikin da a muke yi ba mai tsarki ba ne. Har ta kai bana k'aunar na fita. Amma idan ban je ba sai ta aiko wai na je, a wannan lokacin k'warai Dada take tausayina ni da yara. Kullum a cikin sadaka da addu'a take yiwa Tijjani. Kuka kam bansan wa yafi yi a tsakaninmu ba. Ta damu k'warai har jininta ya hau. Ban sake samun damar gano Tijjani ba har aka yi sati da zuwanmu. A lokacin kuma na fara gazawa. Tashin hankalina na sake hauhawa. Baban Kasuwa da na Tsakiya babu wanda ya tako kafarsa da nufin yi mini jaje. Ashe wai na yi laifi da ban bisu kofofinsu na gaishe su tare da yi musu jaje tunda ai su d'ansu ne tun kafin ya zama mijina. Ni luma damuwata ta girmi tunanin zuwa gaishe gaishe. Sannan mafi yawa a wajen Dada nake ganinsu na kuma gaishe su a mutunce. A lokacin na sake fahimta tare da gasgata idan Baban Marina ya kauce bamu da wanda zai tsaya kai da fata ya tallafemu idan mun shiga cikin kalubalen rayuwa. Tausayin k'ananun y'aya'n Baban Marina ya sake rub'anya tashin hankalina. Gabadaya na zama tamkar wata zararriya, na k'are na fige tamkar kudin guzuri. Bayan addu'ar da nake yi wa Tijjani da y'aya'na, sai na sake tsananta addu'ar Ubangiji ya sanya soyayya da tausayi mai yawa a tsakanin y'aya'n Baban Marina. Domin kam al'amarin Baffaninmu sai shukuran. Kullum mutuwa na daukarmu daya bayan d'aya amma bata zame musu izna ba. Abin da na sake fahimta kawai shaidan da son zuciya gami da hassada ne suka yiwa zumuncin yau k'awanya. Sassaucin rayuwar da Baban Marina ya samu a dalilin y'aya'n sa ya zama wani abin tattaunawa. Kullum a cikin fad'in ai yanzu ya farfado suke. Na tabbatar ba za'a bar ni na ji da ibtilain da ya fad'o mana ba, sai an tusa ni gaba da muzanci kala kala. Dan haka na kudire da na yi sati biyu zan fad'awa Baban Marina zan koma dakina tunda dai Tijjani bai mutu ba. Washagari muka tafi Kano da ni da Nazira da Yaya Salisu. Gabadaya Tijjani ya fita a hayyacinsa. Ina kuka nake fad'in "Basa baka abinci ko?" Ya girgiza kai ya ce "Abin nan da nake fad'a miki. Da zarar hantsi ko yamma, ta yi sai gabad'aya na rikice, zuciyata kamar ta yi bindiga wajen son na tafi Toro na ga Nasiba. Masifar zafin da nake ji a zuciyata da kirjina ya wuce misali ina fatan na mutu kawai Asiya". Na kasa ce wa komai. Yaya Salisu ya ce "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun! Allah mun tuba." Nazira kuwa kuka take yi tana fad'in "Dama nasan ba haka siddan ka runtse ido ka kafe sai ka aure ta ba." Ni kuwa na zama tamkar mutum mutumi. Domin a yanzu na yarda Tijjani na bukatar na samar masa da nutsuwa. Tunda duk yadda yake cikin wannan tashin hankalin amma yana fad'in yadda yake ji game da al'amarin ta. Na tabbatar ba son zuciya ko tozarci ba ne ya sanya yake fad'a mini yadda yake ji akan Nasiba ba. Cikin tausayi nake kallon sa gabad'aya ya zube, ya yi duhu. Tausayi, so, kauna suka sake yi mini rubdugu a dukkan zuciyata da gangar jikina. Murya a tausashe na ce "Ka tsananta addu'a ka kuma yi hak'uri. Da kaina zan kawo ta ka ganta". Ya zuba mini ya ce "Yaushe?" Na ce "Gobe ko jibi". Ya yi k'asa da kansa ya ce "Goben dai." Da k'arfin hali na ce "To". Ya kidime ya ce "Wanne irin to kike nufi Asiya?" Na ce na gaskiya da gaskiyar magana ". Ya saki ajiyar zuciyar samun nutsuwa ya ce "Ina twins, me ya hana ki zo da su na gansu?" Idona cike da k'walla na ce "makaranta suka bi yaran gidan." Haka muka ba shi abin da zamu ba shi. Aka tafi da shi. Tuni kuma an saka ranar da za'a gurfanar da shi gaban kotu. Sai dai Yaya Ammar ya tabbatar mana BAUCHI za'a dawo da shi. Tunda a cikin jahar Bauchi aka kama shi. Ba'a san dalilinsu na kawo shi Kano ba tare da sun sanarwa da kowa nasa ba har tsayin kwanaki biyu. Da yammaci sosai muka isa Toro. Muka tarar da Nasiba a k'ofar Dada domin mijin babarta aka kwantar a asibitin koyarwa na jamiar Jos. Lokacin da abin ya faru tana can bata dawo ba, sai yau aka sallame su. Babar tata ta wuce gidanta da marar lafiya. Ni da Nazira muna kallon yadda gabadaya ta takure ta kasa sakat tunda muka shiga. Akwai alamun tasku a tare da ita. Na yi jarumtar ce wa "Nasiba Bulkachuwa na ta jajen ki. Ya damu da rashin ganinki
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161