Skip to content

Chapter 55

Chapter 55

Bakar Taada Book One Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

daddawa, man shanu, nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya* *08039183880* ✍️ *WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE BIYA KUDIN KARATUN KI TA WANNAN ASUSUN DAN GUJE WA BAKAR TA'ADA!* *REGULAR 500* *VIP 1K* *VIA* *2384876855* *SURAYYA IBRAHIM DAHIRU* *ZENITH BANK* *KO* *7061488065* *SURAYYA DAHIRU IBRAHIM* *OPAY DIGITAL SERVICES*. *TURA SHAIDAR BIYA TA WADANNAN LAMBABOBIN* *08032773332* *09069067488*. *Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki* *Maganin sanyi* *Saiwowin Tsumi* *Saiwowin dahuwar kaza* *Saiwowin dahuwar tattabaru* *Gumba* *Tsumin kwakwa* *Y'aya'n gadali* *Hadadden daka*. *Tsugunno mai sa a matse* *Goran tula* *Goran tula syrup* *Garin goran tula*. *Maganin gyaran nono*. *Zuma ta mussaman*. *Tsumi*. *Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*. *Domin kuwa asalin saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*. *Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntube ni dan samun naku kayan cikin sauki da mututantawa. Ina aikawa ko ina a fad'in tarairaiyar Nijeriya* *08032773332* *Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko Kuma kina sha'awar yin register da su*. *Ki tuntubemi babbar dealer din su Aisha lame* *Ina kuma fad'a muku akwai da daddan ganyen shayi na Lame Tea* *Akwai pop corn* *07036662633* Ya girgiza kai, bai ce uffan ba, ya tashi ya kwashi kayan abincin ya nufi kicin da su. Ina hangen sa ya dauko farantai ya juye kayan miya da ya barsu a tsakar gida. Ashe har da doya guda uku manya. Sai da ya jide ya adana komai. Sannan ya daga murya ya ce "Zan je sallar isha." Bai jira amsata ba yasa kai ya fita. Na tokara na dauro alwallah dan nima na sallaci isha. Na idar na jima a zaune sannan na shiga daki na yi shirin wanka. Na fito na shirya a nutse. Na dawo falo da nufin na sha ruwa. Aka dawo da wuta. Na kalli receiver dokin a ha'da mini ita ya kama ni. Ina tsaye na gan shi ya dawo, na tsinci kaina da lekensa ta windo. Na ganshi da bargo irin mai sau'kin ku'di da kuma pilo guda daya. Kai tsaye dakin da kayansa suke ciki ya shiga da su. Na dan ji wani iri. Na tsinci kaina da tambayar kaina da cewar wato bai damu sai ya zo dakina ba. Duk da k'arancin shekaruna ni din ma'abociyar karatun littafan Hausa ce mussaman da nake da babbar waya nake karatun littafan online. Ina ganin yanayin yadda angwaye basa daga kafa a wannan fagen. Sannan da yawa an yiwa kawayenmu aure da muka kammala k'aramar sakandire, muna jin labarin zumudin angwaye. Amma shi wannan ko oho. Nan da da nan zuciyata ta baci a dalilin na hakaito*BAKAR TA'ADAR* Da ya saba yake yi! Na ji tsanarsa ta sake tsananta a zuciyata. Na dinga jan tsaki. A haka ya shigo ya same ni. Ya miko mini leda ya ce "Ga shi". Na juya baya ba tare da na kalle shi ba, bare na kar'ba. Ya iso kusa da ni ta yadda muke jin hucin juna. Kamshina ya mamaye wajen, da ace yana shafa turare da sun cakude sun bada kamshi na mussaman. Baya wari, amma kuma ana dan jin tsamin maza ka'dan a tare da shi, wanda rashin tu'amalli da turare ke sababawa. Takaici ya sake k'ume ni. Hawaye ya cika mini ido. Ya nazarce ni. Ya nisa ya ce "Wai menene haka kike mini? Tsabar tsanarsa sai na ji hucin bakinsa mai bashi ne. Zuciyata ta taso na ji tamkar na sheka amai. Na fa'di kan kujerar da bayana na fashe da kuka sosai. Ya matso da sauri da nufin rike ni, na k'walla k'ara sosai. Ya yi maza ya janye hannunsa ya fasa. Ya sassauta ya ce "ki daina yi mini irin haka Asiya. Ubangiji ya sanya mini k'yamar na ji kukanki. Fa'da mini me nake yi miki?" Tsawon lokaci yana dakon amsa ta. Ya kosa da shiruna ya ce "Ki yi ha'kuri komai zai dai-daita mana". Cikin matsanancin kuka na ce "Wallahi ba zai daidaita ba. A hakan ne komai zai dai- daita? Dube ka dan Allah! Ni gaba'daya baka burge ni". Ya murmusa ka'dan, ya mike ya ce "Wata rana zan burge ki In sha Allah". Har ya kai bakin kofa ya ce "Ki ci nama ne, idan kuma ba zaki ci yanzu ba, ki bu'de shi domin akwai albasa a ciki kada ta lalata shi. Ki kara ha'kuri Asiya". Ina ganin ya fice na dinga kuka sosai mai dafa zuciya. Ina jinsa yana ta kiciniyar jawo ruwa a rijiya. Bayan kamar mintina talatin ya dawo ya zauna kusa da ni. K'amshin sabulun wanka kawai na ji a tare da shi ba na turare ba. Cikin rarrashi ya ce "Kuka har yanzu Asiya? Ba zaki yi hakuri ba! Ko wanne bawa da kaddararsa, ba ke ka'dai ba ce, ki tsananta addu'a." Cikin kuka na ce "Addu'a sau milyan nawa zan yi? Ai kaine matsala ta ni kam." Ya yi shiru can ya ce "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun! Na mike da sauri na bar shi a wajen. Ina shiga d'akin na rufe kofar da k'arfin gaske. Na jima kafin barci ya sure ni. Bansan yadda ya kare a inda na bar shi ba. Washagari kuwa tunda na yi alwallah da asuba da na rufe kofata har shad'aya ina kwance duk da ba barci nake yi ba. Sau biyu yana kwankwasa k'ofar. Amma na share shi. Ban fita ba sai wajen shabiyu da rabi. Shima uzzirin shiga band'aki ne ya uzzira mini. Kan dole na yi shirin wanka. Na fito na tarar da shi a saman katanga yana ta daura kwanon setelite. Ya ha'da zufa sharkaf. Na ja tsaki na shige band'aki. Abin mamaki sai na tarar bayan robar band'akin da take a cike. Ya cika mini botikin wanka ya ajiye a inda ya saba ajiye mini. Na yi shiru ina wasi-wasin yadda saurin fishi irin na Bulkachuwa baya yin tasiri akan sha'anina. Na hakaito yadda yake ta ha'da zufa wanda na tabbatar dan ni yake yi. Abin da nake ji mai kama da tausayinsa ya sake tsananta a tare da ni. Bansan me yasa idan yana kusa da ni nake jin zafinsa ba. Amma ga dukkan alamu rashin iya wanka da gayunsa na cikin cikas dinsa a wajena. Na gama uzzirin na yi wanka sosai. Sadda na fito a falo na hango shi ya kunna talabijin yana ta kokarin saita tashoshi. Na shirya tsaf. Kamshina ya cika dakin. Na hau kakkade dakin. Haka kawai sai na ji tamkar ana kallona. Na juyo ai kuwa sai ganinsa na yi yana jingine da bango ya yi mini zuru. Na b'ata fuska na juya na cigaba da aikina. Ya shigo ya ce "Asiya me zan miki ki daina mua'amalanta ta irin haka? Ko arzikin gaisuwa bani da shi a wajen ki? Me ya yi zafi ne?" Na share shi. Ya tausasa harshe ya ce "Burodi na siyo. Na dafa shayi, na kawo nan, ko zaki fito falo? Da kin daure ma, sai ki zo falon kina karyawa kina kallon tashar da kike so". Ban d'ago ba, na ce "Kallo bai dame ni ba." Ya yi shiru na sakwanni sannan ya saki ajiyar zuciya ya ce "Bari na kawo miki nan to". Ya fita ba tare da ya jira amsa ta ba. Bai jima

Table of Contents

Chapters

161 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161