Chapter 80
Chapter 80
koma ruwa ya ce "Nasiba ce asarrariyar Asiya?" Na fizge kafata na tashi. Na ce "Ina dalilin gatsa sunan matar wani ne Tijjani? Kusan mintina ashirin da yin maganar ashe duk yadda na barka kake yin yadda kake so da sunan shafar mai, zuciyarka na tunanin suntumemiyar halitta ko? Wallahi bazan iya da bala'in ka ba Tijjani! Ganin da gaske na fitittike, zan birkice masa. Jikinsa na bari ya ce "Allah ya baki ha'kuri, na yi kuskure. Sai dai ya kamata ki mini shaidar tun ma kafin a mini babban alherin ba ni auren ki ai na fita a dukkan sha'aninta. Bare kuma yanzu da take matar wani. Dan Allah mu bar maganar, bana sonta. Ki yi hakuri." Ya dauko mini wata riga ya ce "Ga gifts din ki na zama matar aure, tun first night dinmu nw so baki, to bata iso a lokacin ba." Cotton yar kanti. Gaba'daya rigar tafi dacewa da yara y'an shekaru goma. Domin har da teddy wacce aka yi jakar goyo da ita. Sannan da hula irin mai malafar nan. Kalar ruwan hoda (pink )da yarfin filawa mai ruwan lemon tsami (lemon green) ce. Ba karamin kyua ta yi ba. Ya mik'o mini sabon pant. Ya ce na saka miki?" Na juyar da fuska. Ban amsa ba. Sai da na shanye kunyar na na ce "Tijjani da gaske dai kallon yarinya kake mini. Ban da haka wannan rigar ai ta yiwa Iklima ka'dan bare ni. Kasan kuma Anas ne yake bina ba ita ba." Kai-tsaye ya ce "Na sani. Sha'awa ta bani, shine na yi kundubalar d'auko miki ita, rabin ku'din na bayar. Abokina yake kawo su daga China. Ta kusa dubu ashirin, sonta nake yi, saka kawai". Na ce "Tsakani da Allah da atamfa ka siyo mini, yanzu wannan ina zan saka na je da ita?" Ya ce "Ba dan ki sa ki fita na siyo ta ba. Dan ki saka mini na kalle ki a yadda nake son ganin ki ne". Ganin ya b'ata fuska ya sanya na juya na saka pant din. Ina juyowa ya bani sabuwar breziya yar mitsil kalar wando da alamu set ne tare suka zo. Ban ce komai ba na kar'ba. Ina ayyana wato ya riga ya gama gane wacce zata yi mini. Domin duk na lefena sun yi mini yawa duk da k'ananu ne sai dai ko nan gaba. Domin da na aikawa Gwaggo akan ta bayar, dawo mini da su ta yi, ta ce nan gaba zasu yi mini na adanasu. Sai da na shafa hoda na goga jan baki kalar ruwan hoda. Sannan na zura rigar. Ta shige ni tsab. Ta d'an zarce guiwata da ka'dan, kasancewar ba ni da tsayi. Ya ce "Wow This is Asi beauty lady". Na dan yi murmushi. Ban ce komai ba. Da kansa ya sa mini hular ya d'auko sabon turare a cikin kayansa da aka rubuta Active woman. Ya bu'de ya hau fesa mini. Kamshin turaren jikinsa da wanda ya fesa mini suka hadu suak bige ni. Suka isar da wani irin sako akan Tijjani a cikin zuciyata. Shi kuma ganin na koma masa wata yar yarinya kankanuwa ya sanya ya sure ni. Ya yi falo da ni. Yana ta sakin maganganun da suke da nauyin bayyana wa. Komai da barin jiki yake yi mini. Ya ajiye ni akan kujera ya ce "Bari na kawo miki abincin Little Angel." Har cikin zuciyata na ji da'din sunan. Duk sunayen da Bulkachuwa yake fa'da mini babu wanda na ji dadinsa irin little. Domin ya dace da ni k'warai da gaske. Shiru shiru bai dawo ba. Sai na yi kamar na leka shi, sai kuma na fasa. Can sai gashi da tray da ya jero kayan abincin. Da walwala ya ce"Sorry little na bar ki ke ka'dai, ga shi babu wuta bare kallo ya hana ki gundura da zaman jiran kukun naki" Na k'yal-k'yale da dariya na ce "Wai kai ne kukun?". Cikin gamsuwa ya ce "Ba ki aminta ba? To mene ne aikina ban da na fita na yi aiki tukuru dan na nemo miki abin da zaki ci. Idan kuwa ina gida, idai baki bata mini rai ba. Still aiki zan miki dan na hutar da ke shiga kicin kullu yaumin". Na murmusa ba tare da na ce komai ba, domin na yarda da dukkan zuciyarsa ya ke yin maganar. Ya bu'de kwanon abincin ga mamakina sai ganin fanke na yi subu-subu sun soyu sun bada kala mai daukar hankali. Na kalle shi da mamaki na ce "Tijjani yaushe ka iya fanke haka?" Ya saki murmshin jin dadi ya ce "Ki bari sai kin ci sai ki tambayi na iya ko kuwa makwaki na yi". Na sauko ya ha'da mini shayi mai madara da milo. Shi kuma ya zuba bak'i. Muka fara cin fanke wanda ba karamin dadi ya yi ba. Na kalle shi na ce "Ya yi da'di sosai. Na ji har da k'wai da madara ka saka. Maimakon ka bar madara ka zuba a shayinka." Ya rausayar da kai ya ce "Ke dai ki sha my little". Ya kashe mini ido sannan ya ce "Ai ina ganin amfaninta. Addu'a nake yi sosai na samu damar da zan daina siyo miki ta sacet. So nake kullum ki sha ta ruwa gwangwani guda. Ta yadda ba zaki dinga gazawa da al'amarina ba". Kunya ta yi matu'kar kama ni. Na sanya dukkan hannuna na rufe fuskata, ina wani irin murmushin da bansan ta inda yake bullowa ba. Da k'yar na cigaba da cin abincin bayan ya ce "Duk a wajen Baba na koyi girki. Yadda kika ga Aliyu da Nasiru suna hidima irin ta y'ay'a mata nima irin wannan goyon ta yi mini. Kullum fa'di take yi, tunda bata samu mace ba, ba zai yiwu a ce ba zamu tallafa mata da kaomai ba. Kullum cikin fa'da mana take yi mu koyi aikin gida dan wataran mu taimaki iyalinmu. Annabin Rahma da yafi kowa daraja yana tallafawa iyalinsa. Ba mallakewa ba ne dan namiji ya yiwa mace hidimar girki, wanki, ko ta shara ba. Amma kuma ta ce "Ban da wanke wanke wannan na yan daudu ne". Muka k'yal-k'yale da dariya domin kuwa munsan kawai ra'ayinta ne amma babu aibu idan mutum ya yi. Ya ce "rigar nan fa ta yi miki kyua my little. Tamkar na dauwama ina kallon ki". Na murmusa ka'dan tare da ce wa"Thank you" a gayance. Na marairaice na ce "Ya maganar tomfirint din?" Cikin nutsuwa ya ce "zuwa wani satin zan kai ki da kaina". Na fa'dada murmushi na ce "Na gode Tijjani". Ga mamakina sai na ji nauyin gatsa sunan da na yi, ta mamaye ni. Karon farko da na ji hakan a rayuwata. Na lura shi kuma yana cikin maza yan ka'dan da basu damu da a fa'di sunansu kai- tsaye ba. Tas muka cinye fanken. Na kwashe kayan dan nasan idan ya mike zai kwashe ne. Na kai wajen wanke wanke na ajiye. Na koma wajensa na ce "Wai da yaushe ka yi kwabin ne?" Ya nisa ya ce"kina barcin gajiyar da na tara miki. Ni fa duk kallon jaruma nake yi miki. Ashe a tsiwa da dambe da sana'ar k'unshi kike da jarumtar". Na girgiza kai na ce "oh
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161