Chapter 104
Chapter 104
shima nasan filin yana nan. Wajen ya rayu, ya yi daraja ainun. Cikin cire girman kai Tijjani ya yi masa bayanin yana son ya zama cikin yaran shagon ko da ciccire ribabbun kayan miya ne. Domin ya fahimci idan Yabi ta haihu ba k'aramin nauyi ne zai sake hawa kansa ba. Ga shi kuma, kullum rayuwar k'ara tsananta take yi ga talaka. Da sakin fuska ya karb'e shi ya kuma babshi wani bangaren da zai dinga kula da shi. Dan haka sai Tijjani ya zama sai bayan kwana uku yake zuwa Toro. Duk sadda zai je kuma zai je da kayan miya, da kayan abinci. Sannu a hankali yake bin kasuwar yana kuma yin biyayya. Amma ba'a dauki lokaci mai yawa ba sai ya fahimci yadda *BAK'AR TA'ADAR* hassada ta yi katutu a zuciyar jama'a. Mafi yawa yaran shagon sun ha'de masa a dalilin suna ganin maigidan nasu ya daukake shi. Sannan ba ya yarda a yi aikin ha'inci da shi. Domin mafi yawa suna satar kayan su siyar ba tare da sum saka ku'din a shagon ba. Zuwansa sai k'udaden shiga suka karu dan haka Alhaji yake bud'a masa yake yi masa Ihisani. A yanzu da ya wadata su da abinci sai ya koma siyan kayan haihuwa. Duk sadda zai tafi sai ya sayi riguna unisex guda biyu, baya damuwa ko da iri daya ne matu'kar dai kala ta banbanta su. Da ya tara riguna da yawa sai ya koma sayan ragowan kaya. Yau ma Sai da ya biya ya siyi setin robar wanka mai sau'kin ku'di. Ya kalli rukunin masu tsada mother care. Ya ji sun ba shi sha'awa. A fili ya ce "Allah ka hore mini wata haihuwar na siya wa Asiya irin wadannan". Ya kara da setin mai na Nycil. Ya tafi ya hau mota. Bayan ya siya mata tarkacen su fruits dangin mangwaro da su abarba. Sannu a hankali muke rayuwa, har cikina ya shiga watan haihuwa, zuwa lokacin kuma ya canja mini gidan, amma shima na rabin shekara ya kama tunda ya fara tunanin mu koma Bauchi da zama, amma ya ce sai na haihu tukun. Kowa ya kalle ni sai ya yi maganr girman cikina. Har rinjaya ta yake yi. Idan ya tafi Bauchi sai Iklima ta dawo gidana. Sai ya dawo sannan ta tafi. Cikin sa'a haihuwa ta kama ni yana gari, kuma da daddare. Dan haka ya samo abin hawa, muka tafi, sai da aka karb'e ni, aka bani gado. Sannan ya tafi gida ya fa'da. Take Baban Marina ya ha'do shi da Mama akan ta zauna da ni. Har asuba ban haihu ba ina shan azabar duniya. Na yiwa Gwaggo addu'a yafi cikin carbi. Sai da na gama galabaita sannan aka fahimci bazan iya haihuwa da kaina ba. Nan da nan aka shirya ni zuwa d'akin tiyata. Amma muna shiga ciwo ya sake tasowa fiye da ko wanne. Na dinga kururuwa ina salati, tare da fa'din a ce wa "Gwaggo ta yafe mini." Likitocin da zasu yi mini aikin suka rufu a kaina. Ai kuwa sai ga haihuwa gadan gadan. Suka taimaka wajen zaro jinjiri. Yana fito wa ya xika dakin da kuka mai tsananin gaske tamkar gyare. Na fara maida numfashin wahala da gajiya. Ai sai wani sabon ciwon ya taso, gaba'daya na rasa karfina. Take kuma likitocin suka tabbatar ba mabiya ce kawai a cikin ba, akwai sauran halitta. Na fara kuka domin na tabbatar bazan iya sake haihuwa a yanzu ba. Ina kuka ina fa'din "Summa sabila yassara". Daga haka ciwo ya tsananta, na birkice, ga shi na kasa nishi mai tsanani. Da taimakon Allah da na likitocin na biyun ya iso duniya bayan sun k'ara ni. Wahala kan wahala na yi kafin na rabu da cikin da na kwashe watanni tara ina tiriri da shi cikin kalubale kashi kashi. Ban gama wartsake waccar azabar ba, aka shiga yi mini dinki tamkar k'warya. Duk yadda aka yi mini allura kashe rad'ad'i sai da na dinga jin ciwon har cikin kaina. Sai da suka gyaramu sannan aka karbo kayan Bebi a wajen Mama sannan aka fito da mu. Sai hamdala nake yi a zuciyata. Ina sake girmama sha'anin Ubangiji. Ba a taba ce mini tagwaye ne a cikina ba. Na tarar y'anuwa sun zo asibitin da yawa. Na dan ji da'di domin kaf y'ay'an Babanmu da aka aurar da su. Ba wacce ban ga ni ba, har Ubaida kuwa. Ko Yaya Indo da bata sake taka gidana tun ranar da aka kai ni ba, na ganta a wajen. Idona ya cika da k'walla ina ayyana duk yadda shaidan yake shiga cikin al'amarin zumuncin yau, jini yana da tasiri k'warai da gaske. Ina ta waige waige domin zuciyata so take ta ga jariraina, so take kuma ta ga uban y'ay'an. Amma ban gansu ba gaba'daya. Na ha'diye na yi shiru na cigaba da kallonsu d'aya bayan d'aya. Tare da amsa sannun da suke ta faman yi mini. Na jima kafin barci ya sure ni. Na dai farka na tarar da Babah ta Bulkachuwa zaune a gefena tare da Mama. Sannan Inna da Yaya Ummi suna ri'ke da jariran da aka nad'e su da zani iri d'aya. Dada na gefe tana mulmular goro a bakinta, tana kuma jan tasbaha. Da suka ga na farka, suka hau fa'din "sannu, sannu Yabi". Dai-dai lokacin kuma ruwan da ake k'ara mini ya k'are. Wata jamiar kiwon lafiya ta shigo a daidai ta cire mini, tana mini sannu. Da walwala ta ce "Mrs Bulkachuwa ina taya ki murnan samun wad'annan kyawawan jariran. Allah ya rayasu ya baki lafiya". Na yi shiru su kuma ahalina suka amsa da fa'din "Ameen mun gode". Ta kalli Mama ta ce "Zo ki ri'ke ta, ki taimaka mini mu zaunar da ita. Yaranta suna bu'katar nono". Da dabara suka zaunar da ni. Sai da ta tambayi na ji da'din zaman ko na takura a gyara ni?" A hankali na ce "Ya yi". Dada tana ganin malamar asibitin ta karbi yaron hannun Inna. Ta zabura ta ce "Dakata dafta". Kowa ya mayar da hankalinsa kan Dada da ta jawo ledar da ta zo da ita, ta fito da k'ok'o tare da gorar mirinda da kuma wani ruwan maganin a wata gorar daban. Ta yun'kura da k'yar tana dunduk'e ta nufo gadon. Ta kalli jami'ar kiwon lafiyar da take shirin kwantar da jaririri a jikina ta ce "gafara ka'dan". Cike da girmamawa ta kauce tana ce wa "Sannu tare da mamakin me zata yi. Sai dai su yan d'akin sun san me zata yi. Ta saka k'ok'o a cinyata, ta d'aga rigata. Duk da y'an k'ananun nono gare ni, amma tunda cikina ya fara girma suka ciko. Yau kuwa da ruwan nono ya zo sai suka yi girma suka tsaya k'yam tamkar kwakwa. Karon farko da aka bu'de mini nono a bainar jama'a ban kuma ji nauyi mai yawa ba. Ta daidaita ta dinga zuba ruwan robar ta kuma saka hannu tana wanke mini su. Sai kuma ta fara k'ok'arin matsesu tana fa'din sai an cire mataccen nonon da yake lalata jinjirai kafin a basu su sha. Dukkansu babu wanda ya yi inkarin hakan domin suma akan wannan Ta'adar suke. Nan da nan malamar asibitin ta ce "kin wanke Dada ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161