Chapter 127
Chapter 127
gaskiya a tsakaninmu. Amma kalamaina sun yi matukar dukansu gabadaya, shi kansa kallona yake yi ya kasa ce wa uffan. Karshe dai Babah ta rinjayar da gaskiya a tare da ni. A sanyaye ta ce "Ban yi mamaki ba. Domin mafi yawa maza haka suke yi. Da sun samu wadata kuma sai wulakanci ya biyo kan wacce aka sha gwagwarmaya da ita. Ba ko wanne namiji yake yin hakan ba, amma dai masu yin sun zarta marasa yin yawa. Sannu Yabi!" Ta fada cikin wani irin yanayi, mai wuyar fasaltawa. Kalaman Babah suka sake fadada zullimiin da yake ciki. Murya babu amo ya ce "Babah kada kalamanta su rude ki, ki bata lasisin cigaba da gasa ni da ruwan sanyi da take yi. Ubangiji ya bata iya sarrafa harshe. Wallahi ita take k'warata. Satin da ya wuce muka dawo daga Kano. Na kuma shirya mana tafiyar ne dan mu samu sauyin muhalli watak'ila hakan zai sa ta huce daga murdewar da ta yi. Jikina na rawa na dinga siya mata komai na ga ni. Amma Wallahi yadda kika san mugun abu na yi mata haka ta sake botsare wa. Tunda muka dawo ta sake taurare wa. Wai a ce yarinyar mace kankanuwa kamar wannan ta iya BAK'AR TA'ADAR gaba da miji haka siddan?" Na kalle shi na ce "TA'ADAR da baka yi ta sharri a baya, yanzu so kake ka k'ware a kanta. Bana gaishe ka? Masharranci kawai! Babah ta ce ",Innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Ashe kina iya zagin miji Yabi? A gabana kika ce masa masharranci? Ta jijjiga kai tare da ce wa "Tun baku je ko ina da zaman auren ba kun fara zaman da babu mutunci a ciki?" Ta dinga sababi ta inda ta shiga bata nan take fita ba. Gabadaya ta hadamu ta ki yarda da gaskiyar kowa. Ta kalle ni ta ce "Da kam ni kad'ai nasan wulakancin da zan yi masa a kan abubuwan da yake yi miki. Amma tunda na gane ba ki d'auki tarbiyar gidanmu ta barranta daga zagin mijin aure ba. To ai bani da ta ce wa. Domin na gane dukkanku ne baku da mutunci, dukkanku ne kuke son yiwa auren tawili". Ni da danuwana kuke son ku tozartawa, ku kunyata, ku jefamu cikin bak'in ciki da zunden jama'a ". ✍️ *Y'ar uwa, ya mukaji da bubukuwa?* *Daga nan fa har january kusan ko wanne sati akwai biki, in ba na kusa ba akwai na nesa, ban da tunanin gudunmuwa da ma kudin man da zakaje bikin ga tunanin abunda zaka saka.* *Balle ace maaikaciya ce ko CEO ce kina business din ki, kinsan all eyes on you🧐, ke ba sayen atamfa ba komi tsadanta anyo copynta, shima lace haka, cabdi! To albishirinki yar uwa!* *UMM NIHLA malaysianfabrics ta dauke miki damuwa, tana da fabrics kala kala masu sauki da inganci kuma babu inda zaki samesu in ba wurinta ba, kije taro ki haska kowa sai ya tambaye ki me kika saka ina kika samu💃 maza garzaya gurinta kusa labule.* https://wa.me/message/F3EWRSHQPQAAH1 Ta fashe da kuka tana fad'in ai bata san haka zamu yi mata ba. Da bata zo gidanmu ba. So muke mu kunyata ta ita da Baban Marina. Dukkanmu kowa ya shiga tashin hankalin kukan da take yi. Domin kuka ne wanda yake bayyana tsananin bakin cikin da me yinsa yake ciki. Da k'yar na bude baki na ce "Dan Allah ki yi hakuri Babah". Bata kula ni ba, ba kuma ta fasa kukan ba. Da k'yar ta yi shiru. Amma duk juyin da muka yi akan ta yi hak'uri ta tashi ta shiga daki bata ko yi motsi ba bare ta tanka. A wannan ranar na gane ita ma kafaffiya ce ta gaske. Domin kuwa dukkanmu a falon muka kwana a zaune, don bata yarda ko kishingida ta yi ba. Tashin hankalin da muke ciki tamkar idan an tsaga jikinmu ba za a ga jini a ciki ba. Ana idar da sallar asuba kuwa ta fice ko sallama bata yi mini ba. Haka nan Tijjani bai kai ga dawowa ba. Na bita ina fad'in "Dan Allah Babah ki rufa mana asiri ki yi hakuri, ki dawo ki gafarce mu." Tafiya kawai take yi. Muka yi kicibus da shi ya dawo daga masallaci. Duk kokarinmu akan ta dawo bata yarda ba. Duk rokon da Tijjani ya yi akan ya mayar da ita bata tanka ba, bare ta amince. Akan dole na dawo gida a dalilin ya ce na taho saboda mun bar yara. Na zauna ina hawaye domin ban tab'a ganin Babah ta yi fishi irin haka ba tunda na ke. A sururuce na shirya yara, na basu abinci . Amma ko makaranta na kasa tafiya. Kan dole suma suka zauna. Har azahar babu Tijjani babu labarin sa. Na tabbatar bin ta ya yi dan ya bata hak'uri. Tun fil-azal yana gudun bacin ran ta. Bare kuma yau da ta yi matsanancin fishi. Sai la'asar ya dawo gabad'aya ya yi zuru zuru, ya hargitse. Kallon sa kawai na yi na gane bai ci komai ba. A sanyaye na masa sannu. Ya zauna a falon ya amsa mini shi ma a raunane. Kaina a kasa na ce "Ya ya Babah?" Ya ce "Bata huce ba. Ya zuba mini ido ya ce "Asiya taimake ni ki fada mini laifukan da nake yi miki." Na yi shiru na k'i ce wa komai. Ya numfasa ya ce "Wallahi sai kin fada mini, na gaji da wannan jidalin na ki. Komai na yi miki babu gwangwaninta, kin tada hankalina kin tashi na ki. Mene ne haka. Kowa ya gan ki sai ya ce kina cikin damuwa ko jinya mai tsanani. Me nake yi miki hakan?" Na dauke kai daga kallonsa. Ya taso daga inda yake a zaune ya gurfana a gabana. Ya ce "Tun ban miki duka ba, ki bude baki ki fada mini musgunawar da nake yi miki" Na ce "Doke ni kawai, ai ka fi ga hakan ranka ya dade Alhaji". Ya damke ni ya ce "Tunda kika yi mini sanadin da uwata ta yi mini tofin Allah tsine Bilhillazi komai zai iya faruwa a tsakaninmu ". Ganin ya rikice da gaske idonsa ya kad'a tamkar wanda ya sha kayan maye. Yasa na bude baki na ce "Son ka ne bana yi, na gaji, kawai ka sallame ni". Jikinsa ya saki, damkar da ya yi mini ta yi sanyi a dalilin ya rasa karfinsa. Ya zuba mini ido tamkar mai son ya fahimci hakikanin abin da yake cikin zuciyata. Murya babu amo ya ce "mene ne dalilin janye soyayyar da kika yaudare ni da ita, har na yi zaton babu abin da zan yi ki janye ta Asiya?". Ban amsa masa ba. Ya kasa hak'uri ya ce"Mene ne bana yi miki? Duk abin da na gani burina na siyo na kawo miki, ko na siyo wa y'aya'n ki. Wanne nau'in abinci ne bana ajiye miki duk tsadarsa? Wanccan watan kina ce mini kayan Oriflame kike son amfani da shi, haka na daure na ce ki fadawa yar lame din da take siyarwa ta aiko miki, kuma tuni na biya. Da me na rage ki da kika janye samar mini da nutsuwa? Tunda muka dawo gidannan bamu jitu sosai ba, bamu samu
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161