Skip to content

Chapter 37

Chapter 37

Bakar Taada Book One Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
Download Book

"An gama Yabin Nuru". Zuciyata ta tsinke yau ga abin da Yaya J ya guda, na jingina wa Yabinsa sunan wani ba nasa ba. Mun jima muna dan tattauna wa duk da shine yafi yin hirar sosai. Ya ciro ku'di ya bani, na ki karba. A sanyaye ya ce "Matu'kar baki karba ba, to alama ce ta ban samu karbu wa ba". Jin hakan ya sanya na mik'a hannuna duka biyu na karb'a. Daidai lokacin Bulkachuwa ya shigo a hargitse rigarsa daban haka ma wando daban duk a yamutse. Da alamu ba nisa ya yi ba. Inda a ce d'an wanka ne sosai bansan irin rubibinsa da za'a yi ba, tunda a hakan ma ba'a fasa sonsa ba. Nura ya mika masa hannu suka gaisa ya wuce babu walwala nasan kuma yana taya kwamshina kishi ne. A lokacin na sake tabbatar da tsayi da cikar Bulkachuwa ya kai k'ure wa domin sai na ga Nuru bai kai kafadarsa ba. Daga haka muka yi sallamah ya tafi. Na shiga gida ana kiran magariba. Bayan mun idar da salla na bawa Gwaggo ku'din da ya bani sababbin yan dari biyar guda goma cif. Ta yi shiru sai kuma ta ce "Allah ka sawa al'amarin albarka, ya sa karshen wahalarmu kenan". Na amsa da Amin a zuciyata domin ni kaina na gaji da yadda komai yake kwace mini. Gaba'daya shekaruna sha shida ne da ka'dan amma na gaji tunda al'adar auren wuri ne a gidanmu. Wai duk yadda nake da k'arancin shekarun nan, da yadda nake y'ar tsurut habaicin rashin aurena a ke yi mini, ko a jefi Gwaggo da bak'ar magana. Har ta kai bani da kalubalen da ya wuce zaman gidanmu a rayuwata. Rayuwar gidanmu da ta gidan Yaya Ummi ta sanya na k'yamaci zaman babban gida. Wani zaman idan an yi sa'a sai ya zama tsintsiya dan ha'din kai. Wani kuwa sai ya zama tamkar sansanin yaki dan fitina. Ta sake kallona ta ce "Nasan yaron dan wajen Sahura ne, yana da zuciyar neman na kansa ga shi mai jin maganar iyaye ne, duk cikin matan gidan dakinta yafi na ko wacce fasali da kayan jere mai kyau, kuma duk shi ne yake yi mata, shi ka'dai ne namiji a d'akinta, y'ay'anta duk mata ne, amma da ya ke mai zuciya ne sai tafi mai y'ay'a maza biyar gata da kyan ga ni, ta bar uwar maza je da fankamar ita ce da gida. Shikenan rabuwarmu da Kwamshina. Ya mini waya washagarin da Baba ya ce ya je Azare. Ya fa'da mini yadda Baba ya je ya ba shi hakuri. Ya fahimci Baba suka rabu cikin girma da arziki, tare da ro'kon idan auren ya zo a sanar masa zai halarci dauri aure. Nima ya mini maganganun masu taushi da nuna muhimmancin yiwa mahaifi biyayya. Duk da ba wani sonsa nake yi ba, sai da na yi kukan yadda kalamansa suka dagargaza ni. Kewarsa ta taso mini ba ka'dan ba. Ya dinga rarrashi tare da tambayar me zai siya mini na kayan aure dan na yarda ya gode da karamcin da na yi masa. Na kasa cewa komai sai shine ya ce "Zan aiko miki da sako zuwa satin sama in sha Allah" Ya k'are maganarsa da fa'din "Allah ya sa ki shiga gidan auren a sa'a, Allah ya zaunar da ke lafiya". Bulkachuwa a bakin kwamshina ya ji maganar aurenmu ta ruguje. Rannan da hantsi ya aiko yana kirana. Zuciyata d'aya na je na tarar da shi a tsakar gidan Dada yana zaune kan kujerar tsuguno. Na zauna akan turmin da yake fuskantarsa. Ya kalle ni da tarin kulawa ya ce "Asiya Toro me yake faruwa ne? Jiya na shiga Bauchi sai nake jin labarin da ya ki'dima ni a bakin Honarable. Nasan ba zai mini karya ba, me yasa kika canja? Me yasa dan Allah?" Na yi k'asa da kaina haka kawai na ji hawaye ya k'wace mini. Domin idan aka cire yan kofarmu ba wanda ya nuna damuwarsa ko alhini akan shiririce wa da maganar Kwamshina ta yi sai Tijjani. Na tabbatar bayan soyayyar da yake yiwa lamarin, to akwai kishin wula'kanta ni da aka yi a gidan, shi yasa yake son na yi auren ke ce raini. Ganin hakan sai jikinsa ya yi sanyi ya ce "Ba kuka zaki yi ba, ya ce mini Baba ya gabatar masa da hujja mai k'arfi shi yasa ya ha'kura. Wacce irin hujja ce wannan dan Nabiyur Rahmati?" Ya fa'da a matu'kar zafafe. Kafin na ce komai sai Dada ta rarrafo ta ce "Ni ce nan! Na barranta lamarin, na kwashe masa albarka, ba zai yiwu na ha'da jini da mai kafirtamu ba. Ba zai yiwu ta auri wanda iyayenta suka tabbatar ba mutumin arziki ne ba". Da kakkausar murya ya ce "Dada me kika yi hakan? Su waye iyayenta?" Yana rufe baki ta ce "Su Badamasi mana". Maimakon na ga ya sake fusata sai kawai na ga ya kwashe da dariyar iyashege ya na fa'din "wannan shine abin dariya kunama ta ciji danwanke. Shi Baban Tsakiya idonsa da kwalli har ya ce wani bai cancanci Yabi ba? Sanin kowa ne Jabir da Yabi masoya ne tun suna yara k'ananu, amma shi da kansa ya datse soyayyar kuma yanzu Allah ya turo mata wani sai ya ce bai cancanci a ba shi aurenta ba. Wanne irin lamari ne mai kama da k'yashi da kuma hassada?" Dada ta rabka salati tana fa'din "Kawunka kake fa'din wannan kalaman a kansa? Mai sunan manya anya zaka yi hankali kuwa? Kusan ma fa saboda kai ya yi wannan al'amarin amma ka ke sakin maganganun da suka yi daidai da zaginsa kake yi." Ya sake fashe wa da dariya ya ce "a kaina, ni kuma? Lallai kuwa, zan ga ta yadda za'a yi, wannan bawan Allan ya nufo ni da wani alheri. Rannan ba abin da bai fa'da mini ba, akan sun je kai mini ku'din aure gidan kananun mutane ba'a karba ba. Ya dinga cin alwashin ba zai sake shige mini gaba a harkar aure ba. Ni kuma abin da bai sani ba, ai kawu ba uba ba ne, dama dangin uba ne a hakku su nemo mini aure, bare ya ce zan wani damu." Dada ta sake rangada salati tare da cewa "Mai sunan manya wanne irin dibar albarka kake yi ne haka tamkar ka sha k'waya?" A tunzure ya ce "Ras nake! Na gaji da fitinar mutanan ne, duk wata fitina su suke kitsa ta. A gabansu uwar Nasiba ta dinga sakin maganganu a kaina ta barranta y'arta da ni, ba wanda ya ce kala a cikinsu. Haka nan shima har yau ba wanda ya kalubalan ce shi akan hukuncin da ya yiwa Jabir na auren Maijidda saboda yana da cikakken iko a kansa. Akan me zai yiwa lamarin Asiya katsalandan alhalin ba kallon y'a yake yi mata ba? Akan me zai nemi ya dinga nuna ya isa da ni alhalin akan idon uwata suka kasa yi mini alfarma da kawaici." Ta ce "Allah ya shirye ka, albarkar mai sunanka shiriya zata sauko maka." Ya bata fuska ya ce "Tare zaki roka ta zo mana da ke, tunda akan idonki ake yin abubuwa na kura kurai amma ba kya iya tsawatar wa.

Table of Contents

Chapters

161 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161