Skip to content

Chapter 13

Chapter 13

Bakar Taada Book One Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
Download Book

dai daya tak da na sab'a miki, ki daure ki mini uzziri, ni kuma na yi al'kawarin ba zaki sake kama ni da laifi irin wannan ba". Na dauke kai na ce "To idan na yi ha'kuri na ce maka komai ya wuce, ya zan yi da tafasar da zuciyata take yi idan na ga Nasiba? Ya zan yi na goge amincin da zuciyata ta yi akan ita kake so bani ba, tunda ita din ta fini zama y'anmata?" Tsananin mamakin da na ba shi ya sanya ya kasa magana na tsawon lokaci. Sai da ya jima kafin ya numfasa ya ce "Ni fa ba wacce take burgeni nan duniya idan ba Yabin Marina ba. Kinsan dai ina tsokanar Nasiba tun fil'azal tunda abokiyar wasanmu ce, yar mace da dan namiji muke. A kaikaice na ce "Oh oh, ashe dama ana wasa har irin haka? To kuma wai ya matsayin wannan *Bak'ar Ta'adar* a shari'a tunda ba'a wasa da maganar aure?" Ya dan tunzura ka'dan ya ce "Ke Yabi". Nima na ce "Ke Yabi ko kuma ke gaskiyar magana?" Ya girgiza kai ya ce "Shi kenan na gode, na gode sosai da yadda kika ajiye ni". Ya fice ya bar ni, kafin na shiga wajen Dada Bulkachuwa ya fito daga dakinsa. Ya yi fitoh irin na tantiran yan-iska ya kalle ni ya ce "Asiya Toro rikakkiyar budurwa". Ya kwashe da dariyar iyashege ko me ya tuna kuma sai ya gintse dariyar tasa. A fili ya ce "Ban da ma shan koko d'aukar rai ne, ta yaya kamar Jabir da yake ganin Bigger babes zai tsaya wajen kwailaye irin Asiya Toro? Ya wuce yana sake fa'din " Soyayya da kananun yara menene a cikinsa ban da raini da ba'kinciki, yar yarinyar da bata gama iya wanka ba ma sai ta caccaba maka magana son ranta, abin ba'kinciki kuma dole ka rarrasheta ko ka hadu da gallazawar zuciya." *Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko Kuma kina sha'awar yin register da su*. *Ki tuntubemi babbar dealer din su Aisha lame* *Ina kuma fad'a muku akwai da daddan ganyen shayi na Lame Tea* *Akwai pop corn* *07036662633* Na yi kwafa a dalilin yadda furucinsa suka sake sawa na washe shi. A dole na shiga ciki na gaida Dada. Ina kallon yadda Nasiba take rawar jikin zuba masa ruwa a buta, dan ya yi brush. A raina na ce wannan fa shine shan kokon. Sai da ta gama barebaren yi masa hidima sannan muka fito muka wuce makaranta. Gaba'daya wannan zuwan na Yaya J ban yarda mun shirya ba, haka ya koma Jos. Ni kuma ina k'arfafawa kaina gwara mini Abdulrashid kamar yadda Gwaggo take so, domin ni da kaina ban san waya fi sona a tsakaninsu ba. Sai dai me? Juma'a da maghariba muna tsakar gidanmu sai jin ihun yara muka yi suna "Oyoyo Yaya Jabir, oyoyo". Nazira ta ce "wannan dawowar taki ce Yabi. Na ro'ke ki huce hakanan ai ya garu". Na tabe baki na ce "Rabu da shi, nifa dama ina ta neman hanyar da zan yakice shi a raina, ki ga fa irin yadda Baban Tsakiya ya yi wa Baban Marina, akan idonmu". Ta fesar da iskar takaici ta ce "Amma Baban ya ce ba ruwanmu da kasafinsa da yan'uwansa, a gabanki ya tabbatar bamu fi yan'uwansa a gunsa ba. Aure ai kaddara da rabo ne Yabi. Ban da haka da wani namijin bai isa auren wacce yake aure ba, sai kaddara ta ba shi, haka nan wata macen bata isa mijinta ya kalle ta da nufin soyayya ba, amma saboda karfin kaddara da rabo sai kiga ta zame masa mata kuma uwar ya'yansa. Matu'kar Yaya Jabir mijinki ne, sai kaddara ta sanya aurenku ya yiwu komin k'in da iyayensa zasu yiwa al'amarin. Mu da muka yi sa'a ma dukkan iyayenmu suna da ransu, kullum kuma suna roka mana mu dace da maza na gari, na yi imanin Ubangiji ba zai juyar da addu'arsu ba, hakan kuma ba zai hana mu ga kalubale a cikin ko wanne zabi ba, domin sunnar rayuwa ce komai na da irin nasa cikas din, sai dai albarkacin addu'ar iyaye sai ki ga komai ya saukaka. Jikina ya yi sanyi, na kasa bu'de baki na ce komai. Ta ru'ko hannuna sosai ta ce "Ki yi ha'kuri kin ji Uktina". Na nisa na ce "Na yi ha'kuri saboda ke, amma ki fa'da masa bana son irin wannan wasan, bana so". Cikin jin da'din na yarda da maganarta ta ce "Madallah da K'anwata kuma kawata YABIN J". Na murmusa a raina kuma sai addu'a nake yi mata ita ma Ubangiji ya kawo mata saurayin da zan taya ta sonsa, domin hatta Abdulrashid da ba wani sonsa take yi ba, bata ta'ba kushe shi ba, illah iyaka tafi son Yaya J. Idan ina yi mata d'an bikin ita bakin ganga ce, domin a gabansa bata ta'ba nuna masa akwai wanda take supporting sama da shi. Sai ta murmusa ta ce "Tunda har zuciyar Yabina tana dan sonsa ai kuwa yafi karfin na wula'kanta shi, baya ga haka son ki yake yi, dan haka nake girmama shi. Amma ai bazan so shi na bar Yaya J ba domin yafi shi cancantar ya same ki". Bata ta'ba nuna k'yashi ko takaicin ina da samari ita bata da su ba, duk da ta fini zama cikakkiyar budurwa. Ni da kaina na sani Nazira tana cikin Yan ka'dan da Ubangiji ya wanke musu zuciya akan k'yashi. Allah kenan! Sarkin hikima sai ya bawa bak'ar uwa karimi ko karimar yarinyar da za'a yi ta yi mata alfarma saboda kunyarsu. Hakan ce ta kasance domin sau tari sai na yi yun'kurin yiwa Mama iyashege irin ta dan yau dan ta fahimci dan Babanmu da Gwaggo suna shayinta, tunda laya ce ita, ni kuma mai zamani ce dole kuwa ta kiyaye ni. Nauyin Nazira ka'dai yake sawa nake hadiyar dukkan matsatsin da take sanyamu. Domin na riga na ajiye alakar matar Babana ce tunda bata ta'ba yi mini karar ni din y'arta ce ko ta mijinta ba. Ana idar da sallar isha ya aiko na je. Yana jingine jikin katanga hannuwansa biyu a kirjinsa, sanye cikin shadda shud'iya kalar sararin samaniya. Sai kamshi yake yi. Na rakube gefe guda ba tare da na ce kanzil ba. Ya matso kusa da inda nake ya ce "Assalamu alaikum Yabi". Murya babu amo na ce "Wa'alaika Salam". Ya ce "ki yi ha'kuri, na yi kuskure, tunda na gane da gaske ba kya son irin wannan wasan bazan sake yi miki ba shi kenan?". Na yi kasa da kaina, ba tare da na ce komai ba. Ya numfasa ya ce "Kin yi shiru". Cikin yauki domin da k'yar na ce "Ya wuce". Ya murmusa ya ce "Yabina sarkin ginshira, da rikici". Na kawar da fuskata gefe ban ce uffan ba. Ya dan damu ya fara fa'din "Kin ce "Ya wuce amma kin k'i sakar mini fuska, saboda ke fa na dawo". Fuska ba walwala na ce "Ya wuce mana, mantawa ai sai a hankali, yo ban da ma dai ina ganin mutuncin ka ai da an rabu ke nan, ina ruwana da duk wanda zai nuna mini yana son wata dan ta fini tirinya". Ya

Table of Contents

Chapters

161 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161