Chapter 29
Chapter 29
na fara tafiya, ya biyo ni yana fa'din"me kike nufi Yabi?" Ban kula shi ba, domin gaba'daya wani irin abu ya cushe mini zuciya da mak'oshi. Sai fa'di yake "Kina nufin zaki aure shi ke nan?" A tunzure na juyo na ce "A a ba aurensa zan yi ba, debe mini kewa zai yi, kafin a sahale maka ka nemi aure na". Ya girgiza kai ya ce "Wacce irin magana ce haka Yabi?" Kai tsaye na ce "Mai da'di kuma ta gaskiya". Ya rasa yadda zai yi, hankalinsa ya kai k'ololuwar tashi. Ya saki gauron numfashi ya ce "To ni kuma mene ne makomata ke nan? Na kadu na ce "Ban gane ba? Nusar da ni." Kai tsaye ya ce "Ina nufin ya maganar tawa soyayyar, ya batun aurenmu?" Na kafe shi da ido cikin tsananin kad'uwa. Kawai tambayar kaina nake yi "Ko dai ya samu mental disorder ne? Amma sai na shanye mamakina na ce "Jabir ke nan". Da sauri ya ce "ki ha'da ki ce Jabir Badamasi Toro, ba komai ba ne watarana In sha Allah zaki dawo da yayan domin ko kin yanke alakar da ta ha'damu ai baki isa ki wanke jinin da ya cakudamu ba" Na daure fuska ainun ban ce k'ala ba. Ya ce "Fa'da mini inda kika ajiye ni Yabi! Ina son ki, ina son na rayu da ke, ki yiwa Allah kada ki zalunci zuciyoyinmu, ki mini adalci ko da kina mini kallon azzalumi." Na murmusa na ce " Wanne irin adalci kake nufin na yi maka?" Ba nauyi ya ce "ki aure ni Yabi, ki bani damar da zan rayu da ke". Ido cikin ido na ce "To kuma ya zaka yi da Maijidda da aka baka dan ana ganin ta fini nagarta, kuma y'ar babbar k'ofa ce?" Ya ha'de rai ya ce "Ni da ke ne anan ba ruwanki da kowa, ni nake tsaye a gabanbki, kin sani kuma ina son ki, ina kaunar ki, idan kin bani dama ina da sauran dama uku a gaba da shari'a ta bani". Na jinjina k'arfin halinsa na murmusa na ce "zaka ha'da ni da Maijidda kishi? D'iyar attajiri irin Baban Kasuwa da ta fak'iri irin Baban Marina?" Ya naushi hanunsa ya ce "Kina da bak'ar magana Yabi! Ki yi kokarin kiyaye harshen ki, gubar harshe ta fi ta maciji dafi". Na yi gajeriyar dariya na ce ", Gaskiya na fa'da amma tunda ba'a sonta, to na janye" Nan da nan ya sace ya ce "To ki yafe mini, ina son ki, idan har kika ba ni dama zan tsaya miki, ba zaki yi kuka da ni ba. Zan fafata da duk wanda ya nemi shatale farin-cikinki da iznin Lillahi." Idona ya k'ada tsakanina da Allah ina matu'kar son Yaya J ba kowa zai fahimci hakan ba sai wanda suka yi soyayyar k'uruciya ta rikide ta zama ta gaske, irin wannan soyayyar tana matu'kar tasiri a cikin zuciyar banu adam. Amma na sani idan zan yaudari kowa, bazan yaudari kaina ba. Ba za'a ta'ba bari ya aure ni ba. Bayan k'iyayyar ubana to ni kaina wata irin kiyayya iyayensa suke mini wanda basu ki su gan ni da abin kunya ba. Dan haka hawaye ya b'alle mini, da rawar murya na ce "Yaya J ba kowanne Dan Adam ba ne yake nasarar rayuwa da wanda yake so. Mata da yawa ba wanda suke so k'addara ta aura musu ba, hakan nan mazan. Yarda da k'addara kuma sharadi ne na cikar imani. Ka sani, na sani ba za'a ta'ba barinka ka aure ni ba. Na tabbatar za'a bari ka auro ukun da kake kirari a ko'ina amma kuma ba za'a bari ka aure ni ka'dai ba, na gamsu kana sona, nima kuma har yau din nan ban so wani kamar ka ba, ba kuma zan so din ba. Mu yi addu'a Ubangiji ya sanyamu cikin masu soyayya dominsa wanda sakamakon hakan Aljannah ce". Idonsa ya k'ada ya ce "kin yi magana ta hankali Yabin J. Rabon da na samu aminci irin na yau, tun kafin ki juya mini baya. Abin da nake so da ke na yarda na gasgata ki, amma ki bani dama na sake jarraba wa ko za'a dace a wannan karon, zan yi iya kokarina dan na same ki, ai na yi biyayyar a farko". Na murmusa na ce "Shari'a bata hana hakan ba, amma zan ji nauyi mai yawa a ce ina kishi da Maijidda! Sai kuka ya subuce mini na gaske". A rikice ya ce "Wallahi zan iya rabuwa da ita matu'kar ita ce cikas din cikar burin ranmu. Sai dai ace na aikata *BAK'AR TA'ADAH* na saki aure akan wata macen da bata zo hannuna ba". Na girgiza kai na ce "Ba za'a kai ga hakan ba". A hanzarce ya ce "To ki huce da ni, ki bani damar auren ki". Hawaye na zuba na ce "Na baka Yaya J. Nan da sati biyu ka fito, idan har ya wuce baka bayyana a gaban Baban Tsakiya da Baban Kasuwa da nufin ka je neman aurena gabansu ba, ka tabbatar magana ta k'are a tsakaninmu ta soyayya har abada, na kuma baka dukkan damar da zan iya, sai dai ka sani ba zaka ha'da ni zama da ita a gida guda ba". Ga mamakina sai gani na yi ya zube a kasa yana sujjada. Ya dago ya ce "Alhamdulillah! Alhamdulillah! Alhamdulillah. Zaki ji sakona kuwa daga yanzu zuwa ko wanne lokaci. Sannan na miki al'kawarin a Bauchi zan nema miki inda zaki zauna kafin na samu halin gina miki naki gidan". Ya tako mini har titi ya tarar mini Napep ya biya, na tafi yana d'ago mini hannu cikin matsanancin farin-ciki. Ni kaina wani irin shauki ke fizgata mai danne dukkan bacin rai. Na manta k'iyayyar da Baban Tsakiya yake mini azima ce. Sannan Baban kasuwa ba yadda za a yi ya goyi bayan ayi wa diyarsa kishiya da ni. Amma dukkanmu hankalinmu ya gushe duk da ni din gatse na yi masa, amma TASIRIN soyayyar da nake yi masa ta taso mini haik'an ta saukar mini da farin-ciki mai tsananin gaske. Har nake fatan al'amarinmu ya kasance. Na isa gida na ci abinci na yi sallah na hau kitso tunda mutum uku na tarar suna jirana. Da yake a cikin nisha'di nake kafin ka ce kwabo duk na kitse musu. Hatta Gwaggo sai da ta fahimci irin walwalar da nake ciki, rabon da ta ganni hakan tun komai bai tabarbare mini ba. Ina idar da sallar isha na nufi wajen Dada. Na tarar ta idar da sallar ita ma tana jan dogon carbinta. Ni da Nasiba muke hirarmu, akan makaranta. Dada ta shafa addu'a. Muka gaishe ta ta amsa da walwala a dalilin yanzu shiri take yi da ni tunda tana samun alheri a dalilina. A sanyaye Nasiba ta ce "Kin daina d'ora mana karatu dai Dada". Ta murmusa ta ce "To kuwa yau zamu yi. Zan d'ora muku addu'ar da idan kuka lazumce ta babu ku babu yunwa ila yaumil k'iyamati, ina nufin duk tsanani, Ubangiji zai yassare muku abin da zaku ci". Nan da nan na nutsu domin idan na ji ingancinta na d'orawa Yaya Ummi domin ita kam tana wahala kafin ta k'oshi. Ta gyara
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161