Skip to content

Chapter 138

Chapter 138

Bakar Taada Book One Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
Download Book

sun karade a kwanakin nan amma babu Tijjani babu labarin sa. Kowa ya karaya. A ranar Baban Marina ya taho Bauchi tare da Gwaggo. Nasiha kan nasiha suka shafe lokaci suna yi mini akan yarda da kaddara na yi hak'uri mu bishi da addu'ar idan a raye yake Ubangiji ya tsare mana shi, ya kuma bayyana shi. Idan kuwa rai ya yi halinsa to Allah ya sanar da mu, ya kuma jik'an sa. Na rarrafa na fad'a jikin Baba cikin matsanancin kuka na ce "Sai yaushe zan huta, yaushe ne zan ji dad'in da ake ta fad'in zai same ni? Gabad'aya walagigi yafi yaws a rayuwata Baba! Kalli k'ananun y'aya'n Tijjani wa zai taya ni tarbiyarsu da wahalarsu Baba?" Muryarsa na rawa ya ce "Ubangiji da ya baki su shine jagoran da zai taya ki kulawa da su. Sannan matukar ina numfashi ko y'aya' nawa kika haifa zan kula da su iyakar yadda zan iya, tamkar y'aya'n da na haifa! Yadda ya kare maganar da kuka ya sanya Gwaggo fara kuka duk kuwa da yadda take da jarumta mai yawa. Kowa na falo kuka yake, hatta Mama kuka kuma na gaske ba na ganin ido ba. Tsawon lokaci muna kuka tamkar an tabbatar Tijjani ya k'are. Hanif ya ce "Ku yi hak'uri" Hamim kuwa ya ce "Baban 2 zai dawo a motarsa bai b'ata ba." Gabadaya yaran sun rasa kuzari da karsashi a tare da su. Da yamma mun idar da sallar la'asar Yaya Salisu ya kira Baban Marina da yake zaune a cikinmu tamkar mace. A sanyaye ya ce "Mun samu labarinsa, mun je mun gan shi". Gabadaya dakin muka hau fad'in Alhamdulillah Alhamdulillah! Sai dai Innalillahi wa inna ilaihir rajiun din da Baban Marina yake fad'i ya yi matukar tsorata mu, mussaman ni da zuciyata tamkar ta fad'o k'asa. Na kasa fahimtar bayanin da ake masa. Nasan dai na ji ya ce mun gan shi. Gumi ya dinga keto mini. Ina tambayar zuciyata wanne ibtilai ne ya samu Bulkachuwa irin haka?. Sai da Baban ya ajiye wayar. Tsawon mintina bai iya ce wa komai ba. Gabadaya ya jike da zufa. A sanyaye Gwaggo ta ce "Alhaji fad'a mana halin da ake ciki kada zullimi ya karasa kassara mu. Murya babu amo ya ce "Yana hannun jami'an tsaro. Tun shekaranjiya suke tsare da shi. Kuma damln tsabar raina talakan k'asa suka kashe wayarsa bare wani nasa ya ji halin da yake ciki." Na saki nannuyar ajiyar zuciya, da kuka nake fad'in Allamdulillah! Domin sai na ji tamkar an dauke mini k'atuwar masifar da ta nannad'e ni. Tunda yana da ransa komai mai s'auki ne. Domin ban fahimci ana iya yiwa mutum talala ya zama ba shi da yancin yin komai a rayuwarsa ba. Na kasa yin walwala a dalilin yadda Baban Marina ya yi laushi. Na tabbatar Tijjani na cikin k'ak'ani ka yi. *Toro* Baban kasuwa da Baban Tsakiya zaune a gaban Dada da take kuka face face tana fad'in "Ubangiji ka kare mai sunan manya, ka bayyana shi". Baban Tsakiya ya ce "Ki daina damuwa sai ciwon ya tashi ne? An ce miki a gan shi. Sai dai fitowarsa sai ikon Allah. Tunda laifin da aka kama shi da shi idan a wata k'asar ne take za'a tabbatar masa da haddin kisa." Hannun biyu ta d'ora aka tana kururuwa tana ce wa "Allah ka yi mini dan ma'aiki. Alfarmar Shehu Amadu Tijjani mai karama ka saukakawa wannan yaro". Baban kasuwa ya ce "Allah ne ya yi sakayya ya toni asirinsa. Wai Tijjani ya rasa wadanda zai wulakanta sai mu? A fili yake nuna wa Yaya Sani ne kawunsa da zai yiwa hidima. Akan idonmu zai ta d'orawa yara kayan abinci da kayan miya ana kai wa kofarsa amma mu wayam. Wai shi mai suruki. Alhalin ba akan son ramasa ya bashi auren iblishiyar yarinyar nan ba. Mune muka so a bashi".. Baban Tsakiya ya yi k'uta tare da ce wa "Allah ke nan! Ai duk mai gilli mai son ya wulakanta na gaba da shi ya dinga ganin jarraba ke nan." Dada dai kuka take bil hakki. Domin tun farko tana son Bulkachuwa. Da ya samu wadata kuma ya jiyar da ita dad'i duk da dai ce wa take yi bashi yake biyan ta. Tunda dukiyarta da ya salwantar mata runduna ce babba. Washagari muka dunguma Kano tare da Baban Marina. A babbar hedikwatar y'an sanda ta bonfai muka tarar da shi cikin mawuyacin hali. Hawaye ya tsinke mini. Domin gabad'aya ya fita a hayyacinsa. Babu alamun duka a tare da shi. Amma ya jigata k'warai da gaske. Abin mamaki a wajen muka tarar da su Yaya Jabir ya zo daga Kaduna da kuma Yaya Ammar yayan Nasiba. Duk da shi ma a BAUCHI yake aiki a gidan Yari. Tunda su Yaya Salisu suka fada musu, suka bar komai suka biyo su Kano dan sanin halin da Tijjani yake ciki. Cikin tashin hankali Tijjani ya ke fad'in "Wallahi bana harkar. Ina gida aka mini waya akan na biya na karbi sako a Wunti. Ashe wiwi da koken ce ga shi an kasa samun lambar da aka kira ni da ita. Wallahi ba kayana ba ne, ba ni da alak'a da ita". Ya fad'a idonsa ya kad'a ainun tamkar na rikakken mashayi. Na rushe da kuka riris. Domin dai na riga na gane mun fad'a cikin garari mai girma. Kallon sa na yi na gane iyakar gaskiyarsa yake fad'a babu alamun karya ko kwaskwarima domin ya riga ya bani damar da na fahimci gaskiyar sa da kunbiya kunbiyarsa. Babah ta kasa magana, yayin da Baban Marina ya ce "Tijjani ka fadamana gaskiyar magana, dan musan ta yadda zamu b'ullowa wannan azal d'in. Kasan wahalar da shari'a ma laifi ne babba." Murya na rawa ya ce "Wallahi gaskiyar magana na fad'a. Bana harkar, ba ni da alak'a da kayan da aka kama ni da shi Baba". Gauron numfashi Baba ya yi tare da ambaton "Subhanallah! Baba ta kasa magana duk da idonta a soye yake babu alamun kuka. Na sani kuma tana cikin damuwa ne mai yawa. Na tsugunna a gabansa ya sassauta murya ya ce "Asiya na rantse miki ba ni da alak'a da wannan al'amarin sharrin magauta na had'u da shi. Kaddarar da azal ce ta hau kaina". Na zuba masa ido tamkar ba a gaban iyayenmu muke ba. Shi ma ya zuba mini nasa, tsawon lokaci muna kallon juna. A cikin wannan kallon na tabbatar Tijjani bai aikata laifin da aka jingina masa ba. Na kuma gasgata shi akan gaskiya yake amayarwa. Ni na fara janye idanuwana da hawaye suka cika su taf. Da rawar murya na ce "Na gasgata ka Baban 2! Ina baka tabbas din ko baka samu mutum daya da ya gasgata ka ba. Ni Yabi na yarda bak'in k'azafi aka yi maka, tare da hak'a maka ramin mugunta. Dan haka ina tare da kai cikin ko wanne bigire har mu ga me Ubangiji zai zartar mana". Daga hakan na fara kuka sosai. Yaranmu da suke jikinsa suka yi tsuru tsuru suna kallon yadda nake kuka sosai, shi kuma ya susuce ido ya kad'a. Sai lokacin Babah ta ce "Allah ya warware maka, ya bayyana gaskiyar al'amarin". Yaya Ummi kuwa da Mama kuka suke

Table of Contents

Chapters

161 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161