Chapter 149
Chapter 149
zaba mini su. Muna kwance akan bargon da na shimfi'da akan tabarma tunda gadon ya yi mana kad'an. Ya ce "Kina shan maganin kuwa?" Na ce "Na kai wata ina sha, da yake an dora ni kan maganin da zai taimaka mini wajen conceiving. Ya saki ajiyar zuciya ya ce "Allah yasa satin da na yi addu'armu ta cika. Gobe zan koma kin sani. Wato albarkacin Ammar na yafe wa Baba Maryo! Asiya Ammar mutum ne. Kullum sai ya kai mini abinci. Wanccan satin na nuna masa ina son ya mini alfarmar ganin iyalina na kwana d'aya. Ina rufe baki ya ce "Na fara zazzabi, zai yi kokarin a kai ni asibitin waje daga nan sai ki zo." Ki ga irin hadarin da ya runguma saboda ya faranta mini. Tunda idan aka gane shi za'a iya sallamarsa daga aikin ace ya ci Amanar aikinsa. Ki ga yadda ya bamu sati a maimakon kwana d'aya ko biyu." Na numfasa na ce "Ni ma na yafe mata Allah ya shirye mu gabadaya." Ya ce "Ameen! Allah yasa kin harbu little." Na rufe fuskata a kirijinsa. Ya dinga Shafa fatar jikina ya ce man nan na Oriflame ya karbe ki. Jikar Dada dai ta iya zabarwa mutum man da ya dace da shi." Na murmusa cikin jin dadin yabawarsa na ce Aisha lame ai ta k'ware, wajen mayar da mace zama y'ar gayu ta gaske". Ya ce "Na gasgata ki". Washa gari kuwa aka sallame shi. Ina kallon yadda aka tafi da shi. Sai kawia kuka ya kwace mini a dalilin Babah tana gida saboda yara. Aliyu ya dinga ba ni hakuri yana ce wa "To da ba ki samu damar ganinsa ba fa? Sati guda fa ya zo ya yi miki haba dai Yabi. Ki yi hak'uri komai zai wuce. *** *Watanni biyu* Ana cikin haka kwatsam gwamnatin tarayya ta rage lakcarori cikin ikon Ubangiji har da Yaya Jabir aka sallama. Gabadaya mun ji ba dad'i mussaman da yake ya tara iyali. Tunda amaryarsa ma yaranta biyu, Maijidda na da biyar domin haihuwa take akai akai tamkar da gayya. Zaman Kaduna ya gagara tunda dama a quayers yake. Kan dole ya tattaro ya dawo Toro. Na tausaya, na ji babu dad'i dole a aka hak'ura tare da fatan Allah ya kawo wata damar. Baban Tsakiya ya dinga fad'in sa hannu ne. Kuma a cikin wadanda yake zargi har da Baban Kasuwa. Domin ya ce ai tunda Jabir ya kara aure yake ta tsiyace wa. Tabbas hannu aka saka masa. Yayin da Baban Kasuwa da ahalinsa suke murnanr hakan da ya samu Yaya J. Tunda sun tafi a cewar Jabir yana fifita amaryarsa akan Maijidda da take yar'uwasa kuma uwar y'aya'nsa. To yanzu sai ya yi rashin mutuncin su ga ni. Daga Baban Tsakiya har Baban Kasuwa kowa so yake a ce Baban Marina a bayansa yake. Har yau din nan sun fishi kudi. Amma ya fisu gata da rufin asiri . Domin a yanzu yana fita wajen sana'arsa saboda sabo da kuma mike kafa. Amma duk watan duniya sai mun ajiye abincin da za'a ci a kofarsa da kudin cefane. Hatta sabulun wanki da na wanka da zai bawa iyalinsa mun dauke shi. Hadawa muke yi gwagwadon k'arfin mutum. Ni ce sha kundum. Hakan da suke gani kuma sai kowa a cikinsu yake son ya shige masa, ya soki d'an- uwansa a gabansa. Shi kuwa baya biye wani a cikinsu suyi hirar wani. Amma ya karbe su da fuskar afuwa da sassauci yake mauaamala da su. Tunda ba abin da Ubangiji bai masa ba. Jahilci ne ka ce zaka rama sharri da sharri. Bakar Taada ce ka ce zaka maimaitawa wani irin kuskuren da aka yi maka. Mussaman akan zumunci, matukar ana son gyara, matukar ana son cigaba. To a bar BAK'AR TA'ADAR riko da kullaci. Afuwa da yafiya yana kawo soyayya da masalaha a tsakanin jini guda. Tashin tashina kuwa yana dawo da gaba da k'iyayyar juna. Allah ya yafe mu gabadaya. Zaune nake kusa da Babah yayin da Anas yake kan kujera su Hanif suna ta dabdala a jikinsa. Babah ta kalle shi ta ce "Kai bana son iskanci ka ji. Da wasa kake ko kuwa da gaske kake wannan maganar?" Da murmushi ya ce "Wallahi ta makance Babah! Ga mamakinmu sai Babah ta fashe da kuka tana fad'in"Allah mun tuba. Allah ka yafe mana. Ni dai ka shaida na yafe mata. Anas ina rokon arzikin ka, ka yafe mata. Addu'ar da ka yi mata cikin fishi ne Ubangiji ya karba. Ka yi hak'uri. Yau na sake gasgata A guji addu'ar wanda aka zalunta, mussaman idan ya yi ta cikin fishi da neman agajin Allah". Nan da nan ya ce "Na yafe mata. Ko yanzu idonta ya bude zan yi murna, idan bai bude ba kuwa Allah yasa ya zame mata kaffara. Amma ai ko yanzu ta ga karshen sharri. Tsofe tsofe da ita ta yi mini bakin sharri irin wannn. Haba wannan duniyar cike take da rudani. Ace wai jinin ka bai k'i ka tozarta ka yi bak'in ciki ba?" Ta share hawaye tana fad'in "Babu wanda zai mori zumunci sai wanda ya yi hak'uri ya hadiye komai, ya yi sassauci ya kuma yi afuwa. Zumunci da kansa ya roki Zati ya ce "Ubangiji ka jefa wanda ya yanke ni cikin wuta. Ubangiji ka tsananta wa wanda ya tsananta mini. Allah kuma take ya karbi addu'ar zumuncin. Shi yasa Annabi ya yi ta jan kunnenmu akan zumunci. Hatta makoci da aminin iyaye sai da Annabi ya yi ta jan kunnenmu a kansu bare kuma wadda nasabarku guda. Akwai bukatar mu ninka hak'uri da kawaici, hadi da yafiya idan kuwa ba hakan ba, gaisuwa ma sai ta gagara a tsakanin jini guda." Ya saki ajiyar zuciya ya ce "Da dukkan zuciyata na yafe mata. Na yafe wa kowa. Allah ya cigaba da dafa mana." Ta ce "Ameen na gode Anas. Na gode da ka yarda da maganata Ubangiji ya yi maka albarka". *Ya ce "Ameem Hajiya Babah tamu". ** Jumaa da yamma muka yi Toro. Muka tarar da baba Maryo a zaune a dakinta jikinta ras. Ido kuma gwaragwara amma bata ga ni. Fadi take yi "Na rantse bakin Anas ne ya kama ni. A yiwa ma'aiki a kira mini shi. Wallahi ya fini gaskiya. Hauwa ki yafe mini. Ki roka mini afuwa a wajen Yabi da Tijjani." Ta kece da kuka. Na matsa kusa da ita na ce "Baba ki yi hakuri. Ban kullace ki ba. Na kuma yafe miki. Na Ari bakin Tijjani shi ma ya yafe miki. Allah ha baki lafiya." Babah ma tana kuka ta rik'e hannunta ta ce "Sannu da ibada Maryo! Tuni na yafe miki babu komai a zuciyata game da sha'anin ki. Sai alheri. Allah ya yafe mu gabadaya ya kuma gajarta miki wahala. Sannan Anas ya yafe miki tuni, zan kuma k'ira miki shi ki ji da kunnen ki. A take Babah ta kira Yaya Aliyu ta ce ya bar komai gobe ya zo ya dauke su zuwa asibiti a duba ta da kyau. A Toro Babah ta barmu suka nufi asibitin Jos tare da Yaya Aliyu da kuma Yaya Ammar. Dama Nasiba a can take aure dan haka babu matsalar abinci.
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161