Skip to content

Chapter 154

Chapter 154

Bakar Taada Book One Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
Download Book

da shi a yi tafiyar nan da shi". Idon ta ya ciko da k'walla tana ayyana yadda Baban 2 yake fatan ya kai ta Makkah. Ashe abin na ransa, ashe itace zata riga shi zuwa Sau'udiyya? Hawaye ya tsinke mata. Babah ma ta shiga taya ta. Aliyu ya ce "Maimakon ku yi masa addu'a sai kuma ku yi masa tukuicin kuka?". Cikin kuka sosai Dada ta ce "Kai ku yi kukanku da kyau kun ji ai! Ali ai dole mu yi kuka. Yau sama da shekara Shehu na garkame a haka aka samu rabon Asma'u. Kai rabon haihuwa zazzafa ne". Aliyu ya ce "Kai Dada da fitina kike. Me ya kawo wannan maganar a yanzu kuma? Sannan kuma Yaya Tijjani ne ya koma shehun ko kuwa?" Ta ce "Eh shi fa. Tunda ga y'aya'nsa na girma ai gara na tsayar masa da suna d'aya. To na zabi Alhaji Shehu kawai domin sha Allahu wataran zai zama Alhaji da ikon Ubangiji kuwa". Ya gintse dariyasa ya ce "Ni na tafi, tunda Yabi ta had'a ni da aikin dauko Baban Marina gobe". Sai lokacin na ce "Tare zamu je, zan duba yaron Adda Nazira da ya yi targade." Ya ce "Tom in sha Allah". Babah ta ce "To kuma ya zaka yi da wannan kilifar ne tunda bata isa yaye ba. Watanta uku kacal" Ya ce da ita zaku tafi mana". Dada ta ce "Allahu akabar! Yabi ta haifo Yabi." Ya kwashe da dariya ya ce "A a Dada. Ai Yabi wadda aka haifa a hanyar sau'udiyya dan aikin Hajj ne ko aka je da cikinta. Ita kuwa wannan ai an riga an haife ta, sannan Umrah zaku je ba tawwali ba". Ta ce Hakane, sai ace mata Ummara Husna. Domin na tabbatar sai ta yi jidalin Asiya idan ba'a ce mata Ummarah ba. Oh ashe dai da rabon burin Yabi na zama Hajiya a kusa zai tabbata. Nasan Shehu ya biya mini ne dan na kula da ita, na jagorance ta a wajen sa'ayi da safa da Marwa". Ta bawa Aliyu dariya ainun ya ce "A Ina zaki jagorance ta din? Ai ko ke yanzu kika je d'aya zaku zama, ko wanda ya je bara idan ya koma bana sai ya ga abubuwan da bai san da su ba. Saboda yadda gwamnatin Sau'udiyya ta mayar da hankalinta akan Makkah da Madina gabad'aya. Bare ke mai shekaru ashirin da biyar da zuwa, ina ce da kika je ma ba'a haifi Anas ba?" Ta rausayar da kai ta ce"Ko Yabi yayarsa ma ba'a haife ta ba. Kasan ana daf da aihuwata ta Alhaji ya hadu da sharrin masu zamba cikin aminci, aihuwarta ta zo cikin wani irin yanayi mai tsananin gaske ". Na hauro na ce "Dada kina son fad'an wannan labarin. Nasan idan tafiya ta mika zaki k'arasa abin da kuke fad'a cewar ni na kore masa arzikinsa". Ta kama baki da azama ta ce "Yabi ki yiwa darajar Alhaji da Asma'u kada ki birkice mini. Ko mahaukaci ya ji labarin ki da irin bajintar da kike yiwa uwa da uba ai yasan ke din arzika ce ba wai Yabi ba. Yo duk gidan Marina akwai wanda bai ci arzikinki ba ne? Babu shi Wallahi. Allahu ya huci zuciyar ki. Bazan sake ba. Kai Ali tashi ka yi tafiyar ka, nima alwallah zan yi na yi munajiti da Ubangiji. Kai ma ka yawaita zikirrn ambaton Ubangiji ko na istigifari, ko da kuwa tukin mota kake yi ". Ya yi dariya ya ce "Wato da Yaya Tijjani da Nasiba da Yabi sune maganin Dada." Na dauke kai na ce "Kada ka sani Yaya Aliyu! Baban 2 da Nasiba dai. Tun fil-azal sune zasu yi sa insa da ita ta yi mukus. Amma ni kam menene bata yi mini ba?" Ta yi shiru ya kasa ce wa komai. Sai Babah ce ta fanshe ta da ce wa "To marasa kunya ta yi din. Suma wadancan din waye su da zasu yi maganin uwarmu? Ai tunda aka yi sa'a tana tsananta ibada komai zai daidaita mata." Da haka aka bar maganar domin jikin Dada ya yi sanyi. *INA MUKU ALBISHIR AKWAI DUKKAN TSOFAFFIN LITTAFAN MARUBUCIYA HAJIYA SALIHA ABUBAKAR ZARIA* *ZAKU SAME SU SOFT COPIES A HANNUNA* *HAKA NAN AKWAI WASU DAGA CIKIN LITTAFAN MARUBUCIYA HAJIYA HAFSAT C SODANGI, SUMA SOFT COPIES* *HAJIYA HANNE ADO ABDULLAHI?* *MARUBUCIYAR WANKA DA GARI DA KUMA WACECE UWA?* *TO ITA MA TAKANAS NA SAMO MUKU LITTAFANTA DOMIN KUN SANI TA YI RUBUTUN MASU MA'ANA*. *LITTAFAN DA YAWA, AMMA AKWAI DISCOUNT DOMIN SO NAKE KU YI TA SIYAWA Y'AYA'NKU DA KANNENKU LITTAFAI MASU DARASI DA MA'ANA*. *BA DA JIMAWA BA ZAN ZO MUKU DA SU*. *0803277333*. Da kaina na je Toro na sanar da Baban Marina cewar Tijjani ya biya mana Umrah ni da Dada Aliyu kuwa ya biyawa Babah. Ni kuma na biya masa. Ya yi k'asa kansa tsawon lokaci bai yi ko da motsi ba bare ya yi magana. Ya jima kafin ya d'ago. Na ga hawaye jagejage a fuskar sa. Nima nawa hawayen ya kwace mini amma ni kam na farincikin yadda Ubangiji ya yiwa fafutukar sana'ata albarka nake yi. Domin bani da burin da ya wuce na sanya Baban Marina farinciki tun ina mitsitsiya ta. Gorin da ake mini, haihuwa ta ce ta tsiyata shi. Da kuma bak'in cikin yadda ya zama koma baya a cikin gidanmu na matuka mintsinin zuciyata. Da k'yar ya yi jarumtar ce wa "Na sha fad'a miki ke kad'ai gayya ce Asiya. Na fad'a miki zaki yi albarka. Na dad'e ina fad'a miki akwai lokacin da zai zo da kowa sai ya so ki har makiyan na ki. Ga shi na fara ganin sakamakon alherin da Ubangiji zai yiwa hak'uri da juriyar da kika yi a rayuwar ki. Allah ya yi miki albarka. Daga nan har kasa ta rufe mini ido na yafe miki, kina cikin farar addu'a ta. Allah yasa y'aya'n ki su yi fiye da ke. Allah ya miki tukuici da alheri. Kin yi hak'urin aure, kin yi juriya. Da ikon Allah ba zaki sake fuskantar tsanani a gaba ba." Ina kuka na ce "Allah ya amsa Babanmu! Na gode Allah ya k'ara lafiya. Ya ce "Ku tafi da gyatumar ki Yabi. Kin ga dukkanku mata ne. Da ikon Allah zaki kai ni." Na girgiza kai na ce "Zata je Baba! Amma wannan kudin na tara kaso uku cikin hudu da sana'ar da na rayu ina yin ta. Kai nake son ka je, dan ka ji dad'i ka kuma godewa Ubangiji da ya jarrabe ka da fitinar yan'uwa. Sai kuma ya baka y'aya'n da zasu sadaukar da komai dan ka yi murmushi. Ka je ka yi mana addu'a. Ka kuma tayamu addu'ar Ubangiji ya kubuto mana da Tijjani ". Sai kuka na sosai ya k'wace mini. Abin mamaki sai shima ya taya ni kukan muka dinga yinsa a hankali. Da yake a dakin Gwaggo yake. Ta shigo da Husna a hannunta da ta fara kukan neman nono. Ta tsaya cak bata miko mini ita ba. Ta sassauta murya ta ce "Ayyah Yabi baki ga kullum girma sake kama shi yake ba? Me yasa kike kasa hak'uri a idan kina gabansa? Kin san yadda kukan ki yake rikita shi kuwa? Kalli

Table of Contents

Chapters

161 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161