Skip to content

Chapter 99

Chapter 99

Kallon Kitse Book One Complete Hausa Novels 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

ko, ni zan fita." Gyale ta d'auka ta fesa turare ta juya zata fice, da sauri ya duro daga kan gadon yace "Ina za ki je?" Ta na kallon idon shi tace "Bak'o..." Sai kuma ta yi shiru saboda tuna ranar da ya kwamtse mata baki, rik'e k'ugu ta yi tace "Ka ban hanya mana zan wuce." Rumgumo ta ya yi jikin shi ya dawo da ita ya zaunar akan gado, ture shi ta yi tace "Malam ka daina tab'a ni mana." Sosai ya kalle ta yace "Khadija, har yanzu fa ni mijin ki ne, a labarin da ki ka bani ba ni ne na kore ki ba, amma Khadija ki na hukuntani abisa laifin da na ke tunanin ko da na aikata shi ne dadangan za ki yafe min, me ya sa haka Khadija? Kin daina so na ne yanzu? Ko kuma ba kya son ki tsufa a gida na ne yanzu kamar yanda ki ke fad'a min." Mik'ewa ta yi tsaye tace "Ni dai kawai ka fitar min daga d'aki, so ka ke mutane su d'auka wani abun ne ke faruwa anan? Dan Allah ka tashi ka fita." Yau fa ya yi niyyar ba zai bar gidan nan ba babu wani sakamako mai kyau, dan haka ya haye gadon ya gyara kwanciya ya kalle ta yace "Ba zan fita d'in ba, idan kuma ki na ganin za ki saka k'artin 'yan uwan ki ne su fitar da ni to bismillah." Mamaki ne ya sa ta zaro ido tace "Abban Bilal, yan uwan nawa ne ma k'arti? To ai ko ba k'artin banza bane tunda su na ciyar da duka girman gidan nan dama wasu dake kewayen shi." Hararan ta ya yi yace "Ni kuma na gaza ko? To ki jaraba kiran su ki gani mana idan za su iya." Rumgume hannaye ta yi tace "Amma dai kasan tsaf zan iya saka su kefa min kai cikin kwalbatin unguwar nan ko?" Wata irin dariya ya bushe da ita yace "To ki kira su mana, na fad'a mi ki ina tsoro ne." Fitowa kam ta yi daga d'akin amma abun mamaki ba kowa a falon har telebijin ma an kashe, mayar da d'akin ta yi ta rufe ta dawo ta zauna kan kujerar da ke gaban madubi, kallon ta ya yi yace "Hajia ko za ki iya samo min kayan bacci a gidan nan?" A harzuk'e ta kalle shi tace "A ina zan samo ma ka kayan bacci? Na wa zan d'auko ma ka?" Har ta yi shiru shi kuma ya fara dariya sai kuma ta kalle shi tace "Wai ma tsaya, idan na d'auko ma ka kayan baccin me za ka yi da su?" Ba alamar wasa yace "Nan zan kwana yau, tunda na fahimci ba za ki koma gidan ki ba, kinga saina raba mu ku kwana, biyu a nan biyu a can." Tasowa ta yi ta kamo hannun shi ta na fad'in "A'a wallahi, akan me? Haka kawai kasa a kafa min hak'ora, kwana a nan saboda me?" Fizge hannun shi ya yi yace "In dai ba kya son na kwana nan to ya zamar mi ki dole ki had'a kayan ki yanzun nan mu tafi na mu gidan." Cikin b'acin rai tace "Wallahi babu in da zanje, haka ake kawai ka b'ullo min ta wannan hanyar." A nutse ya kalle ta yace "Na fad'a miki ki bani hak'uri tare da lallab'a ni dan na mi ki maganin matsalar ki, amma girman kai ya hana ki ko? To ba damuwa mu ci gaba da zama a hakan tunda haka ki ke so, yarinya sai taurin kai." "Ni na fad'a ma ka wani abu na damu na?" Ta fad'a ta na nuna kan ta da yatsa, saida ya tashi zaune yace "Ke kuwa ke da damuwa, gata nan b'aro-b'aro ina gani a idon ki." Duk da idon na ta na cikin gilashi amma saida ta mitsika idon ta kafin tace "Ban gane ba fa." Kashe mata ido ya yi yace "Yaushe rabon ki da ni? Yaushe rabon da na yi wasa da ke? Hajia Dije yaushe rabon da ki ji zallar ingantacciyar madara a jikin ki?" Shiru ta yi kawai sai kallon bangon d'akin da take, murmushi ya yi yace "Shi ya sa yanzu zuciyar ki ta cika saurin hawa, ki ka cika masifa da jaraba, sannan ba kya da kuzari kamar yanda ki ke a baya, sannan hakan zai shafi lafiyar abin da ke cikin ki, saboda ni d'in nan da kika raina to lafiyayyen abincin shi na jiki na, za ki iya haifar yaron ki babu kazar-kazar a jikin shi da walwala kamar sauran yara, saboda ya rasa wani muhimmin abu da ya kamata ya samu amma kin hana shi saboda ki na bak'in ciki." Juyawa ta yi ta kalli agogo ta ga har k'arfe goma ta soma wucewa, dan dama shi ma tara ta wuce ya shigo, kallon shi ta yi tace "Dan Allah babban mutum ka tashi ka tafi dare ya yi, ni kai na bacci na ke so na yi." "Wasa ki ke ko Khadija? Yanzu ki na nufin ba ki yarda da abin da na fad'a mi ki ba kenan? To shikenan, ni dai na yi niyyar kwana anan, idan ke ki na jin kunyar kar mu wayi gari mu fito a d'aki d'aya to ki je d'akin Bilal ki kwanta." Dafe goshi ta yi tace "Na shiga uku na, Abban Bilal ya ka ke so na yi ne?" Wani kallon mamaki ya bita da shi, saukowa ya yi daga kan gadon ya tsaya daf da ita yace "Khadija, ke da kan ki, ke ce yau saboda takura da gundurar da na mi ki har ki ke iya fad'a a cikin ido na cewa kin shiga uku, Khadija me nai mi ki da zafi har haka? A gaskiya ban yi tsammanin jin wannan maganar daga bakin ki ba." Juyawa ya yi cikin sanyin jiki ya d'auki hular shi yasa ya kalle ta yace "Shikenan uwar yarima, ni zan tafi, bana iya ce mi ki ga ranar da zan dawo ba, dan gaskiya kin kashe min k'warin gwiwa na, tunda ba kya son komawa zan rabu da ke, idan kin haihu kuma sai ki min magana idan ki na buk'atar takardar ki." Kama hanya ya yi zai bar d'akin Khadija da idon ta su ka cika taf da hawaye ji ta yi kamar ta k'urma ihu, saida ya kama hannun k'ofar zai murd'a ta yi k'arfin halin janyo rigar shi da k'arfi, baya ya yo kamar zai fad'i tare da kallon ta, kafin ya ankare ta hankad'a shi kan gadon ya fad'a da k'arfi, da iya k'arfin ta ta fad'a kan shi ba tare da tunanin cikin jikin ta ba, rufe shi ta yi da duka tako ina kamar Allah ne ya aiko ta, kallon ta kawai yake bai hana ta ba sai murmushi da yake dokawa, ita kam kuka take ta na fad'in "Aikin banza kawai, ashe dama ba so na ka ke ba shi ya sa har za ka iya saki na, so ka ke kaje kai da amaryar ka ku ci amarcin ku." Ganin sosai ta ke kukan da gaskiyar ta ya sa ya kwantar da ita a k'irjin shi

Table of Contents

Chapters

117 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117