Skip to content

Chapter 79

Chapter 79

Kallon Kitse Book One Complete Hausa Novels 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

motar? To saboda ta kai yaron ka asibiti ne, yaron da ya wuni da yunwa alhalin ya na gidan uban shi wanda ke wadace da kayan abinci sama da na shekara d'aya, amma wai akan hakane har ka d'orawa baiwar Allah laifi har ka iya dukan ta, ni ko a gani na ko taka Haseenah ta yi ta mayar da gabanta gabas ta yanka ta da wuk'a za ka iya mata uzuri, uzurin kuwa shine za ka duba dalilin da ya sa ta yi haka tunda ita uwa ce, amma ba komai, ka je gidan ka gani yanda ka lalata mata fuska da rashin hankalin ka, tace ba za ta dawo ba kuma na yarda da abin da ta fad'a, dan haka kaje kai da amaryar taka ku cinye kan ku, amma ka sani wallahi Fodio ina jin tsoron ranar da za ka yi nadama, dan alamu sun nuna *kallon kitse ne ka ke wa rogo*, tashi ka bani wuri." A hankali Usman ya d'ago kai ya kalle shi tabbas ran shi ya b'ace sosai, cikin taushin murya yace "Dan Allah Ba..." "Nace ka tashi ka bani wuri ko." Cewar Baba, mik'ewa ya yi ya juya zai shiga mota malam yace "Ji nan." Juyowa ya yi ya matso ya sake zubewa durk'ushe, d'orawa ya yi da "Har yanzu ita matar ka ce, kuma d'an ka ya na tare da ita, ban kuma yarda ka ce za ka d'auko yaron nan ba saboda banga alamar zai samu kulawa ba, dan haka umarni ne daga gare ni ya zama wajibi a wajen ka kai mu su kayan abinci da basu kud'in da za su yi sauran buk'atun su, ka ji da kyau?" Ya fad'a da kama kunnen shi. Cikin sunkuyar da kai Usman yace "Na ji Baba." "Tashi ka b'ace min da gani." Cewar malam ya na gyara zaman shi, tashi ya yi ya shiga mota ya wuce kamar zai fasa ihu saboda sharudd'an malam, amma kuma ba yanda zaiyi dole ne ya yi hakan d'in. Yamma sosai Haseenah na kwance d'aki ita kad'ai Mariya ta kira ta, bayan sun gaisa ne take tambayar "Wai ni kam ya ku ka kare da rigimar ku da matar nan? In ce dai Usman ya d'auki mataki?" Wata shak'iyar dariya ta yi tace "Ai tuni ta kama gaban ta, yanzu haka ni kad'ai ce a gidan, kwananta biyu yau ba ta gidan." Daga d'aya b'angaren Mariya tace "Ke Haseenah! Da gaske ki ke?" "Eh mana, zan mi ki k'arya ne?" "A'a, amma Haseenah ki na ganin abun baiyi yawa ace ta bar gidan?" "Baiyi ba, tunda ba ni na fitar da ita ba, bansan akan me su ka tattauna ba da har ta bar gidan, kuma shi ma ba na tunanin shi ya kore ta tunda har na ji yace tunda haka ta zab'a matsalar ta ce." Cikin sanyin jiki Mariya tace "Toh, yanzu me ye abunyi? Ba za ki bashi hak'uri ba ya dawo da ita tunda ya na jin maganar ki yanzu." Ba tare da tunanin komai ba tace "Abin da na ke so yanzun bai wuce ki zo gida ki same ni ba na baki kud'i ki kaiwa malamin nan ya sake mana wani aikin." "Wani aiki kuma?" Ta fad'a da k'arfi, cikin sassauta murya tace "Idan fa ta dawo da matsala, so na ke kawai ta ci gaba da zama acan har mala'ikan mutuwa ya same ta." Cike da gargad'i Mariya tace "Ke Haseenah ba ruwa gaskiya, me ya sa za ki yi haka? Me ya yi zafi? Na ga dai Usman ne kuma kin same shi, ina ganin ai zafi idan ta na gidan za ki fi k'unsa mata bak'in ciki, amma a dawwamar da ita a gidan su gaskiya abun ba dad'i." Cikin gaggawa tace "Kinga, kedai idan kin samu dama ki zo gidan ki same ni sai muyi magana." Shirun da Mariya ta yi ne ya sa Haseenah cewa "Ki na ji na?" Abin da ta lura a lamarin na Haseenah shine akwai alamun rashin kunya, amma saita dake tace "Shikenan na ji, idan na fita gobe siyan kaya zan biyo." "Ok." Kawai ta fad'a ta kashe wayar, nan ta ci gaba da zama har saida aka kira sallah magrib ta fito, kuma kamar yanda su ka yi da Usman bai dawo sai bayan isha'i, lokacin ta shirya sosai dan dama da kayan kwalliyar ta a cikin jaka, daga nan restaurent *Kebab* suka nufa cin abinci, rayuwa kenan, rayuwa ta juyowa Haseenah kam yanda ta ke so, gashi kuma ta na garata son ran ta, daga nan ma *plaza* su ka wuce suka siyi ice crime da sauran kayan mak'ulashe kafin su ka wuce gida, wangale k'ofa mai gadi ya yi amma ko kallo bai ishi dukan cikin su duk da gaisuwar da ya ke mu su, girgiza kai ya yi cike da takaici kafin ya rufe k'ofar. *Washe gari* bayan fitar Usman Mariya ta zo gidan, bayan Haseenah ta bata kud'in ta mik'e za ta fita, gwangwanin madara ta gani na *lacstar* aje, kallon ta ta yi tace "'Yar k'anwar tsakura min mana ko a leda ne na d'an kaiwa 'ya'yan ki." Cikin b'acin rai tace "Ba fa na san haka gaskiya, jiya ne fa na fasa madarar nan, idan na ce na dinga rabarwa ai ba za ta min ko sati ba." Waro ido ta yi tace "Sati fa? Yanzu wannan sai ki shanye ta a sati ke kad'ai?" Wata irin dariya ta yi kafin tace "Ai kamar kunu haka nake damata ina sha, kuma shine yace ta zama abinci na saboda ya na son ganin yaron da zan haifa kamar d'an turawa." Ta k'arashe da shafa cikin ta, tab'e baki Mariya ta yi tace "Yanzu ni dai sammin na tafiya ta." Saida taja tsaki kafin ta samo 'yar leda ta zuba mata cokali uku ta mik'a mata ta na fad'in "Karb'i nan ta isheki, ba na so yace ina almubazzaranci da kaya wallahi." Ganin 'yar madarar da ta zuba mata ya sa ranta b'acewa ta aje tace "Ki had'a kawai kisha, Allah ya raba lafiya." Ko a jikin ta ita kam har suka fito farfajiyar gidan Mariya tace "To ai kya bani ko na adaidaita ko?" 'Yar k'aramar jakar hannun ta ta nuna mata tace "Kin ganta wallahi k'ananan kud'i a ciki ita ce jaka biyu (maybe dubu d'aya yanzun, dan farashin kud'in ya sauya), amma ki bari idan ki ka dawo daga wajen malam d'in saina baki." Saida ta kalle ta sama da k'asa ta fice ko sallama ba ta mata ba, tun a hanya Mariya ta yanke hukuncin ba za ta je wajen malam d'in ba tunda ta lura iskanci ne abun na Haseenah, dan haka ma ta wuce gida kai tsaye ta fara tunanin abinyi da kud'in wanda zai anfane ta, a k'arshe ma dai jarin ta ta k'arawa yawa wajen k'ara siyo wasu kayan gwanjo. Yamma lik'is saiga Bilyamin ya sallama gidan su Khadija nik'i-nik'i da kayan abinci da na masarufi, hakan baiwa mutanen gidan dad'i ba saboda a ganin su za su iya ciyar da kamar Khadija d'ari ma bare ita kad'ai, amma da Mama ta fahimtar da su sai suka mayar da wuk'ak'en na su, in da Khadija kuma

Table of Contents

Chapters

117 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117