Chapter 97
Chapter 97
inda za su ci su sha, manyan mutane kuma suka dawo gidan su ango dan cin abinci suma. Bayan tafiyar 'yan d'aurin aure ne ba jimawa kuma Haseenah ta zo ita ma kamar yanda Usman yace ta zo da wuri, a d'akin Hajia suke zaune nesa da juna amma babu mai kula wani, haka suke zaune Khadija na hira da mutanen da ba su je d'aurin auren ba, Hajia ce ta fito daga uwar d'aki ta kalli Khadija tace "Nana wai kinga Bilal kuwa?" "A'a Hajia, ya na ina ne?" "Ai tare da malam su ka shirya su ka fita, kin ganshi kamar shine angon sai rawar k'afa ya ke, saida na gargad'e shi dai kan karya kuskura ya kalli wasu mata." Dariya kawai ta yi ba tace komai ba har mutane su ka fara shigowa aka fara hayaniya, nan su Hassana da sauran mutane suka fara raba abinci ana kaiwa mutane. Bilal ne ya shigo tare da malam kai tsaye wajen mahaifiyar shi ya nufa ya zauna kan k'afafun ta, wanda hakan ya yi daidai da shigowar Usman da kwalbar lemu a hannun sai malam a biye da shi, kwantar da kan Bilal ta yi a k'irjin ta tana sumbatar shi tace "Yarima na yi kewar ka fa, kwana uku ka na nesa da ni." Bilal kenan d'an gata sai kuwa ya sake wani cakume ta kamar zai sa nonon ta a baki yace "Mummy yunwa na ke ji fa." Lek'a fuskar shi ta yi tace "Ban gane ba, ba ka ci abinci ba ne a waje?" Cikin shagwab'a yace "Ban ci ba, to duka fa manya ne a wajen." Murmushi ta yi tace "To yarima na k'arami ne? Yaro ana bikin kawun ka ace ka na rasa abin da za ka ci, to ba ka had'u da Abban ka bane?" K'ara tusa kanshi ya yi cikin jikin ta yace "Um um." D'ago kan ta tayi za ta yi magana sai ga Usman tsaye gaban ta ya na fad'in "Yarima yanzu da girman ka za ka hau k'afafu haka?" Da sauri Bilal ya d'ago ya na ganin Abban shi ne ya yi tsaye ya mak'ale mi shi a wuya, rumgume shi ya yi shima yace "Me ya ke faruwa ne na ga ka na ta zuba shagwab'a haka?" Khadija ce tace "Bai ci abincin bane, amma kuma kai ga hannun ka nan har da lemu ma ka ke korawa." Kallon ta ya yi yace "To yanzu shan lemun nawa ya zama haramun ne ko me?" "Ya zama mana, taya za ka jefa loma bakin ka ba ka san gudan jinin ka ya ci ko bai ci ba." Yanda ta had'e fuska ne ya sa ya ga ko ya fad'a mata shi ma bai ci abinci ba ba yarda za ta yi ba, dan haka ya juya da Bilal d'auke da shi yace "Yarima muje ka zab'i abin da ka ke so ka ci, rabu da mahaifiyar nan ta ka yau tunda safiya ta waye ta tashi da masifa, can ta k'arata da masifarta." Shiru ta yi sai kallon k'eyar shi da take, shi kam jin ta yi shiru ya sa ya juyo dan ya san ta na nan ta na kumbura, wata irin harara ta dalla masa da tasa shi b'arkewa da dariya yace "Yi hak'uri Hajia, nasan me ye matsalar ki, ki ba ni hak'uri sannan ki lallab'a ni sai na mi ki magani." Yanda ta motsa bakin ta ya sa ya fahimci me take nufi, dan haka ya mata gwalo yace "Idan kin kamani ki mayar da gabana gabas ki yankani." Da haka ya fita su ka bar gidan, tun lokacin ba ta sake ganin Bilal ba har biki ya yi biki ana ta bayar da zafi, Haseenah na d'akin Aziza kwance sai narkewa ta ke, sai dai kuma abin ya d'an dameta na yanda kowa baya ma kula ta, sai wanda ya ganta ne dole ya ke iya gaisawa da ita, amma har Aziza sai ta shigo d'akin ta fita ko kallon in da take ba ta yi ba, haka yamma ta yi aka raba abinci, kasancewar a d'aki take ita kad'ai ya sa aka rabe abinci ba'a ma san da ita ba, babu wanda ya damu da hakan sai ma ran su Hassana da ke k'ara b'aci. Da dare mutane duk sun tafi gidan amarya da ango, Khadija ce d'aki ke gaggauta shirya dan tafiya tare da masu jiranta a waje tunda ta zo da mota, sai Haseenah da tun sallah magriba ta tafiyar ta gida, Hajia na zaune kan katifa gyangyad'i na neman fizgar ta Khadija tace "Hajia bacci ne?" Kallon ta tayi tace "To tukuna dai." Saida ta gyara jakarta a kafad'a tace "To ni zan tafi, kuma ina ga daga can gida zan wuce, sai dai gobe idan Allah ya kaimu." "To Allah ya yarda Khadija, Allah hutar da gajiya, angode sosai Allah ya saka da alkairi, saida safe." Duk ta na maganar ne saboda Khadija har ta kai bakin k'ofa ta na amsa mata, za ta bud'a labulen d'akin Usman ya sallamo, kaucewa ta yi da tunanin ya wuce amma saiya wani tsare ta da ido yace "Hajia ke kuma wannan kwalliyar fa? Duk ta zuwa kallon ango da amaryar ce?" Kallon Hajia ta yi sai ta ga ita ma su take kallo dan haka ta share shi kawai, hannu ya sa aljihu ya ciro da hankici (hankiciep) ya kai a bakin ta zai goge mata jan baki, da sauri ta ja baya ta na rufe bakin tace "Ya za ka goge min? Yanzu fa na saka shi, kuma ina da bak'o ne a gida." Wani kallo ya mata yace "Bak'o kuma? Wane irin bak'o?" Ba alamar wasa tace "Bazawari nn..." Bugun da ya kai mata a baki ne ya sa ta saki k'ara ba ta shirya ba tare da rufe bakin ta durk'ushe kan gwiwanta, Hajia da ta zabura ne ta kalle shi tace "Alhaji meye haka? Me tai ma ka?" Zaune ya yi akan kujerar da ke iya fuskantar Khadijar ya na hararan ta, cikin d'aga murya Hajia tace "Fin k'arfi ne ko me? Dallah malam ka bata hak'uri ko." Rai b'ace ya kalli Hajia yace "Hajia ba ki ji me yarinyar nan ta ke fad'a ba ne, ina matsayin mijin ta za tace wani wai bak'o na jiran ta, har da cewa wai bazawarinta." K'wafa ya yi hakan ya sa Hajia kallon Khadija da har yanzu ba ta motsa ba tace "Yi hak'uri kinji Khadija tashi ki tafi abinki, ba zan iya tashi bane saboda k'afafu na amma da na rama mi ki dukan ki, ki yi hak'uri kinji." D'agowa ta yi a hankali ta sauke ido a kan shi sun mata jawur, murmushi ta yi ta kalli Hajia tace "Saida safe." Mik'ewa ta yi ta fice daga gidan, ta yi k'ok'ari ta sauke ma su jiran ta a waje gidan amarya amma ita ba ta tsaya ba ta wuce gida. *A gurguje* A kwana biyu zuwa lokacin da aka kammala sabgar bikin Nura Usman ya shiga taitayin shi, dan ko wayar shi Khadija ba ta d'auka bare ta saurare shi idan ya zo, hakan ya tab'a shi sosai dan ya damu, haka ma Haseenah ta fara damuwa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117