Skip to content

Chapter 25

Chapter 25

Kallon Kitse Book One Complete Hausa Novels 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

godiya ga Allah da ya k'addara had'uwa ta da ke a lokacin da babu wanda ya yi tsammanin faruwar wani abu tsakani na da ke, sannan ina godiya a gare ki da ki ka zama yarinya mai hak'uri da zab'in iyayen ta da kuma tawwakali da hukuncin ubangiji, ina kuma godewa Ashir da ya yi tunanin had'a ni da ke har yanzu mu ke kwance akan gado d'aya a matsayin mata da miji, sannan ba zan manta da k'ok'arin iyaye na a kai na wanda su ka jajirce har sai da su ka ga kin zama mallaki na, tabbas duk wanda ya yi biyayya ga iyayen shi ba ya tab'ewa, ni shaida ne kuma na gani a zahiri, Khadija, zuwan nan da na yi na taho mi ki da tsaraba mai yawa, amma babbar tsarabar da na ke so na ga ta k'ayatar da ke ita ce *kyautar zuciya ta*." Tashi ta yi daga kxance ta na kallon shi tace "Ka na nufin ka mallaka min zuciyar ka gaba d'aya?" Sai da ya jinjina kai alamar tabbatarwa kafin yace "Hakane, kin cancanci fiye da wannan ma, dan da akwai abin da ya fi zuciya ta mahimmaci a gare ni, to da shi zan ba ki, dan a gaskiya ba zan iya ba ki rayuwa ta ba." Da sauri ta kalle shi tace "Ka na nufin ba zaka iya sadaukar da kan ka ba wa ni?" Da fuskar tausayi yace "A gaskiya ba zan iya ba." Cikin rashin jin dad'i tace "Kenan akwai wata da ka ke so?" "Akwai mana." Ya fadada murmushi, sai lokacin ta rarumo gilashin ta ta saka ta kalle shi da kyau, ganin idonta sun kawo ruwa ya sa ya saki dariya ya rumgume ta yace "Ina da wacce na ke so mana, ga ta a gaba na, Nana Khadija *baiwar Allah*, Khadija ke ce na ke so, ba zan iya sadaukar da rayuwa ta ba wa ke saboda da ke kad'ai na ke so na yi rayuwa, ina so na na k'are rayuwa ta tare da ke cikin farin ciki." D'agowa ta yi daga jikinshi ta kai mi shi duka a k'irji ta na fad'in "Har ka tsorata ni." Dariya ya yk yace "Hakan na nufin nima na samu shiga kenan a cikin wannan tattausar zuciyar?" Sai da ta rumgume shi tace "Sosai ma, kai ne farko da ka fara shigar ta, kuma insha Allah kai ne za ka zama na k'arshe, saboda ka na shiga na rufe ta na kuma jefa makullin a cikin tekun maliya." Sumbatar ta ya fara yi daga nan dai aka sake juyewa ni kuma na sake juyowa na fito😎,haka su ka dinga gudanar da rayuwar su abar sha'awa, sun manta da yanda ma aka yi su ka had'u, soyayyar su suke barjewa kawai, zan iya cewa daga cikin biyayyar da Usman ya wa iyayensa akan auren Khadija ce ta sa k'ofofin arzik'i su ka fara bud'e masa ta ko ina, ga kuma addu'a da kullum ya ke samu daga matar shi da iyaye da yan uwa akan k'ok'arin da ya ke da kowa, sosai ya ke samun ci gaba ta fannin kasuwancin da ya saka a gaba, duk da su na d'an samun k'arancin lokacin juna hakan bai hana Khadija taya shi murnar samun ci gaban ba, dan ta lura mutum ne mai son samun na kan shi ba ya kuma buk'atar taimakon kowa, dan ita kan ta yawan kyautar da take wa yan uwan shi da iyayen shi lokuta da dama ya na nuna rashin jin dad'in shi, musamman idan Kabir ko Mannir ko Nura da ke k'arami su ka zo ya ga ta d'auki kud'i masu yawa ta basu wasu lokuta ma har da sabulan wanka da turaruka, sai yai ta fad'a wai ta lalata su har Kabir da ke da aure, ita kam tausayin shi take ganin koyarwa ce ya ke sai wata a baka, duk da ya na fad'a ba ta daina ba saboda a ganinta ita ta na da halin da za ta yi mu su tun da yan uwan mijin ta ne, sannan duk wata ita ma yan uwan ta su kan turo mata kud'i daga cikin ribar da ake samu na kud'in ta da suke juya mata, haka dai har lokacin hutunta ya k'are ta ci gaba da zuwa makarantar ta cikin kwanciyar hankali, duk da mijinta ba mazauni bane, amma ta na gamsuwa da kulawar da ya ke nuna mata. *Wata biyu* da komawa makaranta Khadija ta kwanta rashin lafiyar da ta jijjigata sosai, dan sai da ta kwana hud'u asibiti ba ta cikin hayyacin ta, ta galabaita da mugun zazzab'i da ciwon kai, ga kuma ciwon ciki da ya murd'ata dole ta yi amai, allura kam tasha ta har ba adadi, haka K'arin ruwa har sai da hannayenta su ka kumbura saboda sukar da ya sha, duk da jikin ya yi dama amma sai da ta cika sati d'aya a asibiti kafin aka sallame ta, cikin ikon Allah kuma sai jiki ya yi kyau sosai, tun daga ranar kuma Khadija ba za tace ga ranar da ta sake kwantawa rashin lafiya ba, sai dai kawai abin da ba'a rasa ba irin su ciwon k'ugu, ciwon baya da d'aurewar mara, kullum Usman godiya ya ke wa Allah da Khadija da ta zama silar sauyawar rayuwar shi, bai tab'a tsammanin auren shi da ita abu neda zai kallo ba, duba da babu maganar soyayya tsakaninsu, sannan ita mai kud'i ce kuma matashiyar yarinya mai ji da kyau, amma ta aure shi babu kud'i babu kyau, kuma duk da haka ta zauna da shi da kyautatawa, wannan ya sa lokuta da dama ya kan fi kiran ta da Nana Khadija baiwar Allah, lokacin kuma arzik'i ya hab'ako sosai, sai kawai ya fara da iyayen shi ta hanyar canza mu su fasalin gida, in da ya gwangwaje su da bila (villa) mai kyau yar zamani, ya d'aukarwa mahaifiyar shi wacce za ta dinga girka mu su abinci sai dai su ci kawai, lokacin da cikin Khadija ya girma ne ya samu wani babban aiki, wata kwangila da aka mallaka mi shi milyoyin kud'i, a lokacin ne ya fara mu su sabon gini su ma, ginin da a lokacin ya amsa sunan gini, ta wani fannin kuma dije na zuwa makarantar ta hankali kwance. Lokavin dacikin ta ya isa haihuwa ne wata tafiya ta taso mi shi zuwa Dubaï, shine karo na farko da zai fara zuwa, hakan ya sa a ranar Khadija ta wuni ta na kukan ba zai tafi ba, rarrashin duniya ya yi amma ta toshe kunne ta k'i fahimtar shi, a k'arshe dai dole ya yanke shawarar kaita gida ta zauna tare da su mama har ya dawo, ita kuma bud'ar bakin ta cewa ta yi "Aiko sai dai ka tarar na haihu wallahi, dan ba zan jira ka ni." Dariya ya yi yace "Ba za ki haihu ba insha Allah har sai na dawo." Haka ya kaita gida ya aje shi kuma ya wuce, tun a mota Murtala ya lura yanayin abokin shi ya canza sosai, cike da kulawa yace "Aboki na lafiya dai? Ya na ga ka yi wani iri ne?" A hankali ya kalleshi ido sunyi jawur kamar zaiyi

Table of Contents

Chapters

117 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117