Skip to content

Chapter 44

Chapter 44

Kallon Kitse Book One Complete Hausa Novels 1,198 words 0 views Progress saved
Download Book

ciki." Nan ta bar su suka ci gaba da tattaunawa akan al'amarin gidan da kuma 'yer uwar su, bacci Bilal ya yi Habeeb ya kwantar da shi kafin suma su ka nufi wajen na su matan tare da tattara k'ananan yaran su da su ke tare da su anan. ***************** Washe gari ma Haseenah ce ta shirya abin karin kummalo, Usman da kan shi ya zo ya kira ta dan su ci tare amma tace wallahi ba za ta je ba, tunda dai har ta nuna abata kwanaki ita ma ta ci amarcin ta to ta bata, su biyu kad'ai su ka karya haka da rana ma da ta gama girkin aikowa ya yi aka d'aukar ma sa, tun k'arfe uku na rana Khadija ta shiga madafa ita da Uwani da wasu matasan 'yan mata biyu yaran mak'wabtan su, hakan ya sa gidan ya kaure kamar su na aikin wata hidima, kowa da abin da ya ke yi, Haseenah na iya hangen su ta k'ofa sai tsaki take da hararn su, cikin hukuncin ubangiji sai gashi zuwa k'arfe shida sun kammala komai sun gyara wurin kamar ba su yi aiki ba, a falon shi ma gyara su ka shiga yi in da Khadija ta sa suka gyara zaman komai da ke d'akin zuwa wata kusurwar ta daban, amma uwar d'akin shi da kan ta ta shiga ta yi gyaran, koda aka fara kiran sallah tuni har sun kammala musamman da ya zama akwai masu kamawa, ko da su ka yi sallah duka yaran abinci ta zuba mu su suka ci su ka k'oshi, sannan ta had'a su da kyautar turare wai su shafa tunda yan mata ne, har Uwani ma ba ta bari ba sai da ta mata, haka yaran su ka tafi bayan ta had'a su da jikka jikka, hakan ya sa duk abin da suke in dai ta tura a kira su to ko ba su yi niyyar tahowa ba iyayen za su ce su zo, saboda irin alherin da ta ke mu su, su na tafiya ta shiga uwar d'akin ta ita ma ta d'auko wasu robobi da blanda (blander) ta zauna gaban frigo (fridge). _Kankana ta d'auko wacce ta gyara ta da kyau ta zuba a blandar ta markad'a, wata k'aramar rariya ta sa ta taceta tare da rage wata a cikin wani kofi sannan ta d'auki dabinon da ta jik'a shi da ruwan rake tare da kanunfari ta zuba, shi ma markad'awa ta yi sannan ta tace shi cikin ruwan kankanar, madara peak ta d'auka ta juye a cikin had'in sannan ta d'auki gwangwanin maltina ta juye a ciki shi ma, ta na gama had'awa ta d'auki zuma cokali d'aya ta zuba a ciki, cikin frigon ta aje robar dan ya yi sanyi kafin ta shirya._ _Wani babban kofi ta d'auka ta d'auko ayaba manya guda biyu ta fereta ta yanka a cikin kofin k'anana k'anana, saida ta gama sannan ta zuba madara peak a ciki, kafin ta d'auko wata roba mai d'auke da garin aya ta zuba a ciki cokali uku, sannan ta d'auki wata robar ta bud'e ta zuba garin dabino shi ma cokali uku, juyawa ta yi sosai ya had'e jikin shi sannan ta d'auki kofin ta kafa kai ta shanye, wannan kankanar da ta rage a kofi ta d'auka ta zuba zuma a ciki tare dafasa k'wai d'aya ta kad'a shi sosai sannan ta shanye._ Tashi ta yi ta d'auki komai ta mayar a wajen shi sannan ta dawo gaban fridge d'in ta bud'a, wani kofi ta d'auka wanda dama kullum ya na ciki da karanfani a ciki, ruwan ta shanye wanda su ka jik'a sosai da kanunfari sannan ta rufe ta shiga wanka, da k'yar ta samu ta tsarkake gaban ta saboda ruwan da su ke fitowa, ta na gamawa ta d'auro akwala, ko da ta fito sallah ta fara kabbarawa har ta ida kafin ta zauna gaban madubi, ta jima ta na shafawa ta na gogewa, kwalliya dai ba wata abu ba kam ta yi ta sosai, ta na kammalawa ta mik'e tsaye ta bud'a wata drower ta d'auko wani turare da ba kullum take aiki da shi ba sai Usman ya na gari, a cibiyar ta ta fara fesawa kafin ta fesa a mara, sai bayan kunnuwan ta da wuya da kuma tsakiyar nonuwan ta, haka ma hammata sannan ta fesa a hannu ta shafa a mazaunai, rufewa ta yi ta aje kafin ta d'auko kaya ta saka, wata arniyar doguwar rigar shadda ce ta saka kai kace d'aurin auren shugaban k'asar garin su ne za ta je, wasu masifaffun takalma ta d'auka masu shegen tsini ta saka sannan ta d'auko kallabin kayan wanda dama ta sa aka d'aura mata shi musamman dan wannan ranar, wani siririn gilashi fari k'al ta sanya ta kalli kanta a madubi, murmushi ta sakarwa kan ta kafin ta dawo ta d'auki had'in ta da ta aje dan ya yi rab'a, kafa kai ta yi bata kuma aje ba sai da ta shanye duka sannan, komawa ta yi gaban madubi ta d'auki turaren ta na yau da kullum da har ya zama jikin ta, feshe kayan ta yi da shi sosai take ta sake d'aukar wani halataccen k'amshi mai kashe jiki, cikin takon isa da k'asaita ta fito daga falon, ta na shirin yin zaune a kujera ta ji mai gadi na wangale k'ofa, murmushi ta yi ta aje wayar ta ta juya ta fita, tsinin takalmanta ya sa dole take tafiyar a hankali mai d'aukar hankali, Usman da ya bud'e k'ofa zai fito ya hangota kasa fita ya yi, zuro k'afa ya yi ya na k'are mata kallo har ta tsaya gaban shi, kallon da ya ke mata ne ya tabbatar mata da wani abu ya ke rayawa a ran shi, saida ta sake narkar da ido tace "Wannan kallon fa?" Ba tare da ya daina mata wannan kallon ba ya sauke ajiyar zuciya, ganin baice komai ba ya sa ta kamo hannun shi har ya fito ta rufe motar ta kalle shi tace "Sannu da zuwa my *Exelency*." Murmushi kawai ya yi baice komai ba, matsowa ta yi daf da shi ta shafa fuskar shi tace "Da alama my *world* duk ka wahalar min da kan ka, yanzu muje ciki na baka agajin gaggawa." Hannun shi ta ja su ka yi ciki shi dai kamar sakarai, sai a uwar d'akin shi suka yada zango, kayan ta fara cire mi shi ta na fad'in "My *sweet angel* ya kasa min magana saboda ya na kallo na kamar wata bak'uwa a gare shi yau, amma ba komai girmanka ne ai." Za ta sunkuya dan cire mi shi wando ya rik'o ta, wani irin kallo ya watso mata yace "Gaba d'aya na rasa kuzari na, ban san me zan fad'a ba." Ita mayar masa da kallon ta yi tace "Kar ka damu, zan dawo ma ka da wutar ka." Ta k'arashe da kanne ma sa ido d'aya da d'ata bakin ta har ya yi k'ara, janshi ta yi zuwa ban d'aki har ya shiga ciki, ruwa ta sakar ma sa kafin ta shafa k'irjin shi tace " *My Mine* kasan me zai faru? Yanzu ka fara wankan ina zuwa yanzun nan." Ba ta jira

Table of Contents

Chapters

117 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117