Skip to content

Chapter 17

Chapter 17

Kallon Kitse Book One Complete Hausa Novels 1,198 words 0 views Progress saved
Download Book

cire takalmi za ta shiga kenan Usman shi kuma ya fito, saida jikinsu ya had'e da sauri ta ja baya, sai dai kuma ta na ja da baya ta kai wa tsohuwar karo, da azama ta sake matsawa ta na fad'in "Yi hak'uri, yi hak'uri dan Allah." Wani banzan kallo Usman ya mata ya rab'ata ya wuce ya saka takalmin shi, Khadija kam ajiyar zuciya ta saune ta k'arasa shiga ciki, zaune ta yi kusan katifar da tsohon ke zaune ta aje ledar hannun ta, da murmushi tace "Baba ya jiki?" Shima da murmushin yace "Jiki da sauk'i 'yata, ya na ki jikin? Ince dai ba ki ji ciwo ba ko?" "A'a Baba, ban ji ciwo ba." "To Allah ya k'ara kiyayewa, Allah ya kare mu daga sharrin k'arfe." "Amee Baba, kuma dan Allah ka yi hak'uri, laifi na ne abin da ya faru." "Ah haba haba, 'yata ba laifin ki bane, Allah ne ya aiko ai, sai dai Allah ya k'ara kiyayewa, kuma ku dinga kula ku na tafiya a hankali." "Insha Allah Baba, nagode, ni zan wuce." Tsohuwar ce tace "Sai tafiya y'ar nan, ko ruwa baki sha ba." Da fara'a tace "Ba komai mama, ai daga na ke, kuma tare da yaya na mu ke, ya na sauri zai fita aikin shi na tsayar da shi." "Kuma gaskiya hakane kam karki tsayar da shi." Tashi ta yi ta fito ta musu sallama, tun ranar kuma Khadija ba ta sake samun damar dawowa gidan ba saboda shirye shiryen tafiyar su k'asa mai tsarki, haka lokacin tafiya ya yi kuma su ka tafi sama tare da mama da matar Ashir da ta Bashir, dan dama an had'a su da mama ne saboda dukansu zuwan su ne na farko, masha Allah sun je lafiya kuma sun dawo lafiya, dukansu sun canza musamman Khadija da dama Allah ya hallice ta da kyanta, inda ta k'awata haurunan ta da hak'oran makka guda biyu, saida su ka yi sati su na karb'ar bak'i da huta gajiya, sai dai har lokacin nan Khadija na tunanin tsohon da ta buge, tunanin ta kawai ita ce silar kwantawar shi, dan haka ta shirya da dare tare da ware kayan tsaraba dan ta kai mu su, sanye take cikin bak'ar doguwar riga har k'asa mai walkiya da kwalliya, takalma sai d'an kwalin da ta mi shi sassauk'an aji a saman kan ta, farin gilashin ta mai kewaye da bak'ar kala ya dace da fuskar ta da kuma rigar, farin man leb'e ne kawai ta shafa, yau kuma Naseer ne ya shirya zai kai ta wanda ya zo hutu, har k'ofar gidan ya dire ta shi kuma ya fito ya tsaya bakin motar, ta na zura kai cikin soron sai duhu, wayarta ta fara k'ok'arin fitowa da ita daga cikin k'aramar jakarta sai kawai ta ji ta zube a k'asa, 😂 "Ahhhhhh." K'arar da ta saki kenan lokacin da Usman ya yi gaba da ita ta fad'i zaune a k'asa, wayarta da ledar hannun ta da kuma gilashi duka sun kama gabansu, da sauri Usman ya kunna wutar ta shi wayar dan ganin wacece, " *mai gilashi*." Abinda ya fad'a kenan, sai dai mamaki ne ya lullub'e shi ganin Khadija nata lalubar inda gilashinta ya ke, tambayar da ta zo mi shi ita ce "Ba ta gani ne? Ko kuma har yanzu duhun take gani?" Ya na kallon ta har ta kai hannunta kan gilashin ta, da saurita d'auka ta mak'ala a ido, tarau taga Usman zik'au a gabanta da hasken fitila, da sauri ta mik'e tsaye ta na tattare kayan da su ka zube, shi kam sai ya ji ta ma ba shi haushi, guntun tsaki ya yi ya wuce ta cikin b'acin rai ya fice daga gidan yana fad'in "Idan dai ki ka ci gaba da anfani da gilashi haka kawai, wallahi kin kusa zama makauniya, in banda hauka har cikin dare ma sai kinyi fama da gilashi, kuma yanzu haka ma na masu larurar ido ne take sakawa." Ya na fitowa ya ga Naseer tsaye, gaisawa su ka yi cikin sanin juna, dan da Usman da Ashir sunyi aji d'aya a makarantar boko, hakan ya sa su ka zama abokai sai dai ba abota irin sosai d'in nan ba, ita ma data shiga ciki k'anan Usman da suke uba d'aya ne ya mata iso har d'akin babansu, bai gusa daga wajen ba ya na kallon fuskarta da murmushin ta ya na jin kamar yace ya na son ta, har ta taso ta fito ya rakota k'ofar gida, kallon juna su ka yi ita da Usman da suke ta hira da Naseer, sallama su ka yi Naseer ya shiga mota ita kuma ta juya ta kalli *Mannir* tace "To sai anjima ko." "Sai anjima, sai yaushe kuma?" D'an wasa ta yi da idon ta tace "Kowane lokaci ma za ka iya gani na." "Shikenan to, sai anjima." Bud'a k'ofar motar ta yi za ta shiga sai kuma ta ga Usman sai wani kallo ya ke mata kamar irin ya na jin haushin ta, dan haka ta rufe k'ofar ta zagayo wajen shi ta kalle shi cikin taushin murya da nutsuwa tace "Na ga kamar haushi na ka ke ji saboda abin da ya faru, dan Allah ku yi hak'uri ku yafe min, duk da nasan laifi na ne, amma kuma Allah ne ya aiko, ka gafarce ni idan na b'ata ma ka rai." Juyawa ta yi ta shiga motar, shi kuma juyawa ya yi ya na jan wani tsakin, bin Mannir ya yi da harara yace "Sai ka rufe bakin to sakarai, har da wani sai yaushe za ta dawo, to uwar me za ta maka idan ta dawo?" Bai jira me zaice ba ya wuce sabgar gaban shi, tun daga ranar kuma Khadija ba ta sake komawa gidan ba, dan lokuta da dama ta kan ji ta na so taje saboda tsohuwar da tsohon masu kirki da kuma saka mata albarka, amma idan ta tuna Usman sai ta share kawai, a cewar ta wannan ba shi da kirki ko kad'an, gashi da d'acin rai da zuciya, alhalin Usman kuma ba ma mazauni bane, baya cikakken sati a gida bai tafi sabgar gabanshi ba, musamman ma da iyayen ke yawan mi shi magana akan ya yi aure, shi ya sa ba ya son zaman gidan dan duk motsin shi sai suce da ya na da aure da anyi kaza, aure ba shine gabanshi ba, ya na so ya taka wani mataki kafin ya yi aure, shi ya sa ma shekarun shi *talatin da d'aya* ba sa damunshi, k'annan shi mata yan biyu da suke bi mi shi tuni suka hayayyafa a gidajensu, sannan d'aya k'anan shi da suke uwa d'aya ma yayi aurenshi shekara biyu data wuce, k'annan shi mata kuma hudu ne a gidan mazajensu, duk iskancin da suke mi shi ko a jikinshi kam, neman sisi da kwabo yasa a gaba. *Bayan wata bakwai* Khadija har ta fara karatunta na jami'a (lycée) hankali kwance, ta yi sababbi k'awaye sosai a ciki ne ta had'u da *Barira nagoma* wacce unguwarsu ke kusa da gidansu Usman, duk da Khadija ce ta bige tsohon amma ta manta da abin da ya faru, ranar kawai sun taso daga

Table of Contents

Chapters

117 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117