Skip to content

Chapter 26

Chapter 26

Kallon Kitse Book One Complete Hausa Novels 1,196 words 0 views Progress saved
Download Book

kuka yace "Khadija, ita na ke tausayi, sai ta haihu kafin na dawo, ba na jin za ta wuce sati ba ta haihu ba, dan duk alamu sun nuna haka, kwana hud'u ko bacci ba ta iya yi saboda ciwon baya da mara, mtss." Ya k'arashe da d'an guntun tsaki. Murtala ne yace "To ya za ayi sai hak'uri? Kuma gashi ba ka fad'a mata gaskiyar magana ba cewa tafiyar nan za ta iya d'aukar ka wata d'aya ko fiye da haka." Ajiyar zuciya ya sauke yace "Sati d'aya ma na fad'a mata amma ta damu sosai, ina ga na fad'a mata wata d'aya zanyi? Shi ya sa ma na riga na barwa Hajia komai su kula idan ta haihu, kuma na gode Allah da na iya fad'awa yan uwan ta adadin lokacin da zan iya yi." "Hakan ma da ka yi ya yi daidai, kaga za su dinga kwantar mata da hankali." A haka su ka isa kuma su ka rabu suma cike da kewar juna, a daren wannan ranar Khadija nak'uda ta taso mata, da su ka tafi asibi har sai da gari ya waye rana ta yi fatsal-fatsal kafin ta haihu, duk abin da ake Usman na da labari, lokacin da Husseina ta bawa Khadija waya ya mata magana da ta kasa, wata k'ara tare da kuka had'i da salati da ta yi sai da ya ji kamar ya bud'a ido ya ganshi gabanta, a k'arshe dai *bayan wuya* sai dad'i, ta haihu lafiya haka ma yaro, lokacin wani mugun bacci ne ke d'ibar Khadija amma sai Usman yace Hajia ta bata waya su yi magana, daga kwance ta karb'i wayar ta d'ora a kunne, shiru ta yi sai shine yace "Barka baiwar Allah, daga k'arshe dai Gashi kin haifo min yaro, Khadija ina cikin farin ciki sosai, godiya ko dukiya ba za su iya biyan ki ba, amma ina so ki fad'a min duk abin da ki ke so? Ni kuma zan baki shi a matsayin tukuicin wannan kyautar." Cikin muryar jin bacci tace "Ina hushi da kai kafin minti ashirin da su ka gabata, saboda ka k'i zama tare da ni a lokacin da na ke buk'atar ta, da ka k'ara kwana d'aya tak da na haihu a gaban idon ka, amma bayan minti ashirin da ya wuce, lokacin da na d'ora ido na akan yaron ka, sai na ji komai ya yaye a zuciya ta, dan haka ka d'auka yaron nan shine tukuicinka gare ni." Wata nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke yace "Ki yi hak'uri Khadija, haka Allah ya so, kuma duk da kin ce ba jya buk'atar komai, amma akwai wani abu da zan ba ki, kinsan me ye?" Cikin lumshe ido tace "A'a." "Khadija, nine ya cancanci na yi wa yaron nan hud'uba, kuma gashi bana nan, dan haka babu wanda yafi cancanta sai ke, na d'ora mi ki wannan nauyin a kan ki, idan kin ma sa hud'uba sai ki rad'a masa sunan da ki ka ga ya dace kuma ki ke so." "Da gaske ka yarda na saka mi shi suna da kai na?" Ta tambaya da fara'a. "Sosai ma, wannan hukuncin na jima da yanke shi ai, ba kawai dan bana nan bane." Shiru ta yi kamar mai bacci kafin tace " *Abban Bilal*., hakan ya yi?" Da farin cikin jin sunan da ta sakawa yaron ya sa yace "Masha Allah, Bilal, sunan da ke birge ni, sunan da ya nake da burin sakawa yaro na shi, hakan fa ya na nuna k'arfin soyayyar da ke tsakanin mu ne." Jin bcci na son surarta ya sa tace "Ka gafarce ni Abban Bilal, bacci na ke ji sosai a ido na, za mu yi magana anjima." "Ayyah sannu momyn Bilal, zan barki haka to, amma anjima za mu yi magana, kin yarda?" Cikin hamma tace "Na yi alk'awari." Da haka su ka yi sallama, kamar yanda ya bar komai hannun Hajia haka ta dage sosai ta yi takamata, dan mawasu lokutan maman Khadija da yan biyar ba sa tsayawa komai da an nemi abu za su siyo su kawo, haka dai aka yi shagalin biki babu uban yaro, a lokacin Khadija ta fara damuwa da rashin dawowar Usman, da k'yar yan uwanta da mama suke kwantar mata da hankali, tun suna waya ya na cewa zai zo aiki ne ya rik'e shi har ya kai ya rasa me zai ce mata, sai kawai zuciyar shi ta bashi ya daina kiranta, ita kuma idan ta kira jar ya d'aga sai an kwana biyu, wannan dubarar ce ta jefa Khadija a wani hali na daban, da ta kwashe kwanaki ta na kira bai d'aga ba, damuwar ta ta nunku sosai, mama kuma sai take cewa tayi hak'uri mana da yanda Allah ya hukunta mata, hakan ya sa Khadija tunanin ko Usman ya mutu ne dai, kawai sai ta yanki jiki ta fad'i, sai da ta kwana asibiti, a ranr Usman bai shirya tahowa ba amma dole ya taho, dan cewa ya yi neman kud'i ba zai ja mi shi rasa matar shi ba wacce ya ke da yak'inin ba zai samu kamar ta ba a wannn k'arnin, sai lokacin kad'ai Khadija ta samu sauk'i ta kuma huce. *Allah ka k'ara mana lafiya mai anfani.* 20/01/2020 Γ  12:38 - πŸ’‹πŸ˜˜πŸ’‹: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘ *KALLON KITSE* _(Ake wa rogo)_ πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘ _SAMIRA HAROUNA_ *Littatafan marubuciyar* *1* _KAUSSAR_ *2* _D'AUKAR FANSA_ *3* _BA SO BANE_ *4* _AUREN HAD'I_ *5* _SANIN MASOYI_ *6* _JIHADI_ *7* _K'ANGIN RAYUWA_ *8* _ITACE K'ADDARARMU_ *9* _KAWU NA NE_ *10* _MAATA_ *11* _KALLON KITSE..._ *SADAUKARWA GA* _MATAN FARKO_πŸ§•πŸΌ *(UWAYEN GIDA)* πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S* _(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€› πŸ’•πŸ’•πŸ’• *My Heenat, My BK, My Meelat*πŸ’žπŸ’žπŸ’ž _Alkhairin Allah ya lullub'e min ku, ina k'aunar ku._😘 ```Fatan alkairi masoya``` *MOMYN DADY, KI JI DAD'IN KI WANNAN PAGE TA KI CE KYAUTA.* πŸ˜‰ _Bismillahir rahamanir rahim_ *13* Kullum taresu ke idan dare ya yi har ba ya son rabuwa da iyalin shi, kuma bai sake wani tafiya ba har sai da ta yi arba'in, sabon gidan da ya gina mu su matsakaici daidai da rayuwar su suka tare, haka suke rainon Bilal cikin kulawa da so da k'auna, ta b'angare d'aya kuma ta na ci gaba da zuwa makarantar ta, kasancewar babu nisa da gidan su da makarantar ya sa take aje Bilal nan kafinta wuce, idan ta sauko ta biyo ta d'auko shi, a haka dai har ta kammala karatunta lafiya, haka ma Usman ya na k'ara samun hab'aka a kasuwancin shi, a lokacin da ya ke tunanin nemawa Khadija aikin karatun da ta yi, sai kawai ta shawarce shi kan ta na son fara kasuwanci, ta na so Ashir ya fara kawo mata kwanuka da karap (jug) da sauran kayan anfanin mata ta na siyarwa, ya ji dad'in haka kuma yace nauyi ne a kan shi ya mata hakan, Ashir ya nema su ka yi magana sannan ya fara bashi *million d'aya* dan a fara da ita, cikin ikon ubangiji kuma sai Allah ya sawa kasuwar albarka, duk da komai bashi ne, amma dai ana samu sosai, lokaci na tafiya kamar walk'iya in da abubuwa ke faruwa, ta na taimakon danginshi da danginta da ita kan ta ma da kasuwancinta, in da

Table of Contents

Chapters

117 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117