Chapter 19
Chapter 19
da yer uwar mu alkairi, dan gaskiya na yarda da tarbiyar shi da kuma dattakon iyayensu, sai dai Usman ba kamar sauran maza bane, zai iya nuna cewa kamar Khadija ba tsararsa bace irin tafi k'arfin shi, ni kuma a gani na Khadija ce za ta yi sa'ar samun miji kamar shi, sannan burin mu anan dukanmu bai wuce mu bawa Khadija mijin daya dace da ita ba, sannan mun wa mahaifin mu alk'awarin kula da ita har zuwa lokacin da za mu damk'a ragamar kula da ita a hannun mijin da ya dace, da wannan nake neman shawararku da idan kun amince, sai mu je har gidansu Usman sannan mu nema wa yer uwar mu auren nagartattacen mutum, ba fad'uwa mu ka yi, kuma ba abun kunya bane dan mu muka fara zuwa da maganar, hakan ba yana nufin mun arhantar da ita bane, sai dai ma k'ok'arin kare mutumcinta, ko ya ku ka gani?" Bashir ne yace "Tunda dai har ka yarda da shi ai ina ganin ba wani abu, kawai ayi d'in, burinmu shine ganin Khadija ta dawwama cikin farin ciki." Kallon mama Ashir ya yi yace "Mama ba ki ce komai ba?" Murmushi ta yi tace "Me zance ni, bayan iyayenta kuma yan uwanta sun gama magana, babu abin da zance sai dai addu'a da kuma fatan Allah sanya alkairi." "Ameen mama." Suka amsa a tare, Ashir ne yace "Yanzu tunda dukan mu mun amince, gobe zan je na samu kawu *Kabir* na fad'a ma sa, in ya so sai muje tare, amma ku sani dukanmu za mu tafi neman auren nan." Naseer ne yace "Kar ka damu ai, ni ne ma gaba saboda munfi kusa da ita." Habeeb ne yace "Kai dallah can malam, kowa a gidan nan ai yasan Khadija tafi shak'uwa dani." Wani wawan tsaki Ashir ya yi yace "Aikin banza, ai sai kuyi kuma, amma da yanzu za'a tambaye ta na tabbata ni ne farko." Bashir ne yace "Hum! Kun manta sunan da ta ke kira na da shi ne?" Dariya su ka yi sai Mansur ne yace "Dan ta kira ka da hannayenta sai me?" "Sai ya na nufin mahimmanci na a gareta." Ya fad'a har da juya baki, dariya Mama ta yi ta Mik'e tace "Sai da safenku." "Sai da safe mama." Su ka amsa. *Wannan* k'aramar magana ita ce ta girmama har aka fara shigar da maganar aure tsakaninsu, sai da komai ya daidaita ana shirin kawo akwatina kad'ai yan uwan su ka sanar da Khadija a tunaninsu sun mata (surprise) za ta yi murna, Khadija ta girgiza, amma jin dalilinsu na yin haka domin farin cikin ta ne kawai, a lokacin kukan da take bawai na farin ciki bane, amma saita share ta nuna musu na dad'i ne take, dukansu ta had'a ta rumgume tace "Na yi sa'ar samunku a matsayin yan uwa." A wajen Usman kuma har ya fara bore ya na nuna baya so, ya fad'a mu su kuskuren fahimta ne kawai, amma ko zaiyi aure yanzu ba yarinya kamar Khadija ya ke so ba, sai mahaifiyar shi ce ta zaunar da shi ta nusar da shi alfanu da alkairan da zasu iya tasowa sakamakon auren shi da Khadija, amma duk da haka sai da yace "Hajia, wallahi na tabbata ita ma yarinyar nan bata so na, zaifi kyau ku bar kowa ya zab'i wanda ya masa, amma kar ku ce za ku had'a mu saboda rashin fahimtar da Ashir ya yi." Sosai ta tank'wara shi har ya samu ya sauko ya amince, amma yace saboda sune kawai, ita kuma mahaifiyar ce tace "In dai kuma har saboda mu kayi, to ka sani ba kai ba nadama har abada, insha Allahu wannan auren zai zamar maka alkairi, ba za ka tab'a kuka da zab'in mu ba." Magana ta kankama sosai, amma ango da amarya babu wani mai shiri ko farin ciki, an saka wata *hud'u* mai zuwa, yan uwan amarya da mahaifiyar ta sun dage wajen shirin bikin autar su, gaisuwa kad'ai ke had'a Usman da Khadija a waya, su na gaisawa zata aje wayar ko shi ya aje, kuma kamar an k'yasta ashana sai gashi an cinye wannan lokacin da aka saka, ba dan Usman ya so ba ya baro harkokinshi ya zo sabgar bikin shi, fad'an irin tartsatsin da aka yi a bikin ma b'ata lokaci ne, dan yan uwa biyar sun yi bajinta sosai wajen k'ayatar da yer uwarsu, sai dai kamar yanda Usman ya ke ganin baiyi wani bajinta ba sosai, hakan ya sa yace ba ya buk'atar komai daga gare su shi ma sai amaryar kawai, hakan kuma ya birge mutane da dama, haka akayi wannan walima aka kai amarya d'akin mijinta, kuma duka yan uwa biyar d'in su suka saka k'anwar su tsaka suka iza k'eyar ta har ta shiga d'akin ta. Gidan malam Ali da shima ya gada a wajen na shi tsohon, matsakaicin fili ne sai d'aki ciki da falo, sai ban d'aki a farfajiyar gidan da kuma k'aramar runfar da aka yi ta tΓ΄le aka aje kayan abinci ya zama wajen girki, d'akin nan tamtsam aka mi shi da kaya na gani na fad'a, bayan yan kai amarya su tafiyar su aka bar ango da amarya, shima fita ya yi kafin dare ya k'ara yi ya dawo gidan. Zaune ya same ta akan gado fuskarta rufe, k'arasowa ya yi tare da "Amincin Allah ya tabbata a gare ki." Wayu ta had'e ta rintse ido gabanta na fad'uwa tace ".. *Allah ka mana kyakyawan k'arshe.* 14/01/2020 Γ 14:03 - πππ: ππππππππππ *KALLON KITSE* _(Ake wa rogo)_ ππππππππππ _SAMIRA HAROUNA_ *Littatafan marubuciyar* *1* _KAUSSAR_ *2* _D'AUKAR FANSA_ *3* _BA SO BANE_ *4* _AUREN HAD'I_ *5* _SANIN MASOYI_ *6* _JIHADI_ *7* _K'ANGIN RAYUWA_ *8* _ITACE K'ADDARARMU_ *9* _KAWU NA NE_ *10* _MAATA_ *11* _KALLON KITSE..._ *SADAUKARWA GA* _MATAN FARKO_π§πΌ *(UWAYEN GIDA)* πΈπ¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S* _(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_π€π€ ```Fatan alkairi masoya``` _Bismillahir rahamanir rahim_ *11* "Kai ma haka." A hankali ya zauna bakin gadon ya aje ledojin hannun shi, kallonta ya yi ya d'anyi shiru, dama dai fuskarta a rufe take, dan haka ita ma ta yi shiru, kowa da abin da yake sak'awa a ran shi, kusan minti sha biyar su ka d'auka a haka kafin ya sake kallonta ya d'anyi gyaran murya yace "Ko za ki iya bud'e fuskar ki." Shiru ta yi kamar ba ta ji ba kuma bata bud'e ba, numfashi ya sauke cike da nuna kasala ya zuro hannayenshi ya yaye mayafin, fad'uwar gabanta ne ya nunku, shi kuma ya kafe fuskarta da babu ko d'igon kwalli da ido, sai dai lumshe ido ya yi saboda matsowar da ya yi kusanta k'amshin turaruka ne suka bigi hancin shi, ajiyar zuciya ya sauke yace "Ya kamata muje mu yi alwala ko?" Ba tare da tace komai ba ta fito da k'afafun ta daga tank'warewar da ta mu su ta sauka daga kan gadon, bin bayanta ya yi su ka samu buta su ka yi alwala su ka dawo, hijab ta saka ta shinfid'a sallaya ya shiga gaba ya kabbara sallah, raka'a biyu su ka yi su ka sallame, juyowa ya yi ya na fuskantarta ya zuro hannunshi zai dafa kanta dan yin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117