Skip to content

Chapter 61

Chapter 61

Kallon Kitse Book One Complete Hausa Novels 1,200 words 0 views Progress saved
Download Book

ka." Da yatsanshi ya nuna kan shi yace "Ni ne marar kunyar? Ni ki ke fad'awa haka Khadija?" "An fad'a, da abin da za ka yi ne? Mugu azzalumi, ni dama nasan tunda ka ce za ka k'ara aure nasan abin da za ayi kenan, aikin banza kawai." Da sauri Bilal ya tsaya tsakiyar su cikin d'aga murya yace "Abba." Kallon shi ya yi ya d'an shafa kan shi, kamar zaiyi kuka yace "Abba nasha ganin ku kuna rigima akan abubuwa dayawa, amma ban tab'a ganin ku a irin wannan yanayin ba." Hannun shi ya kama su ka nufi komawa cikin gidan, juyowa yaron ya yi ya na kallon mahaifiyar shi haka ita ma shi ta ke kallo, saida ta ga shigewar su ta juya ita ma dan ba zata tsaya rok'on shi akan Bilal ba, tunda ta haiho shi dai ai ta san ba zai raba ta da shi ba, mai gadi ta barwa kayan Bilal ta fice daga gidan ta hau adaidaita, kai tsaye kuma gida aka aje ta ta shiga ciki cike da kunya da kuma tafasar zuci, kamar yanda har yanzu gidan su ba su daina al'adarsu ba ta taruwa falon mahaifiyar su haka ma yau, da sallama ta shiga duk da taji hayaniyar su ba lallai ta bari su ji ba, ai kuwa ba su ji ba har saida ta shigo d'akin ta aje jakar ta k'ofar d'akin, kowa mamaki ne ya kama shi in da ake fad'in "Khadija, ke ce a wannan daren?" Ashir ne ya d'ora da "Lafiya dai ko auta? Daga ina ki ke haka k'arfe goman dare?" Saida ta k'are kallonsu duka taga yan uwan ta ne kafin ta k'arasa shiga ta je gaban Mama ta zauna kanta k'asa, Mama ce ta fara dafa ta tace "Khadija, lafiya na gan ki haka? Wani abu ne ya faru?" Cikin k'unar zuci tace "Usman ne yace na zo gida sai ya neme ni, Bilal ma na tare da shi." Mansur ne yace "To me ya sa? Me ki ka mi shi haka da ya d'auki wannan matakin." Kallon shi ta yi tace "Saboda amaryar shi mana, saboda munyi fad'a da amaryar shi shine yace na taho gida, kuma wallahi ba zan koma gidan shi ba tunda abun shi akwai rashin mutumci, gwara su zauna shi da ita har duniya ta tashi." A hankali Habeeb ya sa hannun shi ya shafi fuskar ta yace "Yatsu ne fa akan kumatunta, marin ki ya yi?" Ya tambaye ta, saboda idon ta sun rufe ya sa tace "Eh mana, bayan mari ma wace magana ce bai fad'a min ba." "Mari kuma?" Cewar Ashir ya na sake juyo da fuskar ta, Naseer ne ya katse shi da cewa "Ai kuwa Usman bai nemi zaman lafiya ba, yanzu saboda wata shegiyar yarinya zai mare ki, bari su ga yanda ake rashin mutumci kam." Mama ce ta katse shi da cewa "Kai miye haka? Wai me ya sa ku ke haka? Me ya sa kuke son mantawa da baya?" Shirun da su ka yi ne ya sa Mama cewa "Shikenan ita tafi k'arfin a b'ata ran ta kenan? Karfa ku manta shekaru suka yi a tare, shine yanzu daga yar k'aramar matsala za ku wani fara maganar rashin mutumci, to ba na so kunji na fad'a mu ku, kuma ma ita ta fad'a mu ku gaskiyar abin da ya faru? Ita ba babba bace ba? Meya hana ta yi hak'uri da duk abin da ta gani ko ta ji? Ai dama na fad'a mi ki dole sai kin kau da kai musamman yanzu da suke kan ganiyar cin amarcin su, zai iya yin komai saboda giyar da ya ke kurb'a." Cikin rashin jin dad'i Bashir yace "Amma kuma Hajia har da duka? Koma me ya faru ai ya nutsu ya san me yake, amma tab'a lafiyar ta gaskiya fa ba abin da za mu iya jura bane." Cikin hushi Habeeb yace "To ni abin da yafi k'ona min rai shine wai akan wata amarya, to k'ara aure hauka ne da zai kwance mi shi kai, gaskiya har da iskanci." Naseer ne yace " Wallahi magana zan masa, dan ba zai mare ta a banza ba, in ba haka ba kuma to fa abubuwa marasa dad'i ne za su fara faruwa tsakani wanda basu faru ba a baya." Cikin nutsuwa Ashir yace "Kunga ku kwantar da hankalin ku, yanzu dai ba yace ta zo ba har saiya neme ta? To ai sai mu jira shi har ya neme ta kamar yanda yace, kunga sai muyi magana yanda ya kamata." "Ni ko ya zo ma ba zan koma ba, Usman ya gama tozartani a gaban d'ana da matar shi, gaba d'aya nunawa ya ke kamar ba mu tab'a zaman mutumci da shi ba, dan haka ko ya zo ma babu in da zanje." Ta na gama maganar ta ta mik'e ta nufi tsohon d'akin ta da tasan dama nan za ta sauka, Mama ma mik'ewa ta yi ta lek'o k'ofar d'akin ta d'auki jakar ta ta kai mata d'akin kafin ta fito, yan uwan kam sun jima su na tattaunawa dan ransu ya b'ace sosai, in da Khadija ma sam kasa bacci ta yi a daren saboda tunanin sauyin rayuwa, mutumin da ko tafiya zaiyi wacce ta zama dole da k'yar ya ke iya rabuwa da ita, wasu lokuta kuma idan da sarari tare sukan tafi duk in da zaije, ko suje da yaron su ko kuma su bar shi su tafi, amma yau shine ya kore ta daga gidan shi wai saiya neme ta, k'wafa ta yi tare da gyara kwanciya a ran ta tace "Wallahi ba zan koma ba sai ya gane kurensa, har ni nayi kama da macen da zai ce jeki saina neme ki." Wata k'wafar ta sake yi cikin b'acin rai. A wajen.su Usman kuma da k'yar ya rarrashi Haseenah ta hak'ura da taga Khadija ta tafi, ko da ya kwantar da Bilal ya dawo ya dinga mata abubuwa kamar tsohon bazawari, ita kam har kunya ma ya fara bata, haka dai suka kasance har gari ya waye. Kasancewar babu karatu a ranar ya sa Bilal shiryawa ya yi zaune a falon mahaifiyar shi ya na kallo, haka yake zaune wurin nan yunwa na gwagwuyar mi shi ciki amma babu yanda zaiyi, d'akin mahaifiyar shine ke da abubuwan ci kuma a rufe yake, har saida ya kai ya fito wajen mai gadi ya zauna ya na kallon hanya, lokacin ne Usman ya gamo shiriritar sa ya fito neman Bilal, ganin shi tare da mai gadi ya sa ya kira shi suka koma ciki, tare suka karya kumallo ya tashi zai fita, kallon shi Bilal ya yi yace "Abba dan Allah ka tafi da ni wajen Mummy." Cikin d'aure fuska yace "Ni na fad'a ma ka wajen ta zanje?" A hankali ya girgiza kai, ganin ya juya zai fita ya sa shi k'ara cewa "To Abba ka tafi da ni sai ka aje ni wajen Hajia." Cikin hassala ya juyo yace "Wai me ya sa dole sai na tafi da kai? Kai ba za ka iya zama gida ba idan ba karatu? To ba can wajen zanyi ba ka zauna tare da Mamar ka." Kallon Haseenah Bilal ya

Table of Contents

Chapters

117 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117