Skip to content

Chapter 76

Chapter 76

Kallon Kitse Book One Complete Hausa Novels 1,200 words 0 views Progress saved
Download Book

jinjiri, matsala ce ta faru da tasa dole sai na bar gidan nan na wani lokaci, ku yi hak'uri, na bar ka lafiya." Ta na gama fad'a ta shiga adaidaitar suka wuce, da kallo ya bisu ya na fad'in "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un, ita kuma amaryar da abin da ta zo da shi kenan? Wannan wace irin jaraba ce, mata da mijin ta kullum cikin farin ciki, idan ka ji hayaniya to suna wasa ne kamar yanda su ka saba, amma yau gashi su na shirin rabuwa dalilin wata, kai Allah ya kyauta." Usman na ciki shi da Haseenah bai san tsiyar da ake ba, ba jimawa kam adaidaita ya sada Khadija da gidan su, Mama na ganin su da kaya ta fara salati da sallalami, kai tsaye d'aki ta nufa ta aje kayan ta ta wuce d'akin ta, tashi Mama ta yi tabi bayan ta sai matan yan uwan ta ne su ka bisu da ido, matar Habeeb ce kad'ai ta iya cewa "Aifa lokacin ya yi." Shiru sauran su ka yi dan suma kawunan nasu a rarrabe suke, kowa da b'angaren da yake saboda suma akwai uwayen gida akwai kuma amare. Babu abin da Khadija ta b'oyewa maman ta duka ta fad'a mata, duk da taji ba dad'i sosai amma sai bata nuna mata ba, kallon maman ta tayi tace "Dan Allah Mama taimaka min da maganin ciwon kai." Tashi kawai Mama ta yi ta d'auko ta kawo mata tasha ta kwanta, matar Mansur ta shigo d'akin dan su kwashi labari sai dai ta samu Khadija har ta fara baccin wahala da fuska har yanzu a sumtume, sam Mama ba ta fad'awa 'yan uwan ta ba ko a waya sai dare da suka dawo su ka tarar da wannan abin takaici, lokacin Khadija zazzab'i ya sake rufe ta, Naseer har da k'walla ya yi da ya kalle ta, yanda ya sunkuyar da kai ne ya sa Habeeb dafa shi, goge fuskar da ya yi ne ya tabbatar musu kuka yake, Bashir ne yace "Kai haba dai maza, kuka fa? Ai ba kai ya kamata ka yi kuka shi ya kamata ya zubar da hawaye." Wasu hawayen ne suka sake taho mi shi yace "Yanzu domin Allah me ya sa Usman ya yi haka? Mufa mun bashi ita ne da tunanin zai kula da ita, me ya sa zai mana haka yanzu? Saboda kawai ana ganin ita marainiya ce mahaifin ta ya rasu." Sun jima d'akin ta suna tattaunawa in da take kwance ta dunk'ule, saida dare ya yi suka tashi suka koma nasu dak'unan, saida tasha magani kafin ta sake kwantawa, sai dai ba ta yi bacci ba har aka kira sallah asuba, sallah ta yi ta sake komawa ta kwanta ta na istigfari tasbihi da hailala da hannun ta na dama. Ko da Usman ya fahimci basa gidan haka kawai yaji bai wani damu ba, hakan ya sa ma da safe ko da ya je gida ya samu su Hajia da maganar ya kuma fad'a mu su kar suce za su je su dawo da ita, harda had'a su da Allah akan su barta harta shiga hankalin ta, Bilal kuma d'an shi ne ba ta isa ta raba shi da shi ba, amma malam yace sam ba da shi za ayi haka ba, a k'arshe ma tambayar su dalilin faruwar haka akayi, fad'an Hajia shine "Makulli Usman ya bawa Haseenah ta aje na mota da zai tafi, ita kuma ta tashi fita tace ta bata, shi kuma yace kar aba kowa idan za'a fita a fad'a mi shi zai aiko da wani ya kaisu duk in da za su je, shine ta turmushe yarinya da k'aramin ciki ta karb'i makullin, dalilin hka fa ya kusa sawa ta yi b'ari." Duk da jin haka yace zaije ya dawo da ita gidan ta, kuma kamar yanda ya fad'a ya cika maganar shi, amma maganganu mabanbanta ya ci karo da su, musamman da suka fad'a mi shi har da duka, har d'akin Khadija aka mi shi jagora ya ganta kwance da k'arin ruwa a hannu, dan tunda ta yi sallah asuba zazzab'i ya sake rufe ta, hakan ya sa Naseer ya d'auko likita har gida aka dubata, sosai suka nuna mi shi b'acin rai da cewa ba za ta koma ba har sai Usman ya dawo hankalin shi, baiga laifin su ba kam dan ya sa dole wata rana zai neme ta, haka malam ya juya rai b'ace da kuma kunyar abin da ya aikata, tun a hanya yace Usman ya same shi gida za su yi magana, da "To Baba." Ya amsa. *Ku na ganin zaije? Yanzu fa Haseenah ita kad'ai ce.* Saida ya sake wanka ya shirya yace "Amarya ta zanje gida na dawo, amma ba zan jima ba kinji, ki kula da kan ki." Kallon shi ta yi ta na k'ara rufe jikin ta da zanin gado tace "Gida kuma? Na d'auka d'azu ka ce min gida ka tafi, ya da wuri haka za ka koma." Ya na gyara zaman hular sa yace "Eh wallahi Baba ne wai ya ke son gani na, amma na san ba zan jima ba ai zan dawo." Shiru ta yi a zuciyar ta tace "To idan fa yanzu ma dawo da Khadija za su tafi? Dole na yi wani abu." Shagwab'e fuska ta yi tace "Yanzu tafiya za ka yi ka barni a haka? Ba ka da matsala kenan tunda ka samu biyan buk'atar ka ko?" K'ok'arin saukowa ta fara daga kan gadon ta na fad'in "Shikenan ai ka tafi." Matsowa ya yi kusan ta zai kamo hannun ta ta kubce ta shige ban d'aki, bakin k'ofar ya tsaya yace "Haba ke kuwa, kar ki yi hushi mana, kinfa san ba na son b'acin ran ki ko kad'an." "Ahhhhhhh, wayyo Allah ciki na, marata." Fad'in Haseenah daga cikin ban d'aki, bai tsaya tunanin komai ba ya kutsa ciki ya same ta zaune dafe da ciki alamar fad'uwa ta yi, bai tsaya komai ba ya d'auko ta sai kan gado ya dire ta, kallon ta yake ciki da damuwa ya na rik'e da hannayen ta yace "Garin yaya ki ka fad'i haka? Haseenah karfa ki mana asarar kyautar nan da Allah ya bamu, kinfi kowa sanin lokacin da na d'auka ina fatan Allah ya sake bamu haihuwa, ina son na ga gidan nan ya cika da yara kuma ya zamana ke ce uwar su." Yanda ya k'arashe maganar kamar zaiyi kuka ne yasa tace "Ka yi hak'uri dan Allah, ni ma santsi ne kawai ya kwashe ni, ban kula ba sai ji na yi na fad'i saboda rai na a b'ace yake." Kallon ta ya yi yace "To me ya b'ata mi ki rai haka da har ki ke neman ja mana babbar asara." Cikin turo baki tace "To ba kai ne ka ce zaka fita ka bar ni ba, ni kuma wallahi ba na so ka tafi, satin ka biyu fa baka gari, kasan dai dole munyi kewar ka mu na buk'atar ka a kusa da mu, shine kawai daga ka samu yanda ka ke so sai ka ce za ka fita." Da rawar jiki yace "Ai dai fitar ce ba kya so ko? To na fasa, kin gani ma?

Table of Contents

Chapters

117 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117