Skip to content

Chapter 110

Chapter 110

Kallon Kitse Book One Complete Hausa Novels 1,195 words 0 views Progress saved
Download Book

Bilal shekara nawa mu ka d'auka muna neman haihuwa, amma zuwan Haseenah gidan nan sai gashi Allah ya azurtani da nawa cikin nima, watak'ila hakan ya faru ne saboda hak'urin da mu ka yi da kuma tsarkake zuciya ta da na yi wajen zama da ita, ba ka tunanin yanzu idan na sa ka dawo da ita Allah ya sake mana wata rahamar ta hanyar da ba mu yi tsammani ba?" Ganin ya yi shiru alamun maganganunta na ratsa shi ya sa tace "Za ka iya tuna a cikin karatun da ka ke koya mana kai ka bamu labarin abin da ya faru tsakanin *sayyidi na Abbakar* da *musd'ahu* mai hidima gare su kuma wanda su ke d'aukar nauyin shi, Musd'ahu na d'aya daga cikin wanda suke yayata k'azafin da akawa *Nana Aisha (RA)* cewa ta yi zina, a lokacin da ran sayyidi na Abbakar ya b'aci ya kori Musd'ahu daga gidan shi tare da cewa ba zai sake d'aukar nauyin shi ba, me Allah yace akan haka, Allah ya na son masu yafiya, idan ka yafe kuma sai ka manta da komai, sannan ka k'ara da kyautatawa, to hakanne ya kamata ya faru a yanzu, ka yafe mata gaba d'aya, sannan ka manta da abin da ya faru ka daina tunawa, kyautatawar da za ka mata kuma bai wuce ka dawo da ita d'akin ka ba ta haifi abin da ke cikin ta ba ta kuma raine shi gaban ka, kar kaga ka na keyawa da masoyan ka za su kula maka da d'an da za ta haifa, rik'on yaro sai uwar shi, duk wanda kaga bai rayu da mahaifiyar shi ba dan hakan na mi shi dad'i bane, dan Allah miji na, Usman na Nana, ka saurari matarka mana ka tuna had'uwar ku ta farko da ita da kuma yanda zaman ku ya kasance, saika yanke hukunci." Shafa kumatun shi ta yi ta d'aga shi zata koma d'aki dan ta bashi damar yin tunani, sumbatar kumatunshi ta yi ta rad'a mi shi a kunne cewa "Kar ka manta Khadija na matuk'ar son ka sosai, kai ne rayuwa ta babban mutum." Da murmushi kawai ya bita da kallo harta shige d'aki, ya jima nan zaune ya na tunanin abin da ta fad'a mi shi, har ga Allah babu ko k'aunar Haseenah a zuciyar shi bare soyayyarta, amma zai dawo da uta saboda farin cikin Khadija kawai, amma kuma ba yanzu sai ta shiga watan haihuwar ta kad'ai zai dawo da ita, kamar yanda ta sa Khadija zama a gidan su ita ma saita d'and'ana zaman gidan sosai ya ratsata kafin, tashi ya yi ya shiga d'aki saida su ka yi shirin kwanciya kafin ya fad'awa Khadija ya ji zai dawo da ita amma da sharad'i, da sauri tace "Sharad'in me?" "Zan dawo da ita amma ba yanzu ba, idan hakan ya mi ki to, in kuma bai mi ki ba to abar maganar, sannan zan dawo da ita ne ba dan ina buk'atar zamanta a gida na ba sai dan kin matsa." Kallonta ya yi yace "Kin yarda?" Da sauri tace "Na yarda Abban Bilal, duk da haka na san ba zaka tauye hakk'in ta ba." Daga ranar ya samu zaman lafiya Khadija ta daina mi shi magana, haka aka kwashe wasu watannin a lokacin cikin Haseenah ya shiga watan haihuwa, taje asibiti aka bata sati biyu idan bata haihu ba ta koma, a lokacin Khadija da Hajia da Usman da malam suka je gidan su Haseenah biko, abun ya bawa Haseenah kunya sosai ta yanda ta dinga kuka ta na neman gafarar Usman da Khadija, nan iyayen ta ma suka basu hak'uri kafin aka k'ara mata fad'a da nasiha, Khadija da kanta ta tayata had'a kaya dan da tace ma su bari har gobe Khadija tace a'a, tsaf suka had'a kayan suka fito tare da ciki kowace ta na turawa, kayan Usman ya karb'a ya kai mota kafin suka tafi, gida ma saida malam ya sake mu su jan kunne tare da tunatarwa akan zaman aure ibada ne kafin Usman ya mayar da su gida, suna fita Haseenah ta sake fashewa da kuka ta rik'e k'afar Khadija tace "Aunty Khadija ki yi hak'uri ki yafe min dan Allah, wallahi na yi nadamar abin da na aikata." Kamata Khadija ta yi tace "Haseenah na fad'a mi ki ba komai wallahi, na hak'ura har abada kuma, Allah dai ya k'ara had'a kan mu." Bilal ne ya fito daga d'aki da riga a hannu ya mik'owa Khadija yace "Mummy taimaka saka min rigar nan, wuyanta matse ni yake." Da sauri Haseenah ta tara mi shi hannu tace "Kawo na saka ma ka yarima." Bata ya yi ya na kallon mummyn shi a d'ard'ar ya matsa kusa da ita, saida ta saka mi shi ta kalle shi tace "Yarima ka yi hak'uri ka yafewa auntynka kaji, na yi nadamar abin da na yi." Kallon mummyn shi ya sake yi ta sakar mi shi murmushi hakan ya sa ya rumgume Haseenah yace "Aunty amarya, uwa fa ba ta neman yafiyar 'ya'yan ta." Kallon shi ta yi tace "To in dai uwa ce ni ai ba aunty ya kamata ka kira ni ba." Murmushi ya yi sosai ya kalle ta da kunya yace "Mummy." Har zuciya Haseenah taji muryar Bilal ya kira ta da sunan uwa, rumgume shi ta yi take taji wata soyayyar shi ta d'arsu a zuciyar ta, sun jima nan har Usman ya shigo kafin kowa ya nufi na shi d'akin, wani irin sanyi Haseenah taji sai take ji ashe zaman lafiya da wanda Allah ya had'a ka zama da shi dad'i ne da shi, sai taji kamar yau ne aka fara kawota gidan tare da k'udurawa a ranta zata wa Khadija biyayya ko da kuwa za ta zama baiwarta ne hakan ba zai dame ta ba, har ta yi shirin kwanciya Usman ya shigo da doguwar riga yace ta same shi falon Khadija, da to ta amsa mi shi ya fice ko kallon ta baiyi ba, haka ta fito jiki a sanyaye dan tasan yanzu ba mutumcin ta Usman zai gani ba, kuma kamar yanda ya fad'a a gidansu cewa ya fa zo ne saboda Khadija ce ta matsa, to tabbas tasan dawowar nan da ta yi zaman Khadija ne za ta yi, sun samu Khadija zaune da alama su take jira, zaune ya yi kusan Khadija Haseenah kuma cike da kunya ta zauna k'asa, Khadija ce tace ta zauna sama amma tace a'a tafi jin dad'in nan, Usman ne ya gyara murya ya fara magana kamar haka. "... 15/03/2020 Γ  23:06 - πŸ’‹πŸ˜˜πŸ’‹: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘ *KALLON KITSE* _(Ake wa rogo)_ πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘ _SAMIRA HAROUNA_ *Litattafan marubuciyar* *1* _KAUSSAR_ *2* _D'AUKAR FANSA_ *3* _BA SO BANE_ *4* _AUREN HAD'I_ *5* _SANIN MASOYI_ *6* _JIHADI_ *7* _K'ANGIN RAYUWA_ *8* _ITACE K'ADDARARMU_ *9* _KAWU NA NE_ *10* _MAATA_ *11* _KALLON KITSE..._ *SADAUKARWA GA* _MATAN FARKO_ πŸ§•πŸΌ *(UWAYEN GIDA)* πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S* _(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€› πŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”š ```Fatan alkairi masoya``` *ALHAMDULILLAH ALA NI'IMATUL ISLAM* _Bismillahir rahamanir rahim_ *40* "Haseenah, Allah ya nufa dai akwai sauran zama tsakani na dake, ina fatan abubuwan da suka faru a baya sun koya mi ki wa'azi, Haseenah zan fad'a mi ki wata magana wacce a

Table of Contents

Chapters

117 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117