Chapter 57
Chapter 57
ta kud'i a fara mata magani, Khadija na kallo suka dawo suka nufi b'angaren ta, ya jima ya na bata magana da rarrashi kafin ya fita, a gida ma suna tafiya mahaifin ta ya fito ya hau moton shi, bai zame ko ina ba sai *pharmacie salfiya* cibiyar magunguna na addini, da ya fad'a mu su matsalar sun zo ya zo da mara lafiyar da suga yanayin jikin ta, amma tunda ya riga ya zo sai suka bashi wanda ya dace da abin da ya fad'a, amma sunce in har ba ta daina ba to su kawo ta wajen su dan su duba ta, ya na barin nan gidan Haseenah ya wuce kai tsaye, dan suna so su d'auki matakin tunda wuri, Khadija na ganin shigowar shi amma ba ta kawo komai a ran ta ba dan bata nufin kowa da sharri, har falon Haseenah ya ke zaune ya na fad'a mata yanda za ta yi anfani da su, saida ya gama kafin ya bar gidan, Haseenah na ganin fitar shi ta kai magungunan d'aki ta aje, d'ibar wasu ta yi daga cikin wanda za ta yi anfani da su yanzun ta zubar. Usman kuma na barin nan gidan su ya nufa, Hajia ya fad'a ma halin da ake ciki, ta jinjina al'amarin tare da dogon nazari akai, sai dai zuciyar ta ta kasa yarda cewa Khadija za ta iya cutar da ita, dan da za ta hana ta zaman gidan ai da bata ma barta ta shigo ba, amma dai "Allahu a'alam." Cewar Hajiar, ya na fita Aziza ta taso maganar dan ta na waje ta ke jin wasu maganganun, cike da damuwa Hajia ta fad'a mata yanda aka yi, ke Aziza ki na fitowa sai ki ka kira Hassana ki ka fad'a mata, kafin ka ce kwabo maganar ta karad'e yan uwan mata ana ta caccakar Khadija da maganganun b'atanci. Yamma na yi Haseenah ta shiga madafa ta d'ora girki, sai bayan magriba ta k'arasa ta yi wanka ta shirya, ko da ya shigo ya yi wanka ya sake kaya ya zauna wajen cin abinci, kallon shi ta yi tace "Bara na kira su aunty Khadija su zo mu ci abinci." Da ido kawai ya bita har ta fita, jim kad'an su ka shigo tare da Bilal, Khadija ba wai ta shigo bane saboda ta na son cin abinci sai dan gudun matsala, akan cinyar sh ya zaunar da Bilal in da Haseenah ta fara zuba abincin, a faranti d'aya suka fara ci shi da Bilal, amma Bilal na kai lomar farko ya kalli Haseenah ba ko k'yabtawa, da k'yar ya samu ya aika lomar ta gangara cikin shi, Khadija da Usman ma na kai wa suka yi saurin furzo shi waje suna goge baki, haka ita ma Haseenah ta na sawa ta firzo ta na ta faman goge baki, Usman ne ya kalle ta yace "Haseenah me ye haka? Kin d'and'ana girkin nan kuwa kinji?" A marairaice ta kalle shi tace "... *Yasin na gaji.* 11/02/2020 Γ 18:31 - πππ: ππππππππππ *KALLON KITSE* _(Ake wa rogo)_ ππππππππππ _SAMIRA HAROUNA_ *Litattafan marubuciyar* *1* _KAUSSAR_ *2* _D'AUKAR FANSA_ *3* _BA SO BANE_ *4* _AUREN HAD'I_ *5* _SANIN MASOYI_ *6* _JIHADI_ *7* _K'ANGIN RAYUWA_ *8* _ITACE K'ADDARARMU_ *9* _KAWU NA NE_ *10* _MAATA_ *11* _KALLON KITSE..._ *SADAUKARWA GA* _MATAN FARKO_ π§πΌ *(UWAYEN GIDA)* πΈπ¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S* _(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_π€π€ _*H. UMAR*, mahaifin da ya fi na kowa, ina alfahari da kai Baba na, wannan sadaukarwa ce gare ka kai kad'ai, ka cancanci fiye da ita ma, ka huta ka ju dad'in ka, Allah ya k'ara girma da lafiya dattijon arzik'i, *kut.kut.kut.*π kaza._ ```Fatan alkairi masoya``` _Bismillahir rahamanir rahim_ *22* "Wallahi bansan ya akayi gishirin nan ya yi yawa haka ba, ni fa lafiya k'alau na kammala girki na, kuma babu yanda za ayi na yi girki ban d'and'ana na ji yanda ya ke ba, sannan idan ka duba ai haka ba ta tab'a faruwa ba." Satar kallon Khadija ya yi wacce ta kafe Haseenah da ido ta na murmushi dan ita ta fahimci me take nufi da abin da ta fad'a, girgiza kai ya yi yace "Shikenan kar ki damu, komai ya wuce." Mik'ewa ta yi duk ta yi kalar tausayi tace "Ku yi hak'uri dan Allah, bara na samo mu ku ko soyayyen k'wai ne ku ci." Da sauri ya katse ta da "A'a ki barshi kawai, tunda hakane ake so mu zauna, ki kawo mana madara gari da sugar kawai sai mu had'a da farar shinkafar." Haka kam akayi taje ta kawo ta zuba a kofofi ta had'a ma kowa, ta mik'owa Khadija ta mik'e tsaye tace "Gaskiya ba na cin wannan had'in da dare, zanje na samu wani abu na ci da zai d'auke ni a wannan daren." Kai tsaye madafa ta nufa, ba ta ji wahalar d'aukar silallan naman dake cikin masuburbud'ar sanyi ba ta had'a sassauk'an miya mai kyau da dad'i, fitowa ta yi lokacin sai Bilal da Baban shi akan salon suna kallo ta zo gaban tebur d'in ta d'ibo sabuwar shinkafar ta zuba a faranti ta zuba miyar, Bilal ne ya juyo ya kalle ta yace "Mummy ni dai na k'oshi." "Dama bance ka zo ka ci ba." Ta fad'a ta na kai lomar farko, hankali kwance ta kammala ta tashi tace wa su je su kwanta, kallon Usman ta yi tace "Saida safe." "Saida safe." Ya amsa ya na shafa bayan Bilal, da ido ya bisu har suka b'acewa ganin shi, ya na ganin fitar su ya taso in da ta ci abinci, ya na bud'a k'aramin kwanon miyar ya lumshe ido, cokali ya sa ya d'auko tsokar nama ya jefa bakin shi, saida ya sake lumshe ido ya na taunawa ya na fad'in "Umm, umm." Da sauri ya d'ebo shinkafar kad'an a wani faranti ya zuba miyar ya dinga turawa saboda gudun kar Haseenah ta riske shi, har ya gama bata fito ba dan haka ya same ta d'akin ta na ta shirin bacci, nan ya fara lulawa da ita wata duniyar, sunyi nisa sosai ya na neman gangara kawai ta raba kanta da shi ta sauko daga kan gadon, ya na kallon ta kamar wasa ta canza kayan jikin ta ta saka hijab, ba tare da ya taso ba yace "Lafiya dai? sallah za ki yi ne?" Ko kallon shi ba ta yi ba ta nufi k'ofar fita, zaune ya tashi yace "Wai lafiya? Ina za ki je haka?" "Gidan mu." Ta fad'a ta na fita daga d'akin, da sauri ya sauko shi ma ya zura doguwar riga ya fito, ko da ya fito har ta kai farfajiyar gidan, rik'o ta ya yi yace "Haba Haseenah, ina za ki je da daran nan haka?" Kallon shi ta yi kamar za ta yi kuka tace "Ka yi hak'uri dan Allah ka barni na tafi gidan mu, wallahi ba zan iya kai safe gidan nan ba, ni kad'ai na san me na ke ji." A tak'aice dai haka Usman ya yi juyin duniya Haseenah tace ba za ta kwana gidan nan ba, shi kuma a ganin shi abun kunya ne ya kai ta gidan su, a cikin daren nan ya kai ta gidan su wajen Hajia, sam
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117