Chapter 67
Chapter 67
idan za ku yi anfani da su sai ki mata magana, saina dawo." Ya na fad'in haka ya juya rumgume da Haseenah a jikin shi, suna fita saida ya gama shinshine ta da lalabe lalabe kafin ya fito da enveloppe ta kud'i har jaka d'ari biyu ya bata, zo kaga murna ga yar matsiyata an bawa Khadija jaka talatin an bata d'ari biyu, 😂 da k'yar ya fita Murtala ya d'auke shi ya tafi cike da kewar amaryarshi. Sai da rana Aziza ta zo gidan da kayan ta, lokacin Khadija na zaune ta na waya da wata yer uwar ta (cousine) ta na mata k'orafin ta daina zuwa wajen ta, *Aishatu* ce tace "Aunty Khadija na zo Allah ko, ba dai ni nace mi ki na zo ba." "Hum, yaushe to?" Daga d'aya b'angaren ne Aishatu tace "Idan na sa lokaci na sanar da ke." "To ina jiran ki." Ta fad'a su ka yi sallama tace ta gaishe da su aunty (k'anwar maman ta). Ta ga shigar Aziza b'angaren Haseenah amma ko a jikin ta, ta na jin su suna aiki a madafa amma bata kula da tsiyar su ba, har lokacin d'auko Bilal ya yi daga islamiyya, Ashir ta kira a waya bayan sun gaisa ne tace "Yah Ashir wata alfarma a gurin ka dan Allah?" Saida ya yi murmushi yace "Auta ai babu alfarma tsakanin mu, fad'i me ki ke so yanzun nan a mi ki shi?" Cikin sanyin murya tace "Al'amarin Abban Bilal ya na buk'atar addu'a, na sani mijina ba ya hayyacin shi, yanzu haka ya yi tafiya, amma ni saida safen nan na sani, kuma ya tattara makullan mitar shi da tawa ya bawa yarinyar nan, yace sai dai idan ina buk'ata na karb'aa wurin ta, a gaskiya yah Ashir hakan zubar min da mutumci ne, na tabbata sai mun samu matsala da ita akan haka, yanzu haka Bilal na ismaliyya ba'a d'auko shi ba, shine na ke so ka samar min wanda zai dinga kai shi ya na d'auko shi har lokacin da zai dawo, tunda ka ga ma nan da kwana kad'an za'a koma makaranta (school)." Duk da ya ji ba dad'i amma cewa ya yi "Kinga kar ki damu da wannan, barta da makullan ta had'iye su in za ta iya, yanzu zanje na d'auko Bilal d'in na kawo shi gida, ba buk'atar sai an d'aukar mi shi dreba, ba wai dan ba za'a iya biyan kud'in ba, sai dan darajar Bilal ta wuce haka a wajen mu, kamar yanda na ke kai yara na da kai na haka zan dinga biyowa ina d'aukar shi shima, ko da babu mazauninshi a motar shi to za'a siyi sabuwar mota ne saboda shi kawai, motar tsiyar me da har za'a mi ki iko da ita." Ya na fad'a ya kashe wayar bin wayar ta yi da kallo tasan ranshi a b'ace ya ke, amma ta ji dad'i kuma da Allah ya bata yan uwa masu huce takaici, baifi minti sha biyar ba saiga Bilal ya shigo gidan da k'atuwar leda da kayan mak'ukashe a ciki, Haseenah da kallo ta bi shi har ya shiga tana mamakin waya kawo shi, ya na shiga ya aje ledar gaban Khadija ya shiga dan sauya kaya, ba jimawa ya dawo da wayar shi a hannu ya shiga latse latse ya na korawa da kayan mak'ulashen shi, sai daf da la'asar Aziza ta shigo wajen Khadija kawo mu su abinci, ko kallon Allah ya isa ba ta ishi Khadija ba har ta aje ta fita, ta na fita Khadija ta d'auki wayar ta kira *Hafsatu* Mak'wabciyar ta tace ta aiko yara ya amshi abinci, ba jimawa yarta ta zo Khadija ta juye mata shi a kwano d'aya ta tafi da shi, dan ita dai ba za ta ci abincin Haseenah ba in dai har za ta fitar mata da na ta da d'an ta a had'e, sai dai kome zai faru ya faru. *Tun daga wannan rana* Ashir ne ke zuwa ya d'auki Bilal da kan shi tare da yaran shi da na yan uwan shi, dama shi ya d'orawa kan shi alhakin kai yaran, sai dai ba kullum yake zuwa d'aukar su ba sai dai ya sa a d'auko su, amma yanzu da ya zamana akwai Bilal a cikin tawagar da kan shi ya ke d'auko su, hakan ya sa har yanzu bakin Khadija da na Haseenah bai had'u ba da sunan magana, ta yi shiru ta rik'e makullai ta na jiran ace kawo ta yi rashin kunya, Khadija kuma ta nuna mata ita ba bak'uwar mota ba ce, ana cikin haka hutun k'arshe ya k'are na makaranta, yara da manya aka fara hada hadar komawa, Ashir ne ya wa Bilal komai kama daga sababin kaya da abin da zai buk'ata a sabon ajin shi, har zuwa kud'in makarantar shi ya biya ba tare da sanin ma Khadija ba, saida aka kawo kayan kad'ai ta ji kuma ta gani, Usman kuma dama ba kiran ta ya ke ba, idan ma ta kira shi zai ce ta kashe zai sake kiran ta yana cikin mutane ko wani abu, sai in ya kira Bilal ne kad'ai yace ina maman ka yace gata nan, to lokacin zai ce bata waya kuma har su jima suna magana ya na tambayar ta abubuwa. Zaman Aziza da Haseenah ma ba laifi, a fuska faran-faran take mata, amma da ta bada baya za ta bita da harara dan duk ta gundureta, sai dai kuma har yanzu ba ta bar yiwa Khadija bita da k'ulli ba, duk ranar girkin Khadija idan ta aiko mu su da shi bata nunawa, dan dama Aziza sai ta tafi islamiyyar su ta dawo wacce Haseenah ce ke bata kud'in adaidaita dan ta yi nisa daga nan, kullum sai kusan k'arfe d'aya take dawowa, Khadija kuma na gama abinci da wuri tun kafin Bilal ma ya dawo, hakan ya sa da an kawo mata zata zauna ta ci ta k'oshi tasha ruwa, sauran kuma komai yawanshi da kyawunshi sai dai ta shek'a mi shi ruwa ta zuba wajen wanke wanke, da Aziza ta dawo za ta nuna ba'a basu abinci ba, haka za ta aikata ta siyo mu su awara ko soyayyan dankalin hausa, wata rana kuma su dafa indomie ko suyi taiba, kullum a takarce suke hakan ya sa Aziza da taje gida ta fad'awa Hajia, a wannan karan kam Hajia ta yarda tunda Aziza ce ta rantse ta fad'a mata, da farko ta so ta kira Usman ta fad'a ma sa dan ya mata magana, amma sai tayi tunanin ja mata matsala, dan haka saita shirya taje gidan da kan ta da nufin yi mata magana cikin ruwan sanyi, amma abun mamaki a gabanta ta zubawa su Haseenah na su abinci kwanon miya da na tuwo ta bawa Bilal ya kai, ita ma saida aka zubo mata ta ci ba wani sosai ba kafin ta mata sallama za ta tafi, saida ta shiga da nufin yi wa Haseenah sallama ta samu Aziza sun ware sai shigar tuwo suke kamar 'ya'yan yunwa, nan fa Aziza ta shiga cewa wallahi dan ta ga Hajia e ta zo ta zubo mu su, kuma d'ari bisa d'ari Hajia ta yarda, haka ta tafi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117