Skip to content

Chapter 3

Chapter 3

Kallon Kitse Book One Complete Hausa Novels 1,200 words 0 views Progress saved
Download Book

bada goyon bayan ta d'ari bisa d'ari, yanzu amincewar ku na ke buk'ata." Cike da kamala tsohuwar tace "Ba ka da matsala da amincewar mu *Fodio* (sunan mahaifin ta ne, dan haka ta ke ma sa inkiya da Fodio), tun da dai har ka shirya, kuma ka na ganin ba wata matsala, sannan matar ka ma ta amince ba tare da tashin hankali ba, ai ka ga Alhamdulillah, sai dai kawai mu bika da addu'a da kuma fatan alkairi." "Nagode sosai Mama, Allah ya k'ara lafiya da girma, yanzu kenan idan Abba ya shigo za ku iya magana da su, duk yanda ku ka yi zuwa dare idan na dawo na ji insha Allah." Kasantuwar shi d'an fari ya sa ko ido ba ta son had'awa da shi kamar ta na jin kunyar shi, ba tare da ta kalle shi ba tace "Shikenan ba damuwa, insha Allah zan fad'a ma sa." D'an gyara zama ya yi alamar zai tashi yace "Mama babu wata matsala ko wani abun da ku ke buk'ata?" "Ah, Fodio kai ne za ka bar gidan nan da wata matsala? Ai sai dai in ba ka raye, Alhamdulillah wallahi babu komai, Allah dai ya yi albarka, Allah ya sa ka gama da duniya lafiya." Sai da ya durk'usa k'asa ya amsa da "Ameen Ameen Mama, nagode sosai da addu'ar ki gare ni, ni zan wuce sai anjima idan na dawo." "To Allah ya yarda, Allah ya tsare, ka gaishe min da waccen mutumin." Dariya ya yi yace "Watak'ila fa gobe ku gan shi gidan nan, dan mahaifiyar shi ta tafi d'auko shi." Cikin wasa irin ta kaka da jika tace "Ka ce mi shi ma kar ya kuskura ya zo in har ya san ba zai taho da k'atuwar bak'ar leda ba." "Zai zo da ita Mama, ai kin san shi da k'ok'arin cefanai." "Ko dai k'ok'arin jefawa a ciki ba." Da wannan wasan ya bar gidan zuciyar shi sakayau da ita kamar kullum, dan har abada babu abin da ke dagula mi shi lissafi, b'angaren mace, Allah ya wadata shi da mata kamar Khadija, babu abin da ya nema a gurin ta ya rasa, haka ma iyaye, Allah ya bashi iyayen da su ke son abin da ya ke so, sannan su ke nusar da shi tare da kora shi da addu'a a kullum, hakan na sa shi farin ciki , kuma shima ya na k'ok'ari sosai wajen sauke hakk'ok'in duka b'angarorin, haka ne m'a sanadiyar da ta sa kullum ci gaba ya ke gani babu komawa baya ko rashin nasara, dan Allah ba ya kunyatar ko tab'ar da wanda ya kiyaye hakk'ok'in wannan mutanen a duniya. Khadija ma a gidan su farin ciki ta ke kamar ba ta farin ciki a gidan ta, hakan kuma ya samo asali ne sakamakon samun kan ta da ta yi a tsakiyar mahaifiyar ta da kuma d'an ta, sai sauran matan yayyun ta da kuma 'ya'yan su, bayan sun ci abincin rana yan uwan ta maza su uku su ka shigo gidan, anan ta tara su kuma ta fad'a mu su auren da mijin ta zaiyi, ta gaggauta fad'a mu su hakane saboda ta san sune za su iya bata shawara mai kyau wacce ta dace, kuma kamar yanda ta yi tsammani hakane ya faru, sosai su ka kwantar mata da hankali tare ja mata kunne da nasihohi ma su shiga rai, tare da kafa mata misali da matar babban yayan ta wanda da zai k'ara aure ta tashi hankalin kowa, a k'arshe dai sai da ta bar gidan, yanzu gashi nan sai amaryar ke rayuwar ta a b'angaren na su, abin da ba ta son ganin shi ke faruwa a bayan idon ta kuma ba yanda za ta yi, ga yayan ta ma su na hannun uban su sai yaga dama ya ke barin su su je wajen uwar, saboda hure mu su kunne da ta ke, hakan ya k'ara saka jikin Khadija yin sanyi, kuma ta yi niyyar yin aiki da shawarwarin da su ka bata, a haka ita ma ta yi yammacin ta tare da maman ta abar k'aunar ta, zuwa *5:30* na yamma kuma Bilal ya d'auki kayan shi su ka wuce tare da maman shi a motar ta. Su na isa gida Bilal ya wuce da yan kayan shi d'akin shi tare da canza na jikin shi, ita ma kaya ta sauya ta wuce madafa dan sarrafa abin da za su ci da dare, tare da Bilal su ka shiga ya na kama mata duk aikin da ta ke yi, sai da aka gama sallah magrib ta gama lokacin Bilal ya wuce masallacin da ke had'e da gidan su, ta na gama ajewa a mazaunin cin abinci ta yi wanka ta shirya cikin riga da zane wanda su ka d'auke jikin ta sosai, kasancewar babu wata tazara mai tsayi tsakanin sallah magrib da isha'i ya sa ta yi sallahn ta, ta na kammalawa ta fito falon ya yi daidai da shigowar Bilal daga masallaci tare da baban shi. Ta na ganin shi ta tashi tsaye ta turo baki tace "Sai yanzu za ka dawo min gida? Ina ka shige haka?" Kallon Bilal ya yi yace "Yau salon gaisuwar maman ka kenan? To ka fad'a mata ba zan amsa ba." Ita ma Bilal ta kalla tace "To ka fad'awa Abban ka ya juya ya koma in da ya fito, dan ba ya da muhalli a gidan nan yau." Dariya ya yi ya kalli Bilal yace "Ka tambayar min ita kaji, wai dama ana korar mutum da gidan sa?" Da shu'umin murmushi a fuskar ta tace "Ka fad'a ma sa sau nawa aka yi, idan kuma bai tab'a gani ba to yau zai faru a kan shi." Bilal da ya saki baki ya na kallon su dukan su ne ya matso kusan maman shi ya rik'e hannun ta yace "Momy dan Allah ni dai muje ki zuba min abinci na ci yunwa na ke ji." Dafa kanshi ta yi tace "Muje ka ji yaro na, kai da gidan ku." Sun juya za su wuce ta ji ya rik'o hannun ta, juyowa ta yi su ka kalli juna, murmushi ta masa tace "Ina so na rumgume ka, zuciya ta bugawa ta ke da k'arfi." Jan hannun ta ya yi su ka nufi d'akin shi, Bilal na ganin haka ya k'arasa shi kad'ai ya zuba abincin ya fara ci, dan ba zai iya jiran su ba, su na shiga d'aki su ka k'wak'wume juna kamar sun shekara ba su had'u ba, sumbatar ta ya ke tare da fad'in "Na yi kewar ki sosai, wuni d'aya ba mu had'u ba alhalin ina cikin garin nan, gaskiya ba zan k'ara nesanta kai na da ke ba." Da k'yar dai su ka rabu ta taimaka mi shi ta cire ma sa kayan ta mi shi wanka kafin su ka fito, zaune ya yi ta zuba mu su abinci a faranti d'aya, amma saboda sabo har Bilal sai da ya sa hannu a na su abincin ya sake ci, cikin farin ciki da k'aunar juna su ka kammala, Bilal ya wuce d'akin shi ya na kallo, su kuma su na nan falo. *Wannan ita ce rayuwar farin cikin da su ke ciki.*

Table of Contents

Chapters

117 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117