Chapter 53
Chapter 53
da ya yi yace "Malama ya dai? Har yanzu ba ki kwanta ba kamar ki na jiran mu." Ganin Haseenah ta nufi b'angaren ta ko a kwalar rigar ta ya sa shima ya bi bayan ta, ita ma wucewa ta yi ta je falon shi ta zauna kan d'aya daga cikin kujerun teburi ta na jiran shi, ai kam bai jima sosai ba ya shigo falon da alama wanka zai yi, kamar bai ganta ba haka ya wuce uwar d'akin shi ya fara cire kaya, ita ma bayan shi ta bi hannu ta kai da nufin kama mi shi ya yi saurin ja baya sosai yace "Nagode." Ko wando bai cire ba ya wuce ban d'akin, ta na nan zaune har ya fito ya shirya duk ta na kallon shi ta rasa ma abinyi, juyowa ya yi zai fita yace "Idan kin gama kallon nawa na fita ni, zanyi kallo daga yanzu zuwa lokacin da zan kwanta ba na son takura." Da sauri har da gudu ta k'arasa gaban shi ta rik'o hannun shi, za ta yi magana sai kuma ta kasa saboda yanda ya raba hannun ta da na shi, shi kam ta na rik'e hannun shi ya ji kamar ta zuba mi shi ruwan zafi a jiki, ba ta yi magana ba ya fice ya bar ta, falon ta biyo shi cikin rawar murya tace "A...a..abincin..ka..." Da k'arfi ya mik'e daga zaman da ya yi kamar zai had'e ta cikin d'aga murya iya k'arfin shi yace "Ba na ci, nagode, dallah ki fitar min daga d'aki, zuciya ta tafasa take idan ina kallon ki, sam muryar ki babu dad'in ji kuma duk kin bi kin takura ni da zance kamar wata sabuwar rediyo (redio)." Wani dogon tsaki ya ja yace "Haba, ni na rasa gane wannan jarabar." Kai tsaye d'akin Haseenah ya nufa ya na ci gaba da mita, ragwaf Khadija ta fad'a kan kujera ta fashe da kuka, har za ta d'aga sauti sai kuma ta kame bakin ta ta tashi ta koma na ta d'akin, har ta dasa wani sabon kukan sai kuma ta tuna maganar lahaifiyar ta da take fad'a mu su "Duk abin da ya yi zafi laganin shi Allah, ku rik'e Allah a cikin lamarin ku, ba shakka zai taimake ku dan ya na tare da ku." Wannan maganar ce ta sa ta d'auro alwala ta shinfid'a sallaya ta d'auki Qur'ani ta fara karatu, saida ta raba dare kafin ta kabbara sallah a kowace sujuda ta na kaiwa ubangiji koken ta. Usman kuma na shiga ko da ya sauke idon shi akan amaryar shi sai wani irin farin ciki da shauk'i ya rufe shi, sam ya manta da komai a kan shi haka ya so hayake ma haseenah, ita kam sam tsoro ya kamata dan haka ta k'i amince mi shi, da k'yar da sud'in goshi ta lallab'a shi ya koma d'akin shi, amma a ganin shi da ya ga Khadija gwara ya zauna shi kad'ai, haka ya sha baccin shi har kiran sallah asuba. *Allah ka azurta mu da abokan zama na gari* 08/02/2020 Γ 23:04 - πππ: ππππππππππ *KALLON KITSE* _(Ake wa rogo)_ ππππππππππ _SAMIRA HAROUNA_ *Litattafan marubuciyar* *1* _KAUSSAR_ *2* _D'AUKAR FANSA_ *3* _BA SO BANE_ *4* _AUREN HAD'I_ *5* _SANIN MASOYI_ *6* _JIHADI_ *7* _K'ANGIN RAYUWA_ *8* _ITACE K'ADDARARMU_ *9* _KAWU NA NE_ *10* _MAATA_ *11* _KALLON KITSE..._ *SADAUKARWA GA* _MATAN FARKO_ π§πΌ *(UWAYEN GIDA)* πΈπ¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S* _(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_π€π€ ```Fatan alkairi masoya``` 1. Mom teema Hakima 2. Yar baba ( Fatima Zara ) 3. Momyn Dady 4. Chappa *Auntyn Khadi* 5. BILKISU Z. YA'U 6. Raheenah m Abbacar 7. Aishan Umma 8. Maman Labyb 9. Aunty Hawwer 10. Hawwer Jidda 11. Alawiyya 12. Amina 13. Yagana Mousa 14.Rukayya 15. Maman souhailat 16. Ummu sultan 17. Ouma saadou 18. Rahilat 19. Azima *momyn Imane* 20. Mme Jamil 21. Ummi 1 22. Ummi 2 23. Nazeefa 24. Jamila 25. Maijiddah 26. Sadia magaji 27. Phartee shehu 28. Ummu halima 29. Halima Muhammad 30. Maman Tasleem 31. Jawahir Gombe 32. Fareedah Boube 33. Lubabatu Shehu shayi 34. Zeinab mai kano 35. Maman Ahmad 36. Firdaussi Shehu 37. Binta Umar 38. Preettyy Aeeshartyy 39. Rukayya Usman 40. Maryam Abdul Mumin 41. Salma Ibrahim 42. Hussy luv 43. Hafsat A.A 44. Jamila Musa 45. Choukriyya 46. Khadija Isa 47. Matar manya 48. Mamar Soja 49. Momyn Rasil 50. Meeynert 51. Mandiyaπ 52. Habiba Bala _Duk wanda ya ga sunan shi to ya na zuciyar *Samira* ne, sai dai wanda na manta kawai a matsayi na na yar adam ajiza._ _Bismillahir rahamanir rahim_ *21* Abincin jiya ta fara d'aukewa kafin ta d'ora na karin kummalo, ba ta wani d'auki lokaci ba ta k'arasa shirya komai, saida ta shirya ta tashi Bilal shima ta taimaka ma sa ya shirya da sauri, karin kuma ta had'a mi shi ya ci ya k'oshi kafin ya nufi d'akin mahaifin shi, abun mamaki shine a al'adar Usman ba ya komawa bacci bayan sallah asuba, amma sai gashi yanzu rauni da sauyin da aka samu ya sa kasala ta rufe shi ya gagara abin da ya dace, haka ya koma ya kwanta baccin shi, doguwar riga kawai ya zura suka tafi ya kai shi, ko da ya dawo ya samu Khadija zaune a falon shi, da sauri ta mik'e ta kalle shi tace "Ina kwana." "Lafiya." Ya fad'a ya na shirin wucewa, da ido ta bishi har ya wuce d'akin amarsu, tashin ta ya yi a bacci suka shiga wanka tare su ka fito, sun jima kafin su gama shiryawa su fito tare, Khadija na zaune in da ya barta tun farko, zaune su ka yi akan kujera ita kam sai ta kafe shi da ido da tsananin mamaki, jinkirin ne ya sa yasa Usman kallon ta ganin ba ta da niyyar zuba abincin ya sa yace "Abincin na ki ko na siyarwa ne? Sai ki mana baya ni ai." Murmushi ta masa ta mik'e ta fara zubawa, shi ta fara zuba ma ta aje a gaban shi sannan ta zubawa Haseenah da ke ta kakkaryewa ta aje mata, ta na shirin zuba ma kan ta Haseenah ta ture faranti gefe ta mik'e tsaye ta kalle shi tace "Baby, zan koma d'aki na na kwanta, ba na jin sha'awar cin abincin nan kwata-kwata." Kamar mazari haka ya fara tambayar ta "To me za ki ci idan ba ki ci abinci ba? Fad'a min me ki ke so ki ci to? Ai ba kya zauna da yunwa ba ki cutar da kan ki." Cike da yatsina fuska tace "Umm, da ace zan samu indomie da na ji dad'i." Kallon Khadija ya yi ya kula kallon ta yace "Abu mai sauk'i, bara yanzu a dafa mi ki, kije ki kwanta to." Kallon Khadija ya yi da ke tsaye yace "Am dan Allah na ce ba, ki taimaka mata ki d'ora mata, ina ganin kamar ba ta da lafiya ne fa, dan gaba d'aya yanayin ta ya canza." Kallon shi Khadija ta yi ta na wani shegen murmushi mai kama da na mugunta tace "Ka yi hak'uri Abban Bilal, ban raina ka ba, kuma ka isa ka sani komai na yi maka, amma banda hidimar matar ka,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117