Chapter 47
Chapter 47
kujerar ta koma wajen wasu tsofi ta zauna, su kam tabbas jikin su ya yi sanyi, sai dai a ganin su duk cikin sharrin Khadija ne, Husseina ce tace "Gaskiyar Hajia, wallahi duk ranar da yah Fodio ya ji maganar nan a bakin mu, to fa kashin mu ya bushe." Aziza ce tace "To ai dole tunda ta gama da shi, in ba kinibibi ba miye ta ke bashi kowane dare ya na sha da sunan shayi? Har da wasu k'ulallen abubuwa kamar kashin shanu kuma bai kai kashin shanu ba na ga ta na sakawa." "Da gaske ki ke Aziza?" Cewar Rabi'a da duk cikin su tafi tsanar Khadija tun lokacin da ta nemi kud'i wajen d'an uwan ta, ta rik'e abun sosai a zuciyar ta ya na d'awainiya da ita har yanzu, Aziza ce tace "Wallahi kuwa, a madafa ta ke aje abun, kuma ko a gaba na sakawa ta ke." Cike da makirci Rabi'a tace "Hakan ma wata hujja ce da za ta tona ta, Aziza ya za ayi ki d'auko mana wannan abun?" Cike da rashin tsoro tace "Abu mai sauk'i, in dai har yanzu ta na aje shi in da ya ke ai zan gan shi." Hassenah na shiga ta samu Khadija tsakiyar gado da manyan mata sai hira suke ana dariya, cike da fargaba ta yi abin da ya kai ta ta juyo ta fito, wajen su Hassana ta koma su ka ci gaba da hirar su, Khadija kuma na ganin fitar ta ta kalli k'awar ta Hajia Turai Dubaï tace "To kinga amaryar ta wa da har yanzu ki ka kasa zuwa ki gani." Waro ido Turai ta yi tace "Ita ce kishiyar ki?" "Eh." Ta fad'a har da dariya, hararan ta ta yi tace "K'arya ki ke wallahi, wannan ce za ta zama amaryar ki? Haba Khadija, ko da dai nasan halin mutanen mu ba kunya ne da su ba, amma taya Usman zai had'a ki da yarinyar can?" *Umma* Khadija ta kalla tace "Ke da ki ka tabbatar sai ki fad'a mata gaskiya." Umma ce ta d'ora "Wallahi ita ce kishiyar ta." "Bala'i." Cewar Hajia Turai cikin d'aga murya bugu da k'ari Allah ya hore muryar sosai, kasancewar irin mutanen nan ne masu ido bud'e da basu tsoron tashin hankali ko hargowa ya sa ta shiga aibata Haseenah ta na shammace ta, tun Khadija na cewa ta yi shiru dan Allah har ta yi banza da ita, hakan kuma da akayi duk a ido da kuma kunnen 'yar k'anwar mahaifiyar Usman (cousine d'in shi), ba ta b'ata lokaci ba wajen fitowa ta fad'awa Hassana da dama akan maganar Khadija suke, amma sai da ta keb'e ta gefe d'aya, Hassana ba ta tanka ba har lokacin da Mariya ta kira Haseenah wai idan ta na gida za ta zo ta kawo mata sak'on wajen malam, nan Haseenah ta fad'a mata ba ta gida amma za ta zo yanzu ita ta karb'a, sallama ta mu su tace ta tafi gida ba ta jin dad'i, ta na samun adaidaita ta wuce gidan Mariya, magani ta bata kala har uku wanda in dai ta yi aiki da su to ta tabbatar mata Usman zai zama na ta, d'aya za ta shafa a marar ta ne ranar kwanan ta ya sadu da ita, d'aya za ta saka a abin sha da ya danganci koko, fura ko kunu, sai kuma d'aya da za ta zuba a k'ofar d'akin Usman ya tsallaka, cike da farin ciki da jin ta yi nasara ta baro gidan ta nufi gida. Fitar ta ba jimawa Khadija ita ma ta wuce gida dan kama aiki, nan fa su Hassana suka shirya abin da za su fad'awa Usman tare da shirya yanda za su yi. Bayan sallah isha'i Usman na zauna a majalisar su ana hirar duniya kiran Hassana ya shigo wayar shi, sun tsara ita ta kira shi ne saboda ita ce babba da ke bi mi shi, ya na d'auka ta gaishe shi cikin ladabi ya amsa, cikin taushin murya ta d'ora da "Yah Fodio dama ina son yin magana da kai ne, sai dai bansan ta yanda za ka fahimce ni ba." Kamar ya na gaban ta ya yi murmushi yace "Ki tak'aita mana wahala to, ki fad'a a yanda zan fahimta." Gaban ta ne ya sake fad'uwa kafin ta dake tace "Yah Fodio dama abin da ya faru d'azu wajen biki ne gaskiya bai ma kowa dad'i ba, Khadija dai ita ce babba kuma za ta iya rik'e ragamar gidan ka ko ba ka nan, amma abin da su ka yi d'azu da k'awayen ta gaskiya bai dace ba, dan wannan salesalen tayar da masifa ne, wallahi saida mu ka iza k'eyar Haseenah ta koma gida saboda ran ta ya sosu." Kasanvewar ya na cikin mutane ya sa matsa gefe da su yace "Me ya faru? Me Khadija ta yi ita da k'awayen ta? Hassana ba na son masifa da tashin hankali ke kin sanni." Cike da tabbatarwa tace "Wallahi gaskiya na ke fad'a ma ka, a d'akin *Zaliha* fa su ka zauna suna ta shammatar Haseenah su na zagin ta ta uwa ta uba, idan kuma ba ka yarda ba ka tambayi *Nana* (cousine d'in su) za ta fad'a ma ka gaskiya, musamman ma wannan k'awar ta ta mai ido tsaye Hajia Turai." Ba wai rantsuwar da ta yi ba ce ya sa ya yarda sai anbaton sunan Hajia Turai da ta yi, matar ba ta da wata d'abi'a da zai ce ba ya son mu'amular ta da matar shi, sai dai irin matan nan ne da masu da kimtsi, komai ya zo bakin ta fad'a ta ke sannan ba ta tsoron bala'i da mace kl namiji, hakan ya sa ma har yanzu ta ke zawarci babu mijin aure sai duniyar ta da ta ke ci da tsinke, nisa da tunanin da ya yi ne ya sa ya kashe wayar bai ma san ya kashe ba, zunbur ya mik'e ya fad'a motar shi ya nufi gida. Tsaf Khadija ta gama shirya komai ta aje a muhallin shi ta shiga wanka, jin babu motsin ta ne ya sa Haseenah tabbatarwa yanzu ta na wajen shiri, ta falon ta ta shigo na shi falon cikin sand'a da rashin gaskiya, kai tsaye k'ofar uwar d'akin shi ta nufa da k'ullin maganin ta, ta na zuwa ta bud'e ledar tasa yatsu biyu kamar yanda aka fad'a mata, barbad'awa ta yi tare da kiran sunan Usman, sau uku ta zuba kuma a kowane zubawa sai ta kira sunan shi, da sauri ta rufe ledar ta koma falon ta da sauri cikin tsoro, ajiyar zuciya mai nauyi ta sauke kafin ta dafe k'irji ta yi murmushi, Usman da ke hanyar shi ta zuwa gida ne ya ji wani bala'in sarawar kai kamar an buga mi shi guduma, da k'arfi ya take motar ya tsaya ya dafe kan shi, ya jima a haka sai da ya ji motoci na mi shi odar ya ba su hanya kad'ai ya dawo hayyacin shi ya taka, Khadija na d'aki ta gama duk wani shirin ta ta mik'e ta na d'aura d'an kwali ta ji an bud'e k'ofa da k'arfi, juyowa ta yi dan ganin waye wannan, ganin Usman a
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117