Skip to content

Chapter 15

Chapter 15

Kallon Kitse Book One Complete Hausa Novels 1,199 words 0 views Progress saved
Download Book

so, kar kuma ka kuskura na gan ka ko a bakin titi ne, dan ran ka zai b'ace." Mik'ewa Bilal ya yi ya matsa kusan shi yace "Ka yi hak'uri Abba, ba zan sake ba." Kan shi kawai ya shafa bai ce komai ba, jakar shi ya d'auka mai d'auke da littafanshi yace "Na gama." Kallon shi ya yi yace "Ka tabbata ka k'oshi?" Kai kawai ya d'agaalamar Eh, hannun shi ya kama yace "To muje." Juyowa ya yi ya d'agawa mahaifiyar shi hannu yace "Sai na dawo sarauniya." Murmushi ta masa tace "Allah ya tsare, a kula sosai ka ji ko?" Usman ma kallon ta ya yi yace "Ni ma na tafi ba zan dawo ba." Ba alamar wasa a tare da ita tace "Sai na bika duk in da ka ke ai." Dariya ya yi yace "Kar ki damu sarauniya zan dawo ai, ke ce fa." "Ah to, sai na ma riske ka duk in da kaje." Ta fad'a ta na tashi dan had'a kayan da su ka karya. *Kafin mu ci gaba, za mu waiwaiya baya mu ji yanda wannan soyayyar ta fara ta Khadija da Usman.* _Sai mun had'u a shafi na gaba._βœ‹ 10/01/2020 Γ  12:20 - πŸ’‹πŸ˜˜πŸ’‹: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘ *KALLON KITSE* _(Ake wa rogo)_ πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘ _SAMIRA HAROUNA_ *Littatafan marubuciyar* *1* _KAUSSAR_ *2* _D'AUKAR FANSA_ *3* _BA SO BANE_ *4* _AUREN HAD'I_ *5* _SANIN MASOYI_ *6* _JIHADI_ *7* _K'ANGIN RAYUWA_ *8* _ITACE K'ADDARARMU_ *9* _KAWU NA NE_ *10* _MAATA_ *11* _KALLON KITSE..._ *SADAUKARWA GA* _MATAN FARKO_πŸ§•πŸΌ *(UWAYEN GIDA)* πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S* _(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€› ```Fatan alkairi masoya``` _Bismillahir rahamanir rahim_ *9* *Alhaji Ahmad*, dattijo mai dattako, mutum ne da Allah ya wadace shi da komai, dukiya, ilimi da 'ya'ya, matar shi d'aya *Hajia Sadiya*, suna zaune lafiya cikin farin ciki, mutum ne shi da bai da ra'ayin tara mata, hakan ya sa suke zaune daga Sadiya sai yayan ta, Allah ya azurta su da yaya maza guda biyar, *Ashir* shine babba, sai *Bashir* sai kuma *Habib* da *Mansur* da *Naseer*, Naseer na da shekara biyar aka samu cikin da ya wahalar da Sadiya, tun a lokacin su ke ji a jikin su cewa Allah zai musu sauyi ne, cikin ikon Allah kam bayan laulayin da ta sha sai gashi ta haifo kyakyawar yarinya mai kama da ita, *Nana Khadija*, yarinya ce da ta zama tamkar wata zinariya a cikin mutane, kowa soyayya ya ke nuna mata, lele kawai da gata take gani, su kan su yan uwanta suna matuk'ar k'aunar ta, dan har fad'a suke akan wanda ya fi sonta ko wanda zai d'auke ta, haka Khadija ta taso cikin gata da kulawar iyaye da yan uwa, sai dai tun da ta fara tafiya suka lura kamar tana da matsalar ido, basu b'ata lokaci ba wajen ziyartar likitoci, nan aka sanar da su tana da matsalar gani, bata iya gani da kyau sai dishi-dishi, sosai mahaifinta ya damu kuma yake yawon nema mata magani, amma sam ba'a dace ba har k'asar waje an fita da ita, haka dai suka hak'ura aka d'ora ta akan saka gilashi mai k'ara gani, wannan laurar sai tasa iyayenta da yan uwanta sake tausaya mata da k'ara k'aunar ta, sam larurarta bata tab'a damunta ba bare tasa damuwa, tana jin dad'in kasancewarta a yanda take, duba da wasu sam idon ne ma basa da su, tana da shekara *goma sha biyu* a duniya ranar wata alhamis da dare, suna zaune a farfajiyar gida su na ta hira Khadija na kan k'afafun mahaifin ta, da sauri ta juya ta kalli baban ta tace "Baba, ka ga wani ya shiga d'akin ka." Da mamaki ya juya ya kalli k'ofar d'akin na shi ya gan shi rufe, murmushi ya yi ya kalle ta yace "Auta ni banga kowa ba, gashi ki na gani ma d'akin a rufe ya ke." Naseer ne yace "Wallahi nima Baba sai na ga kamar giftawar mutum." Sake juyawa ya yi ya kalli k'ofar yace "To wa zai shigo cikin gidan bayan ga k'ofar nan a gaban mu kuma ace ba mu ga shigowar shi ba." Almajirinsu da ke zaune nesa da su ne ya na cin abinci ne yace "Baban Khadija wallahi nima na gan shi, wani dogo da fararen kaya, amma banga fuskar shi ba, kuma na so inyi magana saina kasa na ji tsoro." _Wallahi wannan wani abun al'ajabi ne da ya faru da wata baiwar Allah da na sani, za mu iya cewa mala'ikan mutuwa ne_ Sadiya ce tace "Kai Ashir tashi ka duba mana." Kallonta ya yi yace "Mama, ni kad'ai? Kawai ki bar shi idan ya ga ji zai fito ai mu gan shi." Dariya aka saka sai Baba ne yace "Ki bar shi kawai, watak'ila fa gizo idon su ke musu, na ga ai ga k'ofar shigowa nan, babu wanda mu ka ga ya shigo." Haka aka share wannan magana aka ci gaba da hira, Khadija ce bacci ya dauke ta a k'afafun shi, a hankali ya d'auke ta ya kai ta makwancin ta ya shafeta da addu'a, fitowa ya yi su Ashir ma har sun tashi, dawo da su ya yi suka zauna, ya jima ya na musu nasiha da su rik'e Khadija da kyau su zama gatanta ita kad'ai ce k'anwar su mace, har sha biyu na dare ta wuce kad'ai suka tashi, d'akin shi ya shiga ya yi shirin kwanciyar shi sannan ya d'auro alwala, raka'a biyu ya samu damar yi wani nauyayyen bacci ya sure shi akan sallayar, daga wannan bacci ne Allah ya karb'i abin shi. Mutuwar nan ta girgiza mutane sosai, musamman Sadiya da ke kwance asibiti ba ta san me ake yi ba, Khadija ma yan uwan ta kad'ai take iya yarda da su, amma haka ko da lokaci ya tafi kowa ya manta, sai dai ciwon na nan a zuk'ata, dukansu mazan babu wanda bai da aikinyi mai kyau, hakan ya sa suke matuk'ar kula da k'anwar su, sosai suke shagwab'a ta, ga yarinya na girma amma gatan da take samu yasa kullum kamar yarinya. Tun Khadija na da shekara sha biyar Ashir ya gwangwaje ta da moto, duk da sauran yan uwan kowa ya so ace shi ya siya mata, amma haka suka hak'ura tun da ya fisu zafin nama, wannan lokacin ne aka musu rabon gado, kowa ya tashi da na shi kason mai tsoka, na Khadija kuma tace a bawa Ashir da Mansur su ci gaba da juyawa dan sune suka fi sha'awar kasuwanci, mamansu ma dama ta na nata kasuwanci, dan haka ta ci gaba daga inda ta tsaya. *Duk* wata ba'a daina abin da Alhaji Ahmad ya fara ba, ana yanka rago ayi sadaka, sannan akanyi waina ayi miya sai su aika inda mahaifinsu ke zama da yamma wajen abokanan shi, haka rayuwar ke tafiya har lokacin da Khadija ta ci jarabawarta kuma sakamako mai kyau, babbar walima yayyun ta suka shirya mata a bazata, kayan da suka shirya mata suka sata ta saka suka tafi da ita babban wajen cin abinci, k'awayenta da maza da dama ta samu wanda su ka yi karatu tare, ta ji dad'i sosai a ranar, anan ta yanka (πŸ˜‚bansan me zan kira cake da hausa ba, amma bara nace mu

Table of Contents

Chapters

117 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117