Skip to content

Chapter 46

Chapter 46

Kallon Kitse Book One Complete Hausa Novels 1,198 words 0 views Progress saved
Download Book

fita daga gidan ba?" Cikin turo baki tace "Na shirya fa na ke ta jira aunty Khadija ta min magana, tunda ai ba zuwa zanyi ba na tisa ta a gaba har sai ta gama shirin ta, ina falo kawai sai fitar ta na ji." Ba dan ya yarda da abin da ta fad'a ba yace ta jira shi ya zo ya d'auke ta, dan in dai Khadija za ta fita to bata kaiwa warhaka bata fita ba saboda taje ta dawo da wuri ta kama aikin gaban ta, hanya ya d'auko dan ya zo ya d'aukar ta ya kira Khadija a waya, bayan ta d'auka ne yace "K'anwar ki ta kira ni tace wai kin tafi kin barta, shine na ce ya akayi haka ta faru?" Khadija da ke tuk'i ne tace "Ba ta fad'a ma ka na kai mak'ura bane wajen jiran ta? Ko kuma kawai ta fad'a ma ka abin da ta ga dama ne?" Murmushi ya yi daga in da ya ke yace "Ran gimbiya ya huce, kawai dai ina tambaya ne." Cike da rashin kulawa tace "Ka ga ina tuk'i fa, sai munyi magana." Kasje wayar ta yi ta ci gaba da abin da take, shima kuma d'auko Haseenah ya yi sai dai bai fad'a mata yanda su ka yi da Khadija ba har suka isa ya sauke ta, da d'ar-d'ar ta shiga gidan bikin ta na sallama wata bayan wata, cikin sa'a ta hango su Hassana da Husseina da duk sauran yan uwan tare da Hajia sarakuwar su zaune, da azama ta isa can ta zauna su ka gaisa, Rabi'a ce ta fara tambayar ta da "... *Ku yi hak'uri masoya abisa jinkiri na, hakan na faruwa ne sakamakon al'amura da su ke sha min kai na.*πŸ‘ 04/02/2020 Γ  21:00 - πŸ’‹πŸ˜˜πŸ’‹: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘ *KALLON KITSE* _(Ake wa rogo)_ πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘ _SAMIRA HAROUNA_ *Littatafan marubuciyar* *1* _KAUSSAR_ *2* _D'AUKAR FANSA_ *3* _BA SO BANE_ *4* _AUREN HAD'I_ *5* _SANIN MASOYI_ *6* _JIHADI_ *7* _K'ANGIN RAYUWA_ *8* _ITACE K'ADDARARMU_ *9* _KAWU NA NE_ *10* _MAATA_ *11* _KALLON KITSE..._ *SADAUKARWA GA* _MATAN FARKO_πŸ§•πŸΌ *(UWAYEN GIDA)* πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S* _(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€› ```Fatan alkairi masoya``` *πŸ‡ΈπŸ‡¦ZAMAN AMANA WRITER'S* (GIDAN ZAMAN LAFIYA DA AMANA INSHA ALLAH)πŸ€œπŸ€› *SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!* *INA JIGA JIGAN MASOYAN πŸ‡ΈπŸ‡¦ZAMAN AMANA WRITER'S WAD'ANDA BASU DA TAMKA A WAJENMU????? DUK WANDA YAKE TARE DAMU A CIKIN GROUPS D'INMU TO MUN TABBATAR K'AUNARMU CE TASA KUKA KASANCE TARE DAMU, MUNA YABAWA KUMA HAR ABADA BAMU DA KAMARKU WALLAHI,πŸ‘ DUK DA HAKA DAI GA LOKACI YAZO, KUMA DAMA TA SAMU NA TABBATAR MANA DA KUMA NUNA MANA HAK'IK'ANIN K'AUNAR DA KUKE MANA,πŸ‘‡* Kunsan cewa k'ungiyarmu *πŸ‡ΈπŸ‡¦ZAMAN AMANA WRITER'S* suna cikin gagarumin gasa na samun award Wanda *women24 TV WhatsApp group* suka shirya kuma zasu gudanar? A wannan gasar ne za'a samu k'ungiyar da tafi kowacce k'ungiya yawan fans da Kuma bin k'a'idar rubutu Dan ki samu damar zabar k'ungiyarmu *πŸ‡ΈπŸ‡¦ZAMAN AMANA WRITER'S ASSOCIATION* zaki iya tuntub'ar wannan lambar 09030159301 Dan su saki a *WOMEN24 TV WHATSAPP GROUP* anan ne za'ayi zab'en k'ungiyar da tafi kowacce k'ungiya yawan masoya *Women24 Tv* Ba zabe kad'ai zakiyi ba Zaki k'aru da abubuwa da yawa kamar haka *Yanda ake girke girke* *yanda zaki gyara jikinki* *yanda zakiyi makeup* *yanda zaki daura Dan kwali* Kuma suna shirye shiryen nan na *arewa24 tv* kamar su *TARKON KAUNA* *DADIN KOWA* *KWANA CHASA'IN* *JAMAI RAJA* *SAPNE SUHANE* *GIDAN BADAMASI* *RUDIN ZUCIYA* *BAGHYA LAKSHMI* *AKUSHI DA RUFI* *AUDIO NOVEL* *HAUSA NOVELS* Kada ki manta da ranar zabe inkin shiga group d'in ki zaba *πŸ‡ΈπŸ‡¦ZAMAN AMANA WRITER'S* tanan ne zaki iya nuna mana irin sonda kuke ma k'ungiyarmu da littattafammu Allah yabar zumunci🀝😍πŸ₯°πŸ’‹ _Bismillahir rahamanir rahim_ *19* "Haseenah ke kad'ai ki ka taho ne?" Da kunya ta kalle ta tace "A'a, shi ya kawo ni ai, da tare da aunty Khadija zamu taho, to kuma bansan tafiyar ta ba." Ai kuwa abin da ta fad'a ya samu shiga sosai, hakan ya sa Hassana cewa "Amma yasan za ku taho tare?" "Eh ya sani, shi yace ma mu taho tare tunda safe." Rabi'a ce tace "Amma kuma dan rashin mutumci shine ta taho ta baro ki? Lallai ma matar nan, kullum iskancin ta k'aruwa ya ke." Husseina ce tace "To ba ita ke da mota ba, kinga kuwa dole ta yi yanda ta so." "Hum." Cewar Hassana, cike da wauta Aziza tace "Wallahi kema kar ki yarda ya siya mi ki ko moto ne, dan ba za ki zauna ta na mulkar ki ba." Hajia ce ta kalli Haseenah tace "Ki shiga wajen mai jegon mana ku gaisa." "To Mama." Ta fad'a ta na mik'ewa, cike da dattako Hajia ta sake cewa "In ce dai ya baki abin da za ki kaiwa mai jegon?" 'Yar dariya ta yi tace "Eh Mama, tunda safe ma ba bamu dukan mu." Hajia na ganin wucewar ta ta kalle su dukan su tace "Yanzu mi ye anfanin haka? Wannan yarinyar yaushe ta shigo cikin ahalin ku da har ku ka yarda da ita haka? Mi ye Khadija ba ta mu ku ba a rayuwa da har ku ka butulce ma ta haka? Dukan ku fa mata ne, kuma Rabi'a ce kad'ai ba ta da abokiyar zama a ciki, ke kan ki Aziza da ki ke wata banzar magana na ga saurayin da ki ke so ai mata gare shi, shin idan aka mu ku haka za ku ji dad'i? Nace za ku ji dad'i idan aka mu ku haka? Ba za ku ji ba kenan? Shine kuma ku ke wa wata rashin kunya wacce ta mu ku alkairin da ki shi d'an uwan na ku bai mu ku kamar shi ba, shi d'an uwan na ku kunsan yanda ya ke d'aukar ta da kuma matsayin ta a wajen shi? Ku kan ku da akwai mutumci ai Khadija tafi k'arfin komai a wurin ku, wallahi ta wuce cin mutumci da cin zarafi, ko ba komai mafi soyuwar abu a zuciyar d'an uwan ku shine d'an wannan matar da ku ka raina, sannan ina yak'ini akai ko tamtama babu cewar Khadija ma tafi soyuwa a zuciyar d'an uwan ku, idan kuma kun shirya rasa shi ne to dan Allah ku ci gaba da mata rashin kunya, ni dai na fad'a mu ku gaskiya a matsayi na na uwa, kuma ke Aziza." Hajia ta fad'a ta na nuna Aziza da hannu kafin ta ci gaba da "Kar na sake jin bakin ki daga yau in har su na maganar su, tunda ke kinfi kowa butulcia cikin su, Aziza matar nan har kashi da fitsarin ki ta ci kamar yanda ni ma na ci, matar nan ta kwantar da ke a gaban k'irjin ta kamar 'yar da ta haifa, matar nan ta mi ki wanka da hannayen ta ta shirya ki, duk lokacin da mijin ta baya nan ke ce abokiyar rayuwar ta, har rayuwa ta canza mu su ta haifi nata yaron ba ta banbanta ki da shi ba, Aziza sai da aka kai k'adamin da ta ware mi ki d'aki a gidan ta, kinfi kowa sanin Khadija a cikin dangin mu, amma kash ke ce farko wajen juya mata baya, Allah ya kyauta." Ta na fad'a mik'ewa ta yi daga kan

Table of Contents

Chapters

117 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117