Chapter 80
Chapter 80
tunanin ta kenan ba zai zo ba ya na nufin na yi ta zama a gida. Gida Usman ya koma dan sanar da su ya tattauna da Nura kuma za su je neman masa aure, har d'aki ya samu iyayen na shi ya sanar da su yanda ake ciki, ya d'an jima suna tattaunawa akan lamarin kafin ya fara yunk'urin tafiya, "Karb'i nan." Cewar malam, kallon malam ya yi ya kalli kofin hannun shi, ruwa ne dai fari k'al da su, kallon malam ya yi yace "Baba wannan fa? Na miye?" "Karb'i kasha, na tsari ne." Ya fad'a ba alamar wasa, hannu ya sa ya karb'a ya yi bismillah ya kifa kai ya shanye, aje kofin ya yi ya musu sallama ya fita, bayan shi Hajia ta biyo saida ya zi gaf da d'akin ta tace "Bismillah nan." Saboda ba za ta kira sunan shi ba, bayan ta kawai ya bi suka shiga, ya na shiga ta mik'o mi shi roba da nono a ciki da abun magani tace "Shanye ka bani roban, kuma ka hi bismillah, sannan kasha zuciyar ka d'aya ba tare da tunanin cutar da wani ba ko wata." A raunane ya kalle ta yace "Hajia shi kuma wannan na miye?" Wani kallo ta watso masa amma ba tace komai ba, sanin ma'anar kallon ya sa ya kifa kai nan ma saida ya shanye kad'ai ya mik'a mata robar ya mata saida safe ya fito, haka ya d'auki hanya ya na tunanin abin da iyayen shi ke nufi da shi, da haka ya isa gida ya samu Haseenah yau dai ta yi girki kam, amma badan ranshi na so ba ya ci abin da ta dafa d'in har suka kwanta. Bayan tafiyar shine Hajia ta ji kamar ta yi kuskuren rashin sanar da shi wani abu, amma ta yi niyyar fad'a mi shi gobe da safe idan ya zo, sai dai kuma ta makara kam, dan Usman ya jima baiyi bacci ba ya na dafe da cikin shi, da Haseenah ta tambaye shi kuma bud'ar bakin shi cewa ya yi "... _Mu tara a shafi na gaba insha Allah._ *Ku yi hak'uri da ni mutane na abisa jinkira na, hakan na faruwa ne saboda sauyawar yanayi na.* ~*LUVE U ALL*~π₯°π 23/02/2020 Γ 13:03 - πππ: ππππππππππ *KALLON KITSE* _(Ake wa rogo)_ ππππππππππ _SAMIRA HAROUNA_ *Litattafan marubuciyar* *1* _KAUSSAR_ *2* _D'AUKAR FANSA_ *3* _BA SO BANE_ *4* _AUREN HAD'I_ *5* _SANIN MASOYI_ *6* _JIHADI_ *7* _K'ANGIN RAYUWA_ *8* _ITACE K'ADDARARMU_ *9* _KAWU NA NE_ *10* _MAATA_ *11* _KALLON KITSE..._ *SADAUKARWA GA* _MATAN FARKO_ π§πΌ *(UWAYEN GIDA)* πΈπ¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S* _(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_π€π€ ```Fatan alkairi masoya``` _*Lubabatu Shehu shayi*, ina ganin sak'onninki sosai, lallai ke masoyiya ce ta hak'ik'a, tun a gidan Raheenat muke tare, kuma gashi har yanzu kina tare dani a gida na na kallon kitse, Allah ya bar k'auna._ *KALLON KITSE FAN'S 1&2* π _Wannan sadaukarwar taku ce, kuyi yanda kuke so da ita._π _Bismillahir rahamanir rahim_ *30* "Wallahi kawai wani kindirmu ne Hajia ta bani nasha, gaba d'aya ya na neman lalata min ciki ma." K'aramin tsaki ya yi, ita kam da mamaki tace "Kindirmu kuma? Haka kawai?" Kamar wanda aka takura dole yace "Ina jin ko magani aka saka a ciki kome, ban dai sani ba ni dai kawai ya lalata min ciki sai tayar min da zuciya yake." Cike da kissa ta shafo shi tace "To in hakane kar ka sake sha mana, tunda ya na tayar maka da zuciya, zai iya saka ka amai ma fa." "Ina tunanin haka nima." Ya fad'a ido rufe, kallon shi ta yi tace "To wai ma maganin meye aka baka? Ba ka da lafiya ne dama ban sani ba." Bud'e ido ya yi ya kalle ta yace "Ke kar ki tsora ta, lafiya ta k'alau mana ke shaida ce, tace dai ko maganin tsarin jiki ne da kuma...mtss na manta dai, kawai share." Tashi tayi zaune ta na kallon shi idon shi rufe, tabbas in dai har hakane to iyayen shi sun fara hango wani abu kenan, d'aukar mataki shine abin da ya kamace ta kawai, dan haka tace "To beby in hakane me zai hana ka karb'o maganin, kaga sai ka rik'a sha anan zaifi da sai kaje can, koya ka gani." Cike da damuwa yace "Kar ki damu kan ki, ni fa ba wani shan shi zan dinga yi ba, ina addu'a na tsarin jiki hakan ma ya isa, kawai ki rabu da su, kinsan tsofaffin nan da tame-tame." Murmushi ta yi tace "Duk daha beby, idan ma ba za ka sha ba ai sai ka karb'o shi, dan in har ya na wajen su to ba fashi sai ka sha shi ko da za ka mutu ne." Shiru ya yi ya na tuna lokacin da ya tambayi Hajia amma ta yi banza da shi, hakan na nufin dole dai ya sha ba makawa, dan haka yace "Ba tabbacin za su k'ara bani, amma in har sun bani na sha to zan karb'o shi daga wajen su na taho da shi." "Gaskiya kam, da ba zan so wani abu ya samar min miji ba uban 'ya'ya." Ta fad'a ta na gyara kwanciyar ta, daga haka babu wanda ya sake magana har bacci ya d'auki dukan su. *Yau kam* Alhamdulillah Khadija ta tashi jiki da sauk'i sosai, da kan ta ta gyara d'akin ta da na Bilal da ma na Mama, zuwa k'arfe goma kuma ta fita madafar da matan gidan ke aiki, da kan ta ta fara girkin rana kafin matan yan uwan ta suka fito su ka kama aka k'arasa, *12:10* yaran su ka fara shigowa da sallama wasu kuma da gudu, kowa wajen tashi uwa ya nufa kafin suka wuce d'aki dan cire kaya, lokacin ne Khadija ita ma ta shiga d'aki dan ta yi wanka ta yi alwala, ta na d'aure da k'irji za ta shiga ban d'aki wayar ta tayi k'ara, dawowa ta yi dan d'auka amma har ta tsinke, d'aukar wayar ta yi ta duba mai kiran, sunan k'awar ta ne Kaltume, aje wayar ta yi da niyyar idan ta fito ta kammala za ta kira ta, har ta aje ta yi sauri ta sake d'auka saboda idon ta da ya sauka kan kwanan (date) wata, dubawa ta yi da kyau taga tabbas yau wata na da kwana *21*, kai da kawowa ta fara yi tsakiyar d'akin ta na tunanin yanda ta kasa ankara da lokacin al'adarta har wata ya ja haka, sai lokacin kuma ta iya tunawa fa tunda Usman ya yi aure ma bata sake ganin jinin ta ba, to me hakan ke nufi? Ta tambayi kan ta. "Kenan ciki gare ki kamar yanda Mama ta tambaya?" Da sauri ta zo gaban madubi ta janye d'aurin k'irjin ta tana shafa marar ta, tabbas sai lokacin kad'ai ta iya fahimtar tudun da mararta ta yi, a hankali ya fad'a kan gado ta yi zaune ta rufe ido, wasu hawayen farin ciki ne suka zubo mata ba tare da sanin ta ba, hannu ta sa ta share ta d'aga hannu sama ta furta "Alhamdulillah Allah, Allah kaine Allah, kuma kai ka ce mu rok'e ka za ka amsa mana, Allah nagode ma ka abisa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117