Chapter 63
Chapter 63
Bilal dan Allah duk in da ka ke ka zo gidan nan ka sake ni, wallahi na gaji da abin da ake min kullum ace na yi hak'uri, na gaji Abban Bilal." Usman da tuni ya zabura ya tashi tsaye cikin tashin hankali yace "Haseenah! lafiya? Me ya faru ki ke kuka?" "Ni dai kawai ka zo ka bani takardata, ba na so saina tafi gidan mu ka sake tafiya ka dawo da ni, Allah na gaji da zaman gidan ka." Usman kamar zai fashe da kuka sai kuwa cewa ya yi "Haba Haseenah, ya za ki fad'i haka? Kinsan ke ce rayuwa ta fa, idan ki kace na rabu da ke to ni ina zan saka kai na? Kinsan fa ke ce fitilar gidan nan, ke ce sukuni da walwala na gidan nan, ke ce farin ciki da kwanciyar hankali na, idan ki ka ce za ki bar gidan ya ki ke so na yi to? Dan Allah ki fad'a min miye ya faru ni kuma na mi ki alk'awarin d'aukar mataki da gaggawa." Tunda Murtala ya lura ya kuma ji abin da yake fad'a kan shi ya d'aure, shi dai a sanin shi har ya auri Haseenah ba wani zazzafan so yake mata ba, hasalima kullum cewa yake auren su Allah ne ya k'addara shi kawai, amma da zai iya hanawa da ya hana dan ya zauna da matar shi, ci gaba ya yi da kallon shi yayin da Haseenah tace "Haka kawai dan ka kori matar ka shine k'awar ta za ta zo har gidan nan ta ci mutumci na ta uwa ta uba, ba irin zagin da baiwar Allahr nan bata min ba, ta kira ni da matsiyaciya yar matsiyata, talaka yar talakawa, duk saboda ka kori matar ka, saboda Allah Abban ni ina da hannu cikin korar matar ka da ka yi? Ba kai ne ka yanke hukuncin ba? Amma shine za ta turo min 'yer iska gida har tana neman duka na, to ba zan iya ba wallahi, dan kalaman da ta fad'a ni sun tsorata ni sosai, dan ko ban bar gidanka ba yau to zan barshi gobe, tunda sun ci alhwashin ba za su barni ba nima na rayu da kai, kawai ni ka zo ka sake ni ko na samu naje gidan mu lafiya." Cikin wani irin yanayi yace "Wacece ita? Fad'a min sunan ta kawai." Kamar mai nazari tace "Wata wai ko Hajia Turai, har da cewa na tambaye ka wai kai za ka fad'a min wacece ita." Daga in da Usman ya ke ya nufi wajen motar shi zai shiga ya na fad'in "Kar ki damu ba sai kince komai ba, ba dai haka tace ba? To barni da ita, nasan sosai, marar mutumci ce ta gidan gaba, amma zan wa tubkar hanci." Ya na fad'a ya kashe wayar, ita kam har da tsalle duk da bata san me zaiyi ba tasan dai ta sake gogawa Khadija bak'in panti, zai shiga mota Murtala ya rik'o hannun shi ya na kallon k'wayar idon shi yace "Wannan kamar ba Usman d'ina ba, ya naga ka canza haka, me ya faru ne?" K'ara had'e rai ya yi yace "Ka bari dan Allah ina zuwa yanzu, akwai abin da ya faru ne da gaggawa a gida." Ya na fad'a ya janye hannun shi ya rufe motar ya wuce zuciya sai tafasa take an tab'a mi shi Haseenah, *Abu azimun inji wata k'awata*, aifa abu ya girmama fiye da yanda ma su karatu suke tunani, dan Usman baiyi k'asa a gwiwa ba wajen zuwa ofishin 'yan sanda akai k'arar Hajia Turai akan taje gidan shi ta ci mutumcin matar shi har da mata barazana, zai iya d'aukar mataki amma dan kar ace ya d'auki doka a hannun shine ya sa ya garzayo nan, amma a mata kashedi ba ita ba gidan shi ko da kuwa me ya ke faruwa a gidan. Nan fa aka kaiwa Hajia Turai takardar sammaci har gida, lokacin zuwan ta kenan tare da wasu samari da suka d'auko mata kaya sai ga motar 'yan sanda, ana bata takardar ta shiga motar ta fara bala'i tun daga cikin motar, fad'in take "Ai Usman k'aramin d'an hau ne, baisan ni d'in nan babu gidan kason (magark'ama) da ban kwana ba, wani jami'i ne da ya kwana ya tashi a garin nan bai sanni ba, ko ya d'auka duk bala'in nawa iya baki ne, to muje na nuna mi shi yanda ake rawar...kalmar data fad'a ba dad'in ji, amma dai kamar wannan abar ce ta anbata mai kama da ayaba."😎 Su na isa kad'an ne ya rage ofishin ya kama da wuta saboda yanda Hajia Turai ta d'aga murya take masifa, haka Usman bawan Allah ya zama kamar mahaukaci saboda shegiyar Haseenah shima ya biye mata, mutumin da ko da matanshi ba ya son hayaniya amma sai gashi ya zage damste a waje tare da k'awar matar shi suna musayar yawu, ita tana fad'in ita zai ci wa mutumci saboda yar iskar matar shi, shi kuma ya na fad'in akan me za ta je gidan shi ta yiwa matar shi wulak'anci, cikin masifa take fad'in "Kai in banda ma sususu ne kai, wannan tsomalalliyar yarinyar har yaushe ta zo gidan, yaushe ka fara cin gindin ta da har ka mance kalar gindin Khadija 😎, kenan ita wajen bokaye ta kai ka, banza kawai lusari marar kunya, kai har ka isa ka manta hallacin da Khadija ta ma ka, tun ba ka da komai take tare da kai, kusan ma ita ce silar arzik'in ka, amma shine yanzu ka samu sabon..." Da k'yar dai wanda ke mu su shari'a yace kar ta sake zuwa gidan shi, kuma kar wani abu ya samu matar shi, in ba haka ba za ta shiga hushin hukuma, bud'ar bakin ta cewa ta yi "Wallahi kunji na rantse ko, da ace nasan in da ake siyar da k'ank'arar mayu to da na siyo ba dan komai ba sai dan na lashe matar ka, ka sani ba zan sake zuwa gidan ka ba, amma wallahi tallahi na had'u da matar ko sai na ci kakan..., tunda tace ma ka na yi abin da banyi ba kuma ta lak'awa k'awa ta sharri ko, to ba makawa sai ta samu shaidar sanin Hajia Turai, ka dube ni da kyau Usman kai ka sanni, wallahi k'aramin aiki na ne na keta yarinyar nan da wuk'a, kuma a shirye nake da na je duk kotun da aka kira ni dan shari'a akan ta, banzaye kawai daga kai har ita." 😂 _Allah ya kyauta._ Nan aka raba su kowa ya kama gaban shi, amma fa Hajia Turai ta zuba ido da kunne ta na jiran ta ji wani sabga da zai taso wanda zaisa ta had'u da amaryar Usman, Usman kam tunda ya shiga mota ya kifa kan shi yake jin zuciyar shi babu dad'i haka ma yanayin shi, wai me ya faru da shi da har ya aikata wannan abun kunyar? Gashi ya ja bala'in da yafi k'arfin na shi ta ci mutumcin shi son ran ta, Me ya sa ya yi haka to? Me ya sa baiyi bincike ba ko ya duba al'amarin? Amma kuma ya na tunawa da Haseenah sai zuciyar shi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117