Skip to content

Chapter 70

Chapter 70

Kallon Kitse Book One Complete Hausa Novels 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

yi yace "Tonton Nura, ina kwana?" "Lafiya lau, ka tashi lafiya?" "Lafiya lau." Ba tare da ya shigo ba daga k'ofar yace "Ina maman ka?" "Ta na madafa." Ya fad'a da ma sa nuni da yatsarshi, hannu ya d'aga ma sa yace "Ina zuwa to." Madafar ya nufa da sallama, ya na ganin Khadija yace "Uwar gida ran gida, uwar gida sarautar mata, kowa ya shigo gida ke ya tarar, ko mai gida sai kin lamunce ya shigo, sannu da aiki." Da wuk'ar hannunta ta nuna shi tace "Bansan dad'in baki, fad'i abin da ka ke so na ma ka." Cikin had'e rai yace "Kamar ya? Ban gane me ki ke nufi ba?" Kallon shi ta yi tace "Ai dana gan ka gidan ka to da dalili, bugu da k'ari kuma gashi har da min wani kirari kamar marok'i." Dariya ya yi yace "Lallai uwar gida daban ki ke da kowace mace, cikin sakan biyar har kin fahimci akwai abin da na ke buk'ata ki min ko?" Hararan wasa ta mi shi tace "Yau da gobe ai bata bar komai ba, karfa ka manta a hannu na ka k'arasa girma." B'ata rai ya yi yace "Haba kema, basar mana." "To naji, me ka ke so." Saida ya matso kusan ta yasa hannu ya na cakurar dankalin da take soyawa ya na jefawa baki yace "Aunty Khadija maganar fa mai mahimmanci ce." "Uhum, ina jinka." Saida ya saci kallon ta yace "Aure na ke so." Da sauri ta dakata daga abin da take ta kalle shi tace "Me? Aure fa ka ce Nura?" "Eh mana, ko ban isa ba?" Zaro ido ta yi tace "Ni bance ba, amma dai me zai hana ka bari kad'an k'ara mallakar hankalin kan ka, Nura aure fa ba iya abin da kawai ka ke tunani bane." Kamar zaiyi kuka yace "To ni me na ce mi ki ina tunani?" Mirmushin gefen labb'a ta yi tace "Ba ma irin wannan hirar da kai, amma na tabbatar ba zai wuce wutar balaga ce ke fizgarka ba." "Kinsan me?" Ya fad'a ya na rik'e k'ugu, "A'a sai ka fad'a." "Mijin ki ma haka yace da na masa magana, wai na bari har nan da ko shekara biyu, a gaskiya kuma ni ba zan iya ba, aunty Khadija wallahi gaskiya na ke fad'a mi ki, na fad'awa su Baba sunce ba ruwansu na fad'awa Usman tunda shine zai min auren, shi kuma yace ba yanzu ba." Ajiyar zuciya ta sauke tace "Yanzu me ka ke so na ma ka?" Cikin sigar rarrashi yace "Ki daure dan Allah ki taimaka min ki ma sa magana, wallahi nasan zai saurare ki, ni fa har mun gama magana da iyayen yarinyar ma, sunce kawai na turo manya na." "Babbar magana." Cewar Khadija, "Haba wannan k'arama ce, yanda na san ki da Abban yarima ai sha yanzu mgani yanzu ne." "Sanin da ka yi mana ada ne wannan." Cewar Khadija a zuciyar ta. Basarwa ta yi tace "Shikenan kar ka damu, zan jaraba na gani, amma ba lallai ya amince ba tunda har ya nuna bai yarda ba tun farko." "Zai ma amince in dai ki ka masa magana wallahi." Da haka ya bar gidan ita kuma ta shiga tunanin yanda za ta fara tunkarar sabon Usman d'in ta da maganar nan, ba ma lallai ya saurare ta ba bare har ya amince da abin da Nura ke tsammani. Ta na gama abin karin ta bawa Bilal na su Haseenah ya kai mu su, suma ko da su ka kammala suka fito farfajiyar gida, Bilal na yawo da moton shi a tsakar gidan Khadija zaune da waya ta na tunanin ta kira ko karta kira, ta na haka sai kiran shiya shigo wayar ta, yau ma mamaki ta yi ganin kiran shi, hakan ya sa ta d'auka ta aza a kunne, ba sallama bare gaisawa yace "Na kira Hajia akan maganar tafiyar nan, sai ki shirya da wuri ki same su can gida dan sun ce Naseer ne zai kai su." "H...hello." Ta fad'a da sauri saboda jin zai katse kiran, cike da k'aguwa yace "Ina ji? Lafiya?" Cikin fad'uwar gaba tace "Lafiya lau, dama ina son yin magana da kai ne." "Magana akan me kuma?" Murya k'asan mak'oshi tace "Nura ne dama ya same ni akan maganar aure da ya ke so, amma yace ka ce ba yanzu ba, shine..." "Shine za ki sani na yarda na mi shi auren ko me?" Ya fad'a cike gatsali, kamar ta kashe wayar sai kuma ta daure tace "A'a ba haka bane, ya fad'a min ne saboda shi a tunanin shi Khadija tafi k'arfin komai a gurin Abban Bilal, ya zo da buk'atar shine gare ni saboda sanin da ya mana ina iya shawartarka akan al'amura har na cikin gida ma kuma ka yi aiki da ita, ya fad'a min ne ba dan tunanin zan saka ka dole ba, sai dan cewa kamar ina da mahimmanci da kima a wajen ka da zan iya nemawa wani alfarma a wajen ka, sannan ni a gani na ba wani abu bane idan an mi shi auren, matashi kamar Nura ya kalli iyayen shi yace ya na son aure, ina ga a mi shi auren shi yafi kwanciyar hankali." Har k'asan zuciyar shi maganganunta sun ratsashi, amma saiya dake yace "Me Nura ya sani a game da aure da za ayi mi shi? dan ya na da abinyi ba shi ke nuna zai iya rik'e mace ba." "Amma ai ko neman auren ya tafi daga cikin tambayoyin da za'a masa akwai son sanin abin da yake, hakan kuma nasara ga d'an uwan mu da ya zamana ya na da aikin yi, ko ba komai zai ciyar da ita, zai shayar da ita da tufatar da ita, sannan ina da yak'inin zai kula da ilimin ta ko wane iri ne, sannan zai iya biya mata buk'atar ta." Saida taji sautin sauke ajiyar zuciyar shi a kunnenta kafin yace "Bansan me ya fad'a mi ki haka ba da ki ka yarda da shi, gashi har kinsa nima na ji banda wata hujjar hana shi auren, ki fad'a ma sa na amince, amma dole ya jira ni na dawo sai ayi duk wacce za ayi, idan kuma ba zai iya jira ba sai ya turaki ki nemo masa auren." Ya na fad'a ya kashe wayar, ita kam dad'i ne ya sata bushewa da dariya saboda abin da ya fad'a a k'arshe, wayar Nura ta kira ta fad'a ma sa yanda su ka yi da shi, sosai ya yi murna tare da binta da addu'a Allah ya barta da yayan su, suna gama waya ta ji wayar Bilal na k'ara, hannu ya sa a aljihu ya fito da ita ya d'auka, take ta fahimci Abban shi ne ya kira shi, suna nan zaune Hajia ta shigo gidan da sallama saboda ganin su, da farin ciki Khadija ta mik'e ta tarbe ta tana mata sannu da zuwa su na gaisawa, Bilal ma saida su ka tab'a hira irin ta kaka da jika kafin ta kalli Khadija tace "Ina yer uwar ta ki ta na ciki?" "Eh Hajia su na ciki." Nufa b'angaren ta yi ta na fad'in "Bara mu gaisa." "A fito lafiya."

Table of Contents

Chapters

117 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117