Skip to content

Chapter 117

Chapter 117

Kallon Kitse Book One Complete Hausa Novels 768 words 0 views Progress saved
Download Book

yarima ma zai zama waliyi na." Dariya suka saka a tare sai Khadija da tace "Komawa baya kenan, to idan zaka je d'aurin auren dai ka shafa gawayi a kanka danka rufe wannan farin abun na kan ka." Sake shafa kan yayi yace "Alamar arzik'i ne ai, kuma naga kema akwaita a kanki." Cike da k'aguwa Bilal yace "wai yanzu na zo da matsalata amma ku manta kun shiga sabgar gabanku, Allah ya shirya min ku iyayena, banda kamarku a duniyar nan." Harya juya zai fita ya tsaya ya nuna su Humaira da yatsa yace "Kuma wallahi babu inda za ku je, na gaji da wannan yawan na ku kullum." Khadija ce tace "To ni ka ban makullin tawa motar zan fita, ai dai kasan aro ne na baka jiya ko." Kallon Usman yayi yace "Idan sarki ya bayar da izinin fita sai ku fad'a min zan kawo mu ku." Cike da jin dad'i Usman ya aika mishi da sumbata yace "Allah ya maka albarka yarona, shi ya sa banda matsala da gidan nan ko bana nan nasan akwai original Usman a gidan, da ni ne da yanzu sun min fari da ido na basu makullan." Fita yayi daga d'akin sai Usman daya kalli su Aisha yace "Ku kuma ki fito daga nan munafukai kawai, dama da kinga suna raba ido kinsan basu da gaskiya, kuma wallahi ku ka sake shigar masa d'aki ba neman izini da kaina zan hukuntaku." Cikin turo baki suka sauko suka fita daga d'akin suna kumbura, dan tunda su ka ji Bilal ya rantse sun sa babu inda za su je, suna fita Usman ya kalli tsofaffin nashi yace "Ku shirya da kyau, wannan hutun na k'arshe zan had'a yaran nan da Bilal na aurar da su." Wata sanyayyar ajiyar zuciya Khadija ta sauke tace "Alhamdulillah, wallahi naji dad'i da wannan maganar, dan duk sanda na kalli yaran sai naji fargaba ya ziyarceni, gashi k'awayen su sun fara aure, sai kaga an fara sakawa yaranka wani tunani na daban alhalin kana tsaye kan tarbiyarsu tsawon lokaci." Haseenah ce tace "Allah yasa haka shi yafi zama alkairi, amma ka fitar musu da maza ne?" "Eh to, a tunani na dai da zan had'a Aisha da *Kamal* (babban d'an Murtala) ne." Humaira kuma sai a had'a ta da *Mujahid* (d'an Issoufou d'an uwan Usman), amma fa sai in basu da wanda suke so, dan ba zamu had'a su da wanda ba sa so ba tunda zamaninmu da nasu ba d'aya ba, da a lokacin yanzu ne aka mana auren da aka yi mana ni da *Dijangala* to na tabbatar ba za su zauna ba." "Ai ko ni da ga yanzu ne aka had'a ni da kai to da babu abin da zanyi da tsoho." Cewar Khadija kafin ta d'ora da "A gaskiya dukansu sun fad'a min suna da samarinsu har shi Bilal d'in." Kallonta Usman yayi yace "Kenan duk sun fad'a mi ki nine suka mayar bare." Gwalo ta mi shi tace "Nifa uwa ce." Haseenah ce tace "Aunty su wa suka fad'a mi ki suna so?" Cike da k'asaita tace "Sirri ne tsakani na da yara na." Tasowa Usman yayi ya bata kunnanshi yace "To fad'a min a kunne naji." Ai kuwa rad'a mi shi tayi cewa "Bilal ya fad'a min suna soyayya ne da *Ikram* (yar Kaltume), sai Humaira tace suna soyayya da *Kamal* d'in da ka ke son had'a Aisha da shi, sai kuma Aisha tace wani yaro ne mai sunan *Jabir*, d'ane ga Alhaji Abbakar, amma kuma da wata yar matsala." Kallonta ya yi yace "Matsalar me?" D'orawa ta yi da "Domin kuwa *Miemie* (yar Ashir) tana mutuwar son Bilal, dan har ta fad'a masa ma, kuma yace ba zai iya cewa baya sonta ba saboda tana birge shi sosai." Dariya usman ya yi sosai kafin yace "Dan haka saiku shirya, yaronku da mata biyu zai fara insha Allah, na yarda da mazantakarshi." _Tofa fan's wata sabuwa, ga Usman na shirin lak'abawa Bilal mata biyu a lokaci daya, tabbas akwai wasu darussa a cikin labarin rayuwar gidan Bilal, sai dai Meeranku yanzu ta zama lazy wrriter, da zan zo na kawo mu ku d'orawar shi amma ba zan iya ba saboda na gaji yasin._ *Alhamdulillah* *Alhamdulillah* *Alhamdulillah* *Ina godiya ga Allah da ya nuna min na kammala littafi lafiya kamar yanda na fara, Allah ubangiji kasa a anfana da darasin dake ciki, Allah ka sa mu tsarkake zuciyoyinmu wajen yin kishi mai tsafta, duk wanda suke da abokan zama Allah ka k'ara had'a kansu, wanda basu da kuma Allah ka had'a su da na gari, Allah ka k'ara sanyaya mana zuk'atanmu.*👏👏👏

Table of Contents

Chapters

117 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117