Skip to content

Chapter 66

Chapter 66

Kallon Kitse Book One Complete Hausa Novels 1,203 words 0 views Progress saved
Download Book

dan haka ta marairaice tace "Um,um gaskiya ni na fasa tafiyar ma, ka ga kai kasuwancin ka ne zai kai ka, bai kamata muje tare ba kuma na hana ka sabgar gaban ka, kawai kaje Allah ya tsare mana kai, ranar da na haihu sai mu tafi tare da yaronmu mushak'ata." Saida ya rumgume ta yace "Gaskiya ban ji dad'i ba, Haseenah ba zan iya farin ciki ba ki na nesa da ni, me ya sa ba za ki je ba? Zan iya yin wata d'aya fa ko sati uku ban dawo ba, ki na ganin zan iya rik'e kai na bayan na saba da ke a d'an lokacin nan." Cike da gatsali tace "To ba ga aunty Khadija ba, ku je tare mana, ni kuma sai mu zauna abunmu ni da yarona Bilal, ko ya ka ce?" Tunda ta ambaci sunan ya ji kamar ta jefe shi da mashi akan tsohon ciwon shi, b'ata rai ya yi yace "Ya ina magana da ke za ki kawo min maganar matar can? Gaskiya ba na so kar ki sake." Saida ta shafi fuskar shi tace "To shikenan yi hak'uri ba zan sake ba." "To yanzu fad'a min za ki je ne?" Ya fad'a ya na k'ara cukuikuyeta, ba alamar wasa tace "Gaskiya ba zan je ba, kawai ka tafi kai kad'ai." "Shikenan, amma taya zan barki ki zauna tare da matar can? Na ga fa ba wani sakin jiki ki ke da ita ba." Shiru ta yi ta na tunanin abinyi ita ma, da sauri yace "Ko na kira Hajia ta turo mi ki Aziza? Tunda kinga dama ita ce ke zuwa nan idan zanyi tafiya." Wani murmushi ta yi da bai kai ciki ba tace "To shikenan ba damuwa, hakan ma ya yi ai." Da haka ya fito ya shiga d'akin shi ya yi wanka ya shirya ya fito kan teburi, saida Haseenah ta fito kafin su ka fara cin abincin, tabbas daga yanda ya ke cin abincin za ka san ya masa dad'i, amma da zaran ya had'a ido da wacce ta dafa abincin saiya d'aure fuska, haka su ka gama ya tashi ya fita su ka bishi da addu'a, Khadija da ta bi bayan shi har wajen mota sannan ya juyo ya kalle ta yace "Ya dai malama ki ke bina haka?" Murmushi ta yi tace "Abban Bilal hushi ka ke dani har yanzu akan abin da ya faru?" Wani d'auke kai ya yi yace "Mtsss, ba komai kawai, kawai dai ki na ba ni mamaki ne." A hankali ta janyo hannun shi ta na shafawa, in da shi kuma ya ke jin kamar hannun wuta ne da ita, cikin taushin muryar da tasan ta na tasiri akan mijin ta ta fara magana "Dan Allah ka yi hak'uri ka yafe min, insha Allah ba zan sake b'ata ma ka rai ba, ka ji? Ka yafe min, kasan hankali na ba ya kwanciya idan ina ganin ka haka." Saida ya raba hannunshi da na ta yace "Shikenan ba komai, Allah ya sa haka." Juyawa ya yi zai shiga mota tace "Shikenan kuma ba komai za ka tafi." "Kamar me fa?" Cikin yanayin jan hankali tace "Ba rumgumewa, ba sumbata, abun ba armashi." Kasak'e ya yi ya na kallon ta da tunanin abinyi, matsawa ta yi kusan shi ta shafo fuskar shi, a hankali ta kai bakin ta kan na shi ta zura harshenta cikin bakin shi, harshenshi ta kama tana wasa da shi in da ta kai d'aya hannun ta cikin rigar shi ta na murza k'irjin shi, d'aya hannun kuma shafar sumar kan shi take ta na yamutsata, tunda ya lumshe ido ya rasa kuzarinshi, hak'ik'a ya na son abin da take ma sa sosai d'in nan, amma ya na jin ba zai iya biye mata ba, amma da ya ke Khadija bala'i ce saida ta watsa mi shi duk wani lissafin shi da nutsuwa ya ma manta ina ne ya ke yanzun, me kuma zaiyi ko ya ke yi, saida ta ji jikinshi ya saki sosai sai wani gurnani da yake ya na k'ok'arin kai hannayen shi cikin rigar ta kawai ta raba kan ta da shi, wani arnan kallo ta masa da manyan idon ta a cikin gilashi kafin ta kashe mi shi ido d'aya, wata yar mik'a ta yi tare da fad'in "Ashhhh." Bye bye ta mi shi ta juya da nufin komawa ciki, wata karairaya ta dinga yi wanda ya sa hankalin Usman k'ara tashi saboda yanda take juya jikinta, wata zabura ya yi saboda wani zirrrrr da ya ji tun daga k'asa har sama, fitowa ya yi daga motar ko rufewa baiyi ba ya bi bayan ta har da gudu ya na so ya kamo ta, ta na shiga falon ta ga Bilal zaune sai kawai ta wuce d'akin ta, Bilal na ganin baban shi ya bi bayan maman shi sai kawai ya mik'e ya fita, wajen mai gadi ya zauna su na hira ya na kallon hanya, Usman na shiga wani k'arfi ne ya zo mi shi cikin sauri ya ke son aika sak'on shi, haka dai al'amari ya yi nisa sosai suka gangara, tabbas tun bakin k'ofar za ka ji abubuwa kala kala masu rikatar da mutum, amma ya na k'arasa shiga ciki sai ya ji wani b'acin rai da rashin ma'ana da...abubuwan ma dayawa, da k'yar ya k'arasa abin da ya fara cikin d'an lokaci ya samu nutsuwa ya tashi ya yi wanka ya saka kayan shi, ko kallon ta baiyi ba ya wuce abin shi ya na jan tsaki ya na gunguni. *A gurguje* Bayan ya fita gida ya nufa in da ya aje mu su duk wani abun buk'ata, sannan ya fad'awa Hajia ta tura Aziza can ta taya Haseenah kwana, tunda yamma ko da Haseenah ta karb'i girki Usman ya zo gidan, bai bari ta yi aikin ba ya zura ta d'aki ya na ta huce haushin shi na safe, har saida ta kai ita kan ta Haseenah ta fara nadamar kan ta dan ba k'aramar wahalar da ita ya yi ba, hakan ya sa ko da dare ya yi yace ta shirya suje cin abinci, saida su ka shirya za su tafi ya shigo falon Khadija yace Bilal ya zo su fita unguwa, sam ba ta yi tunanin har da Haseenah ba, har su ka fita sune sai sha d'aya da rabi na dare suka dawo, kai tsaye kowa falon shi ya nufa, sai lokacin ne Bilal ya fad'a mata har da auntyn shi su ka tafi, ba ta nuna mi shi komai ba, amma ta na shiga d'aki ta yi yan dabaru ta ci abinda ya sawak'a saida ta zubar da hawaye, har ta yi bacci ba ta ga Usman ba da sunan zai mu su saida safe. Misalin *08:10* ya shigo falon ta cikin shirin da gani ba tambaya kasan tafiya zaiyi, tare suke da Haseenah dan Bilal na d'aki har yanzu ya na shiri, kud'i ya mik'o mata yace "Ga wannan kya yi anfani da shi, ni yanzu zan wuce Niamey zuwa asuba kuma jirgin mu zai tashi, nasan akwai komai babu wani abin da za'a buk'ata, sannan maganar kai Bilal makaranta na barwa amarya ta duka makullan motar da tawa da taki,

Table of Contents

Chapters

117 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117