Skip to content

Chapter 13

Chapter 13

Kallon Kitse Book One Complete Hausa Novels 1,199 words 0 views Progress saved
Download Book

gidan mijin ki ba." Cikin sanyin jiki Haseenah tace "Ke, wannan ai ba komai bane, gaskiya ta fad'a." "Tab'." Cewar Aziza tare da kallon k'awar ta, farantin abincin su ta d'auka ta d'auki bredin tace "Muje d'aki sai mu ci ko." Tashi su ka yi su ka bi bayan ta, abinci su ke ci su na hira, Haseenah dai na sauraren su sai dai ta yi dariya, har su ka gama su ka d'ora daga inda su ka tsaya, ko da yamma ta yi su ka kama mata aikin dare ta yi, da su ka gama za su tafi kyaututtuka ta ba su, turaruka da sauran kayan kwalliya da kud'i wai su shiga adaudaita, da k'yar su ka karb'i kud'in da ta dage sosai, su na tafiya ta koma d'aki ta yi wanka ta shirya dan tarbar mijin ta, ta na gamawa ta d'auki d'aya kwanukan abincin ta sallama har falon Khadija, amsawa ta yi Bilal na zaune kusa da ita ya na karatu, da murmushi ta amsa ta na fad'in "Amarya ke da kan ki?" Sunkuyawa ta yi ta aje kwanukan ta d'ago ta kalle ta tace "Ga abincin ku nan." Juyawa ta yi za ta fita Khadija tace "A'a, ban gane abincin mu ba, ni da wa? Ko kin manta ba'a raba abinci a gidan nan? Ai Abban Bilal bai yarda da haka ba, duka iyalinshi su na cin abinci tare ne." Juyowa ta yi cike da gadara da ido tsakar kai tace "Eh, na sani, amma waccen ai tsohon yayi ne, yanzu kuma na shigo gidan, dole za'a samu canje-canje da dama, daga yanzu in dai girki na ne gaskiya miji na zai ci abinci a nawa b'angaren ne ba na shi ba." Juyawa ta yi har ta fara takawa Khadija ta gyara zama tace "Haseenah, nasan kinsan abinda ki ke shirin aikatawa kamar k'ok'arin rusa farin cikin gidan nan ne, dan haka kar ki ce za ki biyo min ta wannan hanyar, da ba zan d'auka ba, kin ganni nan? Wallahi ba na d'aukar raini ko rashin kunya, zaifi mi ki tun wuri ki fara taka tsantsan, abinci kuma ki d'auki kayan ki ba zan ci ba, ba kuma zan bawa yaro na ba, dan bansan me ki ka saka mana a ciki ba." Wata dariya Haseenah ta yi tace "Ikon Allah na kwance ya fad'i, wato ke yanzu tunanin ki kenan? Nima zan yi abin da ke ki ke yi ne, hum! To ki farka, ni ba boka ba malam zan mallaki miji na, ke kuma da ki ke barbad'e a abinci sai ki yi ta yi, da sannu k'aryar ki za ta k'are a gidan nan." Tsaye ta mik'e da mamaki a fuskar ta tace " Au! Kema tunanin ki kenan? Hhhhhhhh, lallai yarinya, in kuwa har wannan shine tunanin ki, to ki zanca tun wuri, dan wata rana zuciyar ki za ta iya raya mi ki kema ki bi boka da malam dan samun zuciyar babban mutum, kinga kuwa har abada ba za ki san sirri na ba." Matsowa ta yi kusan ta dafa kafad'ar ta tace "Haseenah, ina kishin miji na, amma duk da haka bai sa na ji a raina cewa zan iya cutar da ke ba, ki kwantar da hankalin ki sannan ki nutsu, sannu a hankali sai kema ki ciri tuta a wajen mijin ki, ni zan taimaka mi ki kamar yer uwa ta." Matsawa ta yi nesa da ita yace "Me? Taimako? Ki na kishiya ta za ki taimake ni dan na samu soyayyar mijin mu? Allah ya kiyaye, to me ki ka d'auke ni? Ban cika mace ba ko me? To ba na buk'ata, nasan hayoyin da zan shawo kan miji na, ba sai wani ya taimaka min ba." Murmushi Khadija ta yi wanda har ya fito da haurun makkar ta guda biyu, Haseenah kam juyawa ta yi ta koma na ta falon ta zauna, ta na kallo Haseenah ta shigo da kwanon ta aje mata a kan teburin ta ta fice, tab'e baki ta yi tace "Ina daidai ke wallahi, sai dai duk abin da zai faru ya faru." Ba jimawa kam sai ga Usman ya shigo, kai tsaye b'angaren Khadija ya nufo da tunanin zai tarar da duka iyalin na shi anan, Khadija da ran ta ke b'ace kasa tashi ta yi ta tarbe shi kamar yanda ta saba, da gudu Bilal ya k'arasa ya rumgume shi, tare su ka k'araso wajen ta ya na fad'in "Yarima wa ya tab'a min mamanka ne haka?" Hannu ya mik'awa Khadija alamar su yi musabaha, dan in Bilal na tare da su suna kiyayewa wajen tab'a juna tun da ba k'aramin yaro bane, hannun ta ba shi lokacin da ta ke kallon Bilal da shi ma ya ke kallon ta, murya k'asa k'asa yace "Ba komai Abba." Zaune ya yi kusa da ita ya na kallon ta yace "Ba gaskiya ka fad'a ba yarima." Kallon shi ta yi tace "Sannu da zuwa." "Sannu da gida, ya kuka wuni?" "Lafiya k'alau." Ta fad'a a tak'aice, dariya ya yi ya kalli Bilal yace "Ka gani ko? Na fad'a ma ka akwai wani abu, ba haka Khadija ta ke amsa min ba." Murmushin yak'e ta yi tace "Kai ma kasan in dai ka na lafiya to mu ma mu kan kasance cikin k'oshin lafiya." D'an juyawa ya yi yace "Ina amaryar ki ne ban ganta ba?" D'an canza fuska ta yi tace "Ta na b'angaren ta mana." Mik'ewa ya yi tare da kamo hannun ta da na Bilal yace "Muje to mu ci abinci ko, dan yunwa na ke ji sosai." Fizge hannun ta ta yi tace "Kaje kawai ka ci, mu har munci abincin mu ai." Da tsantsar mamaki ya ke kallon ta, amma sam ta k'i had'a ido da shi, hannun ta ya sake kamawa su ka nufi d'akin ta ya maida k'ofar ya rufe ya juya ya na kallon ta yace " Ina jinki, fad'a min me ya faru?" Zaune ta yi akan gado tace "Ba komai." Had'e fuska ya yi yace "Khadija kar ki min k'arya, gaskiyar abin da ya faru na ke so na ji." "Nace ba komai ko, ba komai, kaje kawai ka ci abincin ka, ni da d'ana har munci." Ajiyar zuciya ya sauke ya zauna kusa da ita yace "Khadija, wannan ba d'abi'ar ki ba ce, dan Allah kar auren da na yi ya sa ki canza daga yanda na sanki, kinji ko." Shiru ta yi har sai da ya janyo ta ya na shirin kai bakin shi a nata ta yi saurin rufe bakin ta da hannun ta, wani tuhumammen kallo ya mata yace "Meye haka? Ba kya so ne?" "Eh." Ta fad'a tana mik'ewa tsaye, fizgo ta ya yi ta koma kan gadon da k'arfi, kafe ta ya yi da ido yace "Me ya sa?" Juya mi shi baya ta yi, sake juyo da ita ya yi yace "Nace me ya sa ba kya so? Sai kin fad'a min dalili na rabu da ke." Zuciya a wuya sai kawai Khadija ta fashe da kuka ta fad'a kan k'irjin shi, cikin kukan tausayi tace "Ba na so kawai, Abban Bilal ba na so ka na kusanto ni, haushin ka na ke ji

Table of Contents

Chapters

117 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117