Chapter 85
Chapter 85
kasancewar ba sabon abu bane ya sa Hajia cewa idan malam ya zo za ta fad'a mi shi, idan ya amince saita kira a fad'a mi shi, nan ta d'auko ruwan duka biyu ta bashi ya shanye kafin ya fita, daga nan wajen Murtala ya nufa su ka d'an tab'a hira har ya na tsokanar shi wai amarya da uwar gida sun hana shi fita ko ina, nan ya kalle shi ya tab'e baki yace "Wace uwar gida kuma da ba ta nan?" Da mamaki Murtala yace "Ban gane ba ta nan ba, to ta na ina?" K'ara tab'e baki ya yi yace "Ta na gidan su mana." "Gi me?! Murtala ya fad'a da k'arfi har da dafe k'irji, a wulak'ance ya kalle shi yace "Gida na ce, gidan iyayen ta, ko tafi k'arfin zuwa gida ne?" Kai tsaye ba tare da fargaba ba Murtala yace "Ta fi k'arfi, wallahi in dai Khadija ce tafi k'arfin haka aboki na." Sake tab'e baki dai ya yi yace "Sai kuma ka yi kan ka ake ji." Dafa shi Murtala ya yi yace "Wai dan Allah in tambaye ka mana? Ka na nufin ta tafi gidan su saboda ganin damar ta? Ko kuma kai ka kora ta gida? Ko kuma ma dai wasa ka ke min?" Cikin hassala yace "Ya zan ma ka wasa da wannan maganar, wai ita Khadijar nan me ku ke d'aukar ta ne da ba za'a hukunta ta ba?" Wani kallo Murtala ya ma sa yace " Mun d'auki Khadija a matsayin rayuwar Usman, sannan Khadija ita ce sirrin duk wata nasara ta Usman, kar ka manta da haka aboki na, duk abin da ka zama yau Khadija ta taka muhummiyar rawa a zuwan ka wannan matakin, amma gaskiya abin da ka yi yanzun kasa ni kai na na fara jin kunyar had'uwar da ita da iyayen ta da kuma 'yan uwan ta, shin aboki na yanzu da wane irin ido za ka iya kallon Ashir idan kun had'u ko da bisa hanya ne?" Cikin b'acin rai ya kalle shi yace "Da wane ido fa, da idon da ya ke kallon na shi 'yan uwan matar wacce ya saka lokacin da zai k'ara aure, Rahama ba, ka tuna da ita? To ai gwara ma ni tunda ba sakin ta na yi ba, kuma ita ce ta d'auki kayan ta ta tafi ba ni nace ta tafi ba." Murmushi Murtala ya yi yace "Kafi kowa sanin dalilin da ya sa Ashir ya rabu da Rahama, ta yi ikrarin in har ya k'ara aure to ba shi ba kwanciyar hankali, sannan daga lokacin ta dinga nuna raini akan mutanen da suka fi komai daraja a wurin shi, mahaifiyar shi da kuma Khadija, wulak'anta su da ta fara yi ta na kallon su kamar sune ke zugashi ya sa ya kasa jura ya sallame ta, amma kai kuma fa? Fad'a min tayar ma ka da hankalin da ta yi." Tsaki ya yi yace "Kaga, ni ban zo nan ba saboda jin wannan maganganun, kawai..." Dafa shi ya yi cikin nutsuwa yace "Me ya ke damunka aboki na? Fad'a min miye matsalar mana? Khadija ce fa, matar nan da ba ka son komai sama da ita, ina wannan soyayyar? Ina wannan k'aunar? Ko da yake ma bai kamata na tambaya ba, nasan har yanzu ka na son ta." "Ba gaskiya bane, ni yanzu ba na son ta." Ya fad'a ba alamar wasa, murmushi Murtala ya yi yace "Ka rufe idon ka, sannan ka saurari zuciyar ka ita kad'ai, kar ka bari wani tunani ya shiga tsakanin ka da zuciyar ka, ina tabbatar ma ka hoton Khadija za ta gani." Ya na fad'a ya mik'e ya shiga cikin shagon shi dan ya ba shi dama, Usman kuma na ganin haka saiya mik'e ya tashi ya shiga motar shi shima ya bar wajen, gida ya koma ya na zuwa mai gadi ya bud'e masa k'ofa ya shiga, har ya aje motar a muhallin ta kalaman Murtala na masa yawo, hakan ne ya tilasta masa dafe sitiyari ya rufe ido ya na mayar da nutsuwar sa gare sa, ya jima a haka kafin ya zuba ya bud'e ido saboda ganin Khadija da ya yi cikin doguwar riga bak'a, gefen ta Bilal sai dariya suke suna kallon wani abu da ya birge su, amma ko da ya bud'e ido ya na tuna fuskar ta saiya k'ara had'e fuska, tsaki ya yi kawai ya fito daga motar ya wuce wajen amarya. Da shigar shi ya samu Haseenah na waya da Mariya akan maganar su, kasancewar a shirye take ya sa tace ta karb'o sak'on ta zo ta amsa ko ta aiko a karb'ar mata, a cewar Haseenah "Zan kira yah Mubarak ya je ya amso min." Da "Sai ya zo." Mariya ta amsa su ka datse wayoyin. Wanka ya fara shiga ya yi ya fito d'aure da abin tsane ruwa a k'ugu (towel), wayar shi ya d'auka gaban madubi ya danna kiran lambar Bilal, a daidai lokacin Bilal na zaune gaban Khadija su na karatu, ya na fito da wayar daga aljihu ya datse kiran saboda ganin mai kira, irin shi ma wai an tab'a mi shi mahaifiya d'in nan, ganin hakane ya sa Khadija kallon shi tace "Bilal, ba kiran ka ake ba na ga ka na katsewa? Waye haka?" Turo baki ya yi gaba baice komai ba, dariya Khadija ta yi tace "Ko dai surukata ce ta ke kiran shi ya sa ba ka so ka d'auka gaba na?" Kamar zai fashe da kuka yace "Mummy." "To waye ke kira?" Ta fad'a ta na d'aukar wayar da ya aje saman gado, tana dubawa ta ga mahaifin shine ya kira ya katse, da mamaki ta d'ago ta kalle shi tace "Bilal! Mahaifin ka ne dama ya kira ka ke katse shi?" Kafe ta ya yi da ido, cikin tsawa tace "Da kai na ke magana ka na jina ka yi shiru, ina so na ji hujjar da tasa ka ke datse kiran shi ba ka d'auka." Cikin turo baki yace "To Mummy ba Abba ne ya daina son mu ba, kuma a gaba na fa ya dakkk..." Kashe shi ta yi da marin da ya sashi saurin dafe kumci ya fashe da kuka, cikin zafin rai ta d'ora yatsanta akan bakin ta tace "Shiiii, kar ka bari na ji sautin muryar ka har zuwa lokacin da zan gama magana." Gimtse kukan shi ya yi ya na kallon idon ta tace "Bilal matsala ta ce fa da mahaifin ka, kai miye na ka a ciki? Me ya shafe ka da har za ka juyawa mahaifin ka baya a kai na? Kasan me ya faru ne a tsakanin mu? Ko kuma na fad'a ma ka ba na son mahaifin ka ne? To maza kafin na k'irga uku ka kira mahaifin ka ka bashi hak'uri sannan ka nemi gafararsa." Da sauri ya d'auki wayar ya mayar da kira, Usman da ke cikin saka kaya ne ya ga kiran Bilal, d'auka ya yi kafin yace wani abu Bilal yace "Assalama alaikum, Abba ina wuni." Wani murmushi Usman ya saki tare da sak'awa a ran shi tabbas Khadija ce ta sashi ya kira shi, dan ya na da yak'ini akan Khadija wajen
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117