Chapter 36
Chapter 36
farin ciki ko karsashi, haka Bilal ya tafi makaranta Khadija kuma ta zauna kafin Uwani ta zo. Bayan Uwai ta zo yau Khadija ta ji bata buk'atar raini a wajen Haseenah, hakanne ya sa ta d'auko tsohuwar ajiyar gas d'in ta mai d'aukar tukunya d'aya ta sa Uwani ta d'ora silalar nama dan suyi na su girkin, su na cikin aikin kam sai ga Kaltume ta sallamo, da farin ciki Khadija ta tarbi k'awar ta, sun jima suna hira anan wajen kafin aikin ya yi nisa Khadija ta barwa Uwani ta k'arasa kula da shi, d'aki su ka koma suka dinga hira har Khadija ta tsegunta mata abinda ya faru daga zuwan amarya har zuwa jiya, nan Kaltume ta jinjina al'amarin kafin ta d'ora da "Kinsan me na ke so dake k'awata?" A raunane Khadija tace "Sai kin fad'a k'awata, wallahi kaina ya kulle." Gyara zama Kaltume ta yi tace "Da alama yarinyar da fitsara ta shigo, amma ki bita ta bayan gida, ki nuna mata na gaba ya yi gaba, na baya kuma sai tsinkaye, ki nuna ke ba wai shekaru ku ka yi tare da shi ba, ki nuna mata ke goggagiyace a fannin sanin mijinki, ki nuna mata na ku ba irin na su bane, sannan *wutsiyar rak'umi tayi nesa da k'asa*, kissa, k'awata yanzu kishi ma cikin kissa ake yin shi, kada ki kuskura ki bari yarinyar nan ta gane kina kishi da ita, bare harta fahimci kuna samun matsala da mijinki, k'awata abun ya na da wuya sosai, saboda ya na buk'atar k'arfin zuciya, amma ni nasan za ki iya, saboda kin jure fiye da wannan ma, yanzu ki fad'a min yaushe ne Usman zai dawo hannunki." "Na yarda Hajiata, amma ai ko ban fad'a mi ki ba ai kin sani" "Hakane kuma fa." Cewar Kaltume, matsowa ta yi ta rad'a mata abu a kunne, a tare suka bushe da dariya harda tafawa da hannu, Khadija ce tace "Banda mastala dake k'awata, nasan za ki gyara ni." Bayan fitar Usman kam gida ya nufa, ya samu mahaifinshi ma na shirin fita, saida ya duk'a k'asa ya gaishe su kafin ya zauna kan tabarmar da Hajia ke zaune, fita malam ya yi Usman ya bishi da "A dawo lafiya." "Allah ya sa." Ya fad'a fita, kallon Hajia ya yi yace "Su Nura har sun fita ne?" "Sun fita tun safe." Cewar Hajia, d'orawa ya yi da "Ba wani abu da ku ke buk'ata?" Ba tare da ta d'ago ba tace "Babu komai Fodio, Allah ya yi albarka." "Ameen Hajia." Shiru ne ya d'an ratsa kafin Hajia ta kalle shi da kyau tace "Jiya su Rabi'a sun zo nan su ke fad'a min wani abu da ban ji dad'in sa ba ko kad'an, sai dai kuma na yi mamaki da hakan ta faru a gidan ka, duba da tsayawarka akan iyalinka da kuma hak'urin ita Khadijar." Ajiyar zuciya ya sauke yace "Hakane Hajia, nima abun ya ban mamaki, sai dai koma miye ni nafi ganin laifin Haseenah, tun da Khadija ai ba yau mu ke tare ba, ko tsakani na da ita bamu tab'a samun matsalar da za ta saka mu d'agawa juna murya ba." "Toh, haka kai ka ke gani, amma yan uwanka ba haka su ke gani ba, sunfi ganin laifin Khadija." Murmushi ya yi yace "To Hajia koma me su ke gani ai wannan matsalar su ce, tun da dai ni ga yanda nake gani kuma na sani." "Hakane, Allah dai ya kyauta, amma dan Allah a saka ido sosai saboda gudun abin da zaije ya dawo." "Insha Allahu Hajia." Mik'ewa ya yi ya zura takalmin shi yace "Hajia ni zan wuce, amma anjima da dare zan dawo, dan mun kwana biyu bamu had'u da yan rigamar nawa ba (k'annan shi)." Daroya ta yi tace "Gaskiya kam, dan tuni ma su ka fara k'orafin amarya ta b'oye ka." "Na sani dama ayi hakan." Ya fad'a ya na dariya, har ya juya Hajia tace "Yawwa har na sha'ada ban fad'a ma ka ba." Juyowa ya yi ya dawo ya sunkuya, d'orawa ta yi da "Jiya matar *Issoufou* (d'an k'anin baban shi) ta haihu, an samu 'ya, idan ka samu dama sai ka je, su ma kuma matan sai ka fad'a mu su." "Ah masha Allah, insha Allah kam Hajia zanje, amma na yi mamaki da bai kira ni ba." "Watak'ila ya manta ne." "Ba shakka kam." Da haka ya bar gidan kuma ya na shiga mota ya kira Issoufou, take yace mi shi su had'u gidan yanzu zai je, haka ko akayi, ka zuwan nashi alkairi ne, domin kuwa kud'i ya bashi ma su yawa ayi hidima, bayan tafiyar shi kuma sai ya ya sa aka kawo mi shi kayan abinci, daga nan kuma makaranta ya wuce d'aukar Bilal. Suna ta hirar su cikin farin ciki sai ga Usman tare da Bilal, sannu da zuwa suka ma sa in da ya dinga tsokanar Kaltume su na wasa da dariya, da haka ya lek'a wajen Haseenah, ya samu ta na girki ba ta gama ba, dan haka ya fita yace sai ya dawo, saida ya dawo su ka yi sallama da Kaltume, sai dai mamaki ya kama shi ganin su na cin abinci har da Bilal ma, dan shigowar shi ya ga gas a waje da tukunya, sam bai kawo a ran shi abinci su ka girka ba, haka ya fita da tunani iri iri da kuma niyyar tsayar da wannan abun, dan ba zai yarda tun yanzu su raba mi shi kan gida ba ta hanyar raba abinci. _Ah to banga laifinka ba._π€·ββ *Luv u guy's* 24/01/2020 Γ 21:19 - πππ: ππππππππππ *KALLON KITSE* _(Ake wa rogo)_ ππππππππππ _SAMIRA HAROUNA_ *Littatafan marubuciyar* *1* _KAUSSAR_ *2* _D'AUKAR FANSA_ *3* _BA SO BANE_ *4* _AUREN HAD'I_ *5* _SANIN MASOYI_ *6* _JIHADI_ *7* _K'ANGIN RAYUWA_ *8* _ITACE K'ADDARARMU_ *9* _KAWU NA NE_ *10* _MAATA_ *11* _KALLON KITSE..._ *SADAUKARWA GA* _MATAN FARKO_π§πΌ *(UWAYEN GIDA)* πΈπ¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S* _(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_π€π€ ```Fatan alkairi masoya``` _Bismillahir rahamanir rahim_ _*ALLAH GATAN BAWA*_ *16* Farar miya Haseenah ta yi da shinkafa, ba wai miyar ba ta yi bane a wajen Usman, sai dai ji ya yi cin shinkafar ta gundure shi, kuma hakan baya rasa nasaba da sabon da Khadija ta mi shi na girka abinci kala kala, musamman da tasan ba ya san shinkafa sosai, sai ta yi wata d'aya ba ta girka ta ba, yanzun ma bai wani ci mai yawa ba ya bar shi, ko da ya yi wanka ya shirya falon Khadija ya shigo, Uwani na ganin haka ta mik'e ta fita, Bilal kuma dama ya na ciki ya na shiri, Kaltume kam ta na sallah la'asar ta wuce gida, zaune ya yi kalle ta ta na fad'in "Har ka fito?" "Um." Ya fad'a ya na sake kafe ta da ido, ita kam gyara gilashinta ta yi ta kalle shi tace "Ya dai? Da magana ne? Wannan kallon haka." K'asa ya kalla kafin ya kalle ta yace "D'azu da na shigo sai na ga kamar girki ku ka yi ko?" Ba tare da shakka ba tace "Eh, girki na yi, da matsala ne?" Gyara zama ya yi kamar zai had'e ta yace "Sosai ma,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117