Chapter 58
Chapter 58
abun bai wa iyayen dad'i ba haka su ka kwana suna jimami, shi ma da k'yar ya dawo gidan ya kwanta, sai dai ba wani bacci ya yi ba saboda Haseenah na nesa da shi, saida asuba da yaje ya tashi Bilal sun dawo daga masallaci ya ke ce ma Khadija "Kinsan yer uwar ki ba ta kwana gidan nan ba?" Da mamaki ta kalle shi tace "Subhanallah, me ya faru da ita? Ta na ina to?" Wani murmushin gefen labb'a ya yi yace "Kar ki damu, gari na k'arasa wayewa zanje na d'auko ta, Haseenah za ta zauna gidan nan kamar yanda ke ma ki ke zaune." K'ala ba tace ba har ya fita, da kan ta ta had'a mu su abin kari suka karya kafin ya fita, daga nan gida ya yi lokacin magana ta gama kewaye dangi Haseenah ta kwana gidan surukanta saboda ba ta son kwana gidan mijin, wannan kuma ba komai bane sai sharrin Khadija da ke son korarta a gidan. Ko da Usman ya je gidan ya samu iyayen Haseenah har sun zo suma, nan fa mahaifin ta ya nuna ba zai yarda a illata mi shi yarinya ba akan namiji, dab haka yace dole sai an kewaya Qur'ani a gidan, duk wanda ya cutar da wani to Qur'ani ne zai ci shi,😂 (tirk'sahi, Haseenah kin jawo bala'i), da k'yar mahaifin Usman ya rarrashe su ya basu hak'uri yace su bar komai a hannu shi zai d'auki mataki, saboda baya so cin zarafi ko mutumci ya fara shigowa lamarin, sun hak'ura amma sun ce dole a binciki gidan dan ga dukkan alama wani kafi ne a ciki da zai hana ta zama, sun yarda da hakan sosai dan haka ma suka ce zasu tura 'yan uwan Haseenah mata su je su duba. Hassana da Husseina aka kira suka zo gidan, nan aka fad'a mu su abin da ya faru da wanda zai faru a gaba, gidan Usman suka nufa tare da Haseenah da ta yi shiru ta kasa magana. Khadija na girkin rana a lokacin ta ga Mariya da kuma *Razina* sun shigo duk da ba ita ce aikin ba, cikin sakin fuska da mutumtawa suka gaisa sosai, ganin za su wuce ciki tace "Ina ga fa ba ta nan, ta fita ina jin." Mariya ce tace "Eh mun sani, ta na nan ma zuwa yanzu." "Ahan." Cewar Khadija ta ci gaba da aikin ta, ta na kusan gamawa kuma sai ga Haseenah tare da su Hassana, suma saida su ka gaisa kafin Khadija ta kalli Haseenah tace "Ke haka ake sai ku fita cikin dare babu wanda ya sani, saida safe ya ke fad'a min wai ba kya nan." Kamar za ta yi kuka tace "Ki yi hak'uri dan Allah." Ta na fad'a ta wuce falon ta. Kallon su Hassana ta yi tace "Ba ta da lafiya ne na ganta wani iri haka? Ko daga asibiti ku ke?" Cikin d'age kai Hassana tace "Lafiyar ta lau." Ta na fad'a ita ma ta yi gaba sai Huseeina da ta bi bayan ta, su na shiga Hassana ta zauna kusa da Haseenah ta dafa ta tace "Haseenah, ki fad'a mana gaskiyar abin da matar nan take mi ki kinji?" Girgiza kai ta yi tace "Ba komai." "Kin tabbatar?" Cewar Mariya da suka zagaye su, shiru ta yi sai Hassana ce ta kalle su dukan su tace "Ku na ji ko, gaskiya dole a d'auki matakin kare yarinyar nan kafin ta cutar da ita, kunga fa yanzu nuna mana ta yi kamar ba ta san me ke faruwa ba, har da tambayar ko ba ta da lafiya ne kuma daga asibiti mu ke, dan haka Haseenah sai kinyi taka tsantsan sosai." Husseina ce tace "Gaskiya wannan rashin tausayi da imani ya yi yawa, ace yarinya ko sati biyu ba ta cika ba amma ki na so ki fitar da ita daga gidan, wannan ai zalinci ne, shikenan fa so ta ke ta mayar da ita k'aramar bazawara." "Haseenah ki na da ciki ne?" Da sauri ta kalli Razina da ta jefo mata tambayar, cikin rashin sani tace "Ban sani ba ni ma." Hassana ce tace "To ko kin sani kar ki yarda ki bari ita ma ta sani, ko ki na ganin alamu kar ki bari ta gane tunda kinga ta fiki wayo, dan wallahi tasan da ciki jikin ki sai ta kusa kashe ki." Mariya ce tace "Kisa fa ki ka ce?" Cike da tabbatarwa tace "K'warai kuwa, ki na ganin ba ta iya wa ne? Wacce suka kwashe shekaru kullum da d'a k'waya d'aya, samun cikin Haseenah fa alama ce ta za ta fara hayayyafa gidan Usman, kinga kuwa dole a d'auki tsatsauran mataki." "To Allah ya raba mu da sharrin wannan mata mu dai." Cewar Razina. "Ameen." Su ka ji an amsa daga bakin k'ofa, wa za su gani in ba Khadija ba da kwanukan abinci tsaye, fik'i-fik'i su ka kama da ido cike da rashin gaskiya, cikin takon izza da isa ta k'araso in da suke ta aje kwanukan ta d'ago ta kalle su d'aya bayan d'aya, murmushi ta yi da ya k'ara mata kyau kafin tace "Ina rok'on Allah ya kare ku daga sharrin na kamar yanda ku ka yi fata, wani abu d'aya da na ke so ku gane shine, da ace ina kishi da Haseenah kuma haukan kishi, to wallahi tallahi da miji na bai ma kula ta ba bare har ta had'a kafad'a da ni, da ace za fitar da ita daga gidan nan bayan ma ta shigo wallahi da ba ma zan bari ta shigo ba, dan in ta shigo ai za ta iya yin alfahari da hakan, sannan za ta ga abin da yafi komai daraja a jikin miji na, za ta kwanta akan shinfid'a shi kamar yanda zan kwanta, to miye anfanin barin sai ta shigo sannan na fitar da ita? Ai ba ma za ta shigo ba wallahi da na so hakan, ku ji da kyau." Ta fad'a ta na kallon su dukan su, ci gaba ta yi da cewa "Idan na yi niyyar mallakar Usman ta hanyar asiri ku sani ina da kud'in da zan iya biyan boka ko da na k'asar india ne, idan har na tashi mallakar Usman wallahi zan mi shi mallakar da har mahaifiyar shi ba za ta anfane shi bane, idan mallakar Usman zan mallake shi cikin awa d'aya tak, kuma na hargitsa duk wani lissafi na shi, idan har na mallake shi to sai ya kai matakin da ko bayan gida zai zaga sai ya nemi izini na kafin yaje ga buk'atar shi, ku a matsayin ku na 'yan uwan shi wallahi sai ku zubar da hawaye kafin Allah ya had'a ku da shi akan hanyar har ku gaisa, dan haka ku daina kallo na a matsayin wacce ta mallake shi har take k'ok'arin fitar da wannan yarinyar, ba alfahari ba, amma zan iya cewa Haseenah ba ta kai macen da zan iya kishi da ita ba har na had'a ta da boka ko malam, ko ke ba ki kai matsayin ba." Ta fad'a da nuna Mariya da yatsa, gyara tsayuwa ta yi ta na murmushi tace "Wannan." Ta nuna labb'an ta da yatsa, "Da kuma wannan."
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117