Skip to content

Chapter 100

Chapter 100

Kallon Kitse Book One Complete Hausa Novels 1,200 words 0 views Progress saved
Download Book

ya na shafa bayan ta ya na fad'in "Kinji yanda zuciya ta kuwa ta buga lokacin da na ambaci kalmar takardar nan, dan Allah Khadija ki daina azabtar da ni haka, gaba d'aya kinsa na zama kamar mahaukaci saboda k'ok'arin ganin kin dawo gare ni, ki tausayawa uban yaran ki mana." Luf ta yi a k'irjin ta na share hawayen ta, sun jima a haka kafin yace "To ya ake ciki yanzu? Za ki koma ne ko ko sai na aiko mi ki da takardar har gida?" Wani naushi ta kai mi shi a ciki wanda ya sa shi bushewa da dariya ya dafe ciki, tashi ta yi zaune kafin ta kalle shi tace "A gaskiya ba zan iya binka ba a daren nan, kawai ka je gobe na dawo da kaina." Dariya ya yi ya kamo kunnen ta ya rad'a mata "Ashe yarinya ta na so na mata b'arin madara." Murmushi ta yi tace "Matsala ta da kai rashin kunya." "Um hakane, amma ai ke ki ka koya min." Tashi ya yi yace "Da gaske za ki dawo gobe?" "Zan dawo mana, ba ni na fad'a ba." "Idan ma ba ki dawo ba wannan karan su Hajia Kaltume da Turai zan aiko su d'auke ki su kai min ke." Kallon shi ta yi tace "Turai dai? Lallai." Tsaye ya mik'e yace "Yanzu kira min Bilal da shi zan tafi, dan nasan dole ma ki dawo idan na tafi da shi ai." Ita kam saboda ta yi niyyar komawa ya sa ta mik'e tace "Muje idan ka d'auke shi sai ka wuce." Tare suka fita daga d'akin su ka nufi d'akin Bilal, idon shi biyu ya na rik'e da wayar shi a hannu, nan ta canza mi shi kaya su ka tafi da niuyar za ta zo mi shi da sauran kayan, saida ya shiga d'akin Mama da ta jima da bacci ya tsokane ta yace ya tafiyar shi, idan ta damu da shi ta je ta yi bikon shi ita ma, saida ta rako su har k'ofar gida Bilal ya bud'e motar ya shiga, Usman na ganin haka ya damk'i Khadija da wata wawar sumbata da ta rikita su dukansu, da k'yar ya sarara mata kafin ya kalle ta da jajayen ido yace "Ki yi sauri ki zo da wuri, ina buk'atar ki kusa da ni Hajia ta." Motsa bakin da ta yi ya sa ya yi murmushi yace "Na ji dai idan kin kama ni ki yankanin amma fa bayan kin shayar da ni ruwan ki." Dungure mi shi kai ta yi tace "Wai kai ka manta da ka tsufa ne, watanni kad'an fa su ka rage ma ka ka cika shekara *arba'in da biyar* cif a duniya, amma ka na abu kamar wani tsohon bazawari." Saida ya sa hannu ya na shafar k'irjin ta yace "Kafin na cika hamsin da biyar kuma sai kun haifa min yara goma, kin ga ai ba na mayar da kai na tsoho ba, kuma ma ai ba daga nan abun yake ba, k'arfi da mazantakar na nan." Ya mata nuni da zuciyar shi. Da haka suka rabu ya tafi da Bilal, yau kam Khadija ta yi bacci cikin nutsuwa saboda burin ta ya cika, ta juya Usman son ran ta ta hakane ma har ta gano yanzun Haseenah ba ta da wani girma a idon shi, dan haka ta yi bacci da zumud'in gari ya waye ta fara shirin komawa. A wajen Usman kam Haseenah ba ta san da shigowar shi ba saboda har ta yi bacci ita ma, saida ya shinfid'e Bilal a gadon shi kafin ya wuce d'akin ta ba dan komai ba sai dan ganin halin da take ciki kamar yanda yake yi kullum, bud'a k'ofar da ya yi ne ya sa ta tashi ta na murza ido, kallon ta ya ke sosai ya na jin wata sha'awar na sake fizgar shi, sai dai kuma ba ya so ya neme ta saboda ba ita ta taso shi ba dama, da k'yar ya iya cewa "Ki yi hak'uri na tashe shi ko? Ashe hr kin kwanta ma, yau kam ban shigo da wuri ba." Gyara zama ta yi tace "Sannu da shigowa." "Yawwa sannu, ya ki ke?" Kallon shi kawai ta yi ba tace komai ba, juyawa ya yi zai fita yace "Saida safe ko, yau ma zan kwana a d'aki na saboda muna tare da yarima ne." Da mamaki tace "Yarima kuma?" Juyowa ya yi yace "Eh, Bilal ba." Wani haushi ne taji ya kamata, saukowa ta yi daga kan gadon tace "Kenan a gidan na su ka yi dare haka? Babban mutum ka na ganin abin da ka ke yi ya dace kenan? Wannan fa ba adalci bane, ka daina kula ni, ka daina min magana, ba ka cin abinci na, sannan ba ka kwana a d'aki na, me nai ma ka hakane da ka ke min irin wannan hukuncin? Ni ba wani abu bane a gare ni dan na durk'usa har k'asa na ba ka hak'uri, ka fad'a min dan Allah." Gyara tsayuwa ya yi ya na kallon ta, hak'ik'a komai gaskiya ta fad'a, sai dai baisan me zaice ba domin kuwa ba zai iya fad'a mata haka kawai ya ke jin tsanar ta ba, cikin taushin murya yace "Kinga ki yi hak'uri da duk abin da ke faruwa, kawai harkoki ne su ka d'anyi tsamari, amma insha Allahu komai ya kusan zuwa k'arshe, ki k'ara hak'uri kinji ko, saida safe." Ya fad'a ya juya kenan ta sake cewa "Shikenan ka je ka kwana da Bilal, dad'inta dai ba ya da abin da ni ke da shi, komai daren dad'ewa nasan dole ka neme ni a duk in da na ke." Juyowa ya yi ya kalle ta da mamaki yace "Da Bilal d'in za ki yi kishi? D'ana ne fa shi, kinsan mahimmancin shi a gare ni kuwa? To shi d'in kamar rayuwa ta ne, ina k'aunar sa fiye da komai, ki iya bakin ki in dai akan iyali na ne, ba na juran b'acin ran su ko kad'an." Idon ta cike da ruwa tace "Usman ba ka adalci wallahi, kullum nunawa ka ke Khadija da d'an ta sune rayuwar ka, kullum sune ma su mahimmanci a wajen ka amma ni ko oho, to kasan ba ka so na me ya sa ka aure ni?" Girgiza kai ya yi yace "Ni bance ba na son ki ba, sai dai abin da na sani kawai shine ina son iyali na, idan ki na son zama da ni ki so su kema, kuma kar ki d'auka Khadija kishiyar ki ce ki yi kishi da ita, maganar gaskiya ta wuce nan a wuri na, Bilal d'ana ne da ya fito daga jiki na tsatsona, amma ina wa mahaifiyar shi son da bana ma sa, kinsan me ya sa?" *Ita rayuwa dama haka take, da kin zauna da su lafiya da wannan ranar ba ta zo ba, kuskuren da mu mata keyi wani lokaci shine, ba ma fahimtar abin da mazajenmu suke so, idan har ki ka fahimci mijinki na bala'in son mahaifiyarsa ko yan uwansa ko yayansa, sai ke ma ki bishi ki nuna musu so na gaskiya, ba dan komai ba dan kawai ki faranta mi shi, hakan

Table of Contents

Chapters

117 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117