Chapter 75
Chapter 75
rab'awa ta yi da nufin shiga ban d'aki ya rik'o hannun ta ya nufi k'ofar fita da ita yace "Muke ki bata hak'uri, 'yan uwan ta ma na nan suna tsammanin jin hukunci daga gare ni, ba zan barki haka ba, amma da farko ki ba su hak'uri." Jin wani sabon rainin hankali ya sa Khadija fizgo hannun ta da k'arfi tace "In kuma ka ga haka ta faru to tabbas ba ta hanyar aure aka haife ni ba." Juyowa ya yi ya na kallon ta ita kuma ta gyara tsayuwa tace "Wallahi na rantse da sarkin daya busa min numafshi ko za ka kashe ni ba zan bawa uban kowa hak'uri ba, Usman." Ta kira sunan shi cikin d'aga murya ta d'ora da "Karfa ka yi tunanin sanin da ka min da, wallahi yanzu walkice ni daidai na ke da k'ugun ko wace shegiyyy..." Marin da ya zabga mata ne ya sa ta fad'i gefe har gilashin ta na fita daga idon ta, dafe kunci ta yi ta d'ago kai ta kalle shi, cikin fitar hayyaci ya shak'o wuyan rigar ta ya mik'ar da ita tsaye yace "Wuce muje na ce." Ba tate da tayi yunk'urin k'watar kan ta ba tace "Ba zan je ba wallahi, banga laifin da na yi ba da zan bawa wani hak'uri." Wani marin ya sake kifa mata da k'arfi da ya sa Bilal zabura ya tashi zaune, sake dafe kunci ta yi ta na kallon shi dishi-dishi, da hannu ya nuna mata k'ofa yace "Wuce muje." "Ba zan je ba." Ta fad'a ta na k'ok'arin tashi tsaye, a karo na uku ya sake gwab'a mata wani marin ya na fad'in "Ai kuwa za ki mutu kamar yanda ki ka ce, tunda taurin kai ne da ke." *Lovely sister kin tuna ko? Ki ci gaba da hak'uri komai zai wuce da ikon mai kowa mai komai.* Bilal na ganin haka ya sauko daga kan gado ya rik'e hannun mahaifin shi ya na hawaye yace "Abba dan Allah ka daina, ka bar dukan ta." Ture shi ya yi gefe d'aya ya na fad'in "Kai bar ni na nuna mata na fita taurin kai, zuciya ai ba ki fini ba." Ya k'arashe da kifa mata wani marin, a tak'aice saida Usman ya mata lafiyayyun mari har guda takwas a kumatu kamar ya samu jaka, da ta kasa tashi ne gashi ba ta iya jin komai ba ta ganin komai ya sa take zaune har yanzu k'asa, cikin hargagi ya ke fad'in "Wai ba za ki tashi ba?" Ya fad'a ya na zura k'afa ya na kai mata hanb'ara, Bilal ne ya rik'e shi ta baya ya na kuka sosai ya na fad'in ya k'yale mi shi Mummyn shi, Usman kam ido sun rufe rai ya b'ace bai ma san me yake yi ba sai harbinta ya ke da k'afa ya na had'awa da hannu ya na nausarta, da sauri Bilal ya zo ya rumgume ta ya juyo da kan shi ya kalli Usman yace "Abba na tsane ka, ba na son ka, ka fita ka ba mu wuri, Allah saiya sakawa Mummy na." Cak ya tsaya da hannun shi sama daga d'agawar da ya yi zai dake ta, duk da ya ji kalmar tsanar har k'asan zuciyar shi amma saiya basar ya nuna ta da yatsa yace "Yanzu hankalin ki ya kwanta da ki ka ji d'ana ya na fad'in ya tsane ni? To ki zuba ruwa k'asa kisha dan farin ciki, ni ma kuma Allah ne zai saka min da har ki ka yi sanadiyar da d'ana ya furta min kalmar tsana, munafuka kawai shed'aniya, kuma ki sani wallahi in har ki ka ce wannan halin za ki ci gaba da nunawa a gidan nan kenan, to ki na tare da wahala wallahi." Juyawa ya yi ya fita, d'auko gilashinta Bilal ya yi ya saka mata, mik'ewa ta yi ta shige ban d'aki ba dan tasan in da take saka k'afar ta ba, zaune ta yi bakin bahon wanka ta kunna ruwa suna zuba ta fashe da kuka, tabbas yau tabbatar da Usman baya hayyacin shi tunda har zai iya mata wannan dukan a gaban d'an su, mutumin da magana marar dad'i ba ta tab'a shiga tsakaninsu ba amma yau har da kiran ta munafuka, ta jima zaune ta ci kukan ta kafin ta mik'e ta wanke idon ta ta kashe ruwan ta fito, lokacin fuskar ta har ta kumbura kamar an hura balam-balam, jakunkunanta ta d'auko ta d'ura duk wani abun buk'atar ta a ciki Bilal na kallo, hijabi ta saka ta kalli Bilal tace "Bilal." Cikin muryar kuka yaron ya amsa da "Na'am Mummy." Cikin muryar da tasha kuka tace "Tafiya zanyi Bilal, ka zauna gidan mahaifin ka dan ba na jin zan iya dawowa gidan nan, amma ka sani ina tare da kai kaji ko." Da sauri ya taso yace "A'a Mummy, ni dai dan Allah ki tafi da ni, wallahi ba zan zauna nan ba, yanzu Abba ba ya so na, aunty amarya ma ba so na take yi ba, ni dai wallahi binki zanyi." "Bilal ba zan iya tafiya da kai ba, ba wai dan ba na so na tafi da kai d'in ba, sai dai nasan mahaifin ka ba zai bari ba, ka tuna ranar ma da zan tafi shi ya hana na tafi da kai? To ka yi hak'uri ka zauna kaji, idan ba ka jin dad'in zaman nan sai ka ce ya kai ka gidan su Hajia." Cikin kula yace "Ni dai ba na so Mummy, idan kuma ki ka tafi ki ka bar ni wallahi guduwa zanyi daga gidan nan." Cikin sanyin jiki tace "Shikenan je ka had'o kayan ka." Ya na fita ta zauna bakin gado ta zuba tagumi ta na fitar da wasu hawaye masu zafin gaske, ba wani jimawa Bilal ya dawo da k'atuwar jakar shi shima ya sanyo duk wani abun buk'atar shi, kallon shi ta yi tace "Ka d'auko kayan makarantar ka?" "Eh, suna ciki." Mik'ewa ta yi ta kashe duk wutar d'akin ta kile da makulli suka fita, a hankali cikin sand'a ta isa ga k'ofar da za ta shigo da mutum falonta da falonshi ta kulleta kafin suka fita ta d'aya k'ofar, nan ma rufewa ta yi kafin tace Bilal ya kira mai gadi k'ofar gida sannan ya tsayar mu su da adaidaita sahu, ba wahala kam mai gadi ya shigo har in da take ya tsaya yace "Mai adaidaitar na k'ofar gida Hajia." "Yawwa karb'i nan." Ta fad'a da bashi jakunkunan tace "Ka fitar mana da su muna zuwa yanzun." "To Hajia." Ya fad'a ya na d'aukar jakunkunan ya jasu Bilal ma ya ja tashi jakar, saida ta lek'o ta hangi motar Usman alamar ya na gidan, saida taga ficewar mai gadi kad'ai ta fito ita ma ta fita, har an yiwa kayan nasu wuri dan haka za ta shiga mai gadi yace "Hajia, lafiya dai ko? Ko tafiya za ku yi ne?" Juyowa ta yi ta kalle shi tace "Ka yi hak'uri Baba mai gadi, duk da dai abin da ya faru yanzun sirrine na gida na, amma kai ba yau muke tare ba, tunda na dawo sabon gidan nan na tarar da kai, tun Bilal na
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117