Chapter 12
Chapter 12
ya fad'i k'asa, tsaye ta mik'e tace "Me ye haka? Wannan wane irin iskanci ne? Wannan wani salon tuggun ku ne ko? To ka kiyaye ni wallahi, ni nan da ka ke gani na turmin tsakar gida ce." Hararan shi ta yi ta koma ta zauna cikin tsawa tace "B'ace min da gani malam." Tashi ya yi ya gyara jikin shi yace "Ki yi hak'uri aunty, dama zan gaishe ki ne kamar yanda na ke gaishe da Ammie na." Tsaki ta yi ta harare shi sama da k'asa ta d'auke kai, wucewa ya yi ya koma wajen maman shi ya zauna kujerar da ita ce kujerar zaman shi dama, ta fara zuba mi shi a faranti kuma Usman ya shigo, daga in da Khadija ke tsaye ta sakar masa murmushi, shi ma mayar mata ya yi tare da nufa wajen su, Haseenah da kallon mamaki ta bishi, aje ledar hannun shi ya yi akan teburin ya sumbaci kumatun Dije yace "Sarauniya ta tashi lafiya?" Karo na farko da Dije ta ji kunyar abin da ya yi gaban mutane, cike da kunya tace "Ina kwana babban mutum." Kallon kwanukan ya yi yace "Ashe kin mana abin kari?" Murmushi ta yi tace "Jiya ma ai gajiya ce ta hana." Juyowa ya yi ya kalli Haseenah da ta daina kallon su dan bak'in ciki yace "Haseenah." Ba tare da ta juyo ba tace "Na'am." "Ki zo ga tuwan ki." Mik'ewa ta yi ta juya ta kalle shi tace "Ya ma fita a rai na wallahi, kawai ka bar shi." Za ta nufi k'ofar da za ta sada ta da d'akin ta ya yi saurin tare gaban ta ya kamo hannun ta ya nufi wajen teburin da ita ya na fad'in "Idan ba za ki ci tuwon ba ai ga sarauniya ta dafa mana wani abun, kuma zaiyi wuya ki ce ba za ki so shi ba, dan na yarda da girkin mata ta." Khadija da ke kallon hannun shi dake cikin na Haseenah wani nauyayyen abu ta had'e a mak'oshin ta, yayin da ita kan ta Haseenah taji kamar ta fasa ihu, haka ta zuba abincin ta zauna ita ma, sakin baki Haseenah ta yi ganin Bilal ya haye k'afafun Usman ya sa hannu a farantin da ke gaban Usman d'in, haka ma Khadija ita ma ta saka na ta hannun a ciki, kallon ta Usman ya yi da dariya yace "Ki saka hannun ki mana, haka mu ke cin abinci anan." A hankali ta zura hannu duk sai ta ji kan ta kamar bak'uwa a gidan, kamar ba gidan mijin ta ba haka ta ji kan ta, dan haka ma bata wani ci mai yawa ba sai kallon shiriritar su ta ke, haka aka gama kuma ya tashi ya tafi kai Bilal makarantar islamiyya, tun da ta shiga d'aki ta d'auki wayar ta, yanar gizo ta shiga manhajar WhatsApp, sak'onni ta samu masu yawa daga mutane da k'awaye, ta yi sa'ar samun k'awar ta Zeinab ta na kai ita, bayan sun gaisa ta tambaye ta ya amarci ne ta ke fad'a mata wai da matsala, duk abin da ya faru ta kwashe ta fad'a mata, shawarar da ta ba ta ita ce ta saki jikin ta ita ma yar gida ce aure ta ke, sannan ta canza wannan tsarin na cin abinci, dan ba zai yiwu ace ko ranar girkin ta sai dai aci tare duka ba, da irin haka su ka jima su na hira kafin Usman ya dawo ta taya shi ya shirya zai fita, jikka biyar (jaka biyar) ya bata kud'in girki duk da babu abin da za ta nema ta rasa a madafa, amma sanin akwai abin da za ta iya nema ya bata su, sallama ya mata kafin ya wuce d'akin Khadija, ya d'an d'auki lokaci kafin ya fito ya fita. *11:00* daidai na rana Haseenah ta fito dan fara girkin rana, kamar yanda Usman ya fad'a mata cewa duk abin da ta ke buk'ata ko za ta yi ta nemi taimakon Khadija ko ta tambaye ta, kai tsaye falon Khadija ta shiga, ganin ta zaune ya sa ta yi sallama ciki ciki kamar an sata dole, da fara'a Khadija ta amsa ta na fad'in "Amarya kin fito?" Wani shegen murmushi ta yi tace "Um." D'orawa ta yi da "Dama zan fara girki ne, kuma yace na tambaye ki idan ina neman wani abu." Cikin sakin fuska Khadija tace "Ayyah, kar ki damu kan ki, ga Uwani sai ku je tare ta taimaka mi ki." Da sauri tace "A'a, ba na buk'ata, nagode, kawai ki fad'a min in da zan samu kayan, dan yace akwai duk abun buk'ata." Cike da iko ta kalle ta tace "Hakane, kije to su na madafar." A gadarance tace "Madafar a ina?" Murmushin gefen labb'a ta yi ta mik'e tace "Muje na nuna mi ki." Bin bayan Khadija ta yi har madafar, k'atuwar frigi (fridge) ta bud'a ta nuna mata tace " Za ki iya samun duk naman da ki ke so." Haka ta nuna mata komai ta fice, ita kuma d'akin ta ta koma ta dauk'o wasu daga cikin kayan miyar da aka had'o ta da su, cire hijabi ta yi ta dauk'o naman zabbi dan wankewa ta fara aikin, ta yi k'ok'ari sosai wajen yin abin da ba ta saba yi ba, sai da ta ga miyar ta ta kusa kammala kad'ai ta d'ora ruwan silalar macca, d'akin Khadija ta je ta tambaye ta adadin wacce za ta dafa? Cike da sakin fuska tace " Eh to, za ki iya saka leda biyu, idan kinsan ba za ki yi bak'i ba." Biyu ta saka kamar yanda ta fad'a mata, sai dai kuma a maimakon ya zo gida cin abinci sai ya kirata wai ta fidda mi shi abinci mai yawa zai aiko a d'aukar ma sa, gashi Aziza ta zo tare da k'awar ta, ga kuma wasu daga cikin dangi su na zuwa, ga kuma k'annan ta su uku sun zo, ga kuma mutanen gida. *Za mu ga idan ki na da wayo ai.*π€ͺ 08/01/2020 Γ 17:09 - πππ: ππππππππππ *KALLON KITSE* _(Ake wa rogo)_ ππππππππππ _SAMIRA HAROUNA_ *Littatafan marubuciyar* *1* _KAUSSAR_ *2* _D'AUKAR FANSA_ *3* _BA SO BANE_ *4* _AUREN HAD'I_ *5* _SANIN MASOYI_ *6* _JIHADI_ *7* _K'ANGIN RAYUWA_ *8* _ITACE K'ADDARARMU_ *9* _KAWU NA NE_ *10* _MAATA_ *11* _KALLON KITSE..._ *SADAUKARWA GA* _MATAN FARKO_π§πΌ *(UWAYEN GIDA)* πΈπ¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S* _(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_π€π€ ```Fatan alkairi masoya``` _Bismillahir rahamanir rahim_ *8* Jin ba za ta iya d'ora wata tukunyar ba ya sa ta aiki Bilal d'an unguwar ya siyo mata bredi mai yawa, maccar da ta dafa sai ta juye wa mijin ta, bredi kuma ta had'a Khadija da shi tace ta rarraba, da mamaki Khadija tace "Amma Haseenah da ba ta isa ba aida wata ki ka d'ora, tun da akwai sauran lokaci bare ace a matse ake." Shiru ta yi ta ba tanka ta ba, haka ta raba miyar wa sauran mutanen da ke wurin, ficewa ta yi daga madafar in da Aziza ta bita da harara, tab'e baki ta yi tace "Kiji wani iyayi kuma, ko ina ruwan ta da abin da ki ka ga damar yi, sai ka ce ke ba
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117