Chapter 106
Chapter 106
da ni." Hannu suka saka tare, kafin ta kai loma bakin ta tace "Wai ina Haseenah ne? Ba za ta fito cin abincin ba?" Jim ya d'anyi kafin yace "Bata nan." Ba tare da damuwa ba tace "Ok, ko ta tafi asibiti ne awo?" Shiru ya yi kamar ba zai amsa ba sai kuma yace "Ta na gidan su." Kallon shi ta yi tace "Gidan su kuma? Lafiya dai ko?" Cike da jin an takura shi yace "Kai Khadija, ta na gidan su na ce mana, sakin ta na yi." Dam, taji gaban ta ya fad'i, tabbas tasan ba su yi zaman lafiya da Haseenah ba, kuma ta na kishinta sosai ta na kuma ji haushin irin cutar da ta mata, amma hakan ba shi zaisa ta yi farin ciki da mutuwar auren ta ba, abu d'aya da ta sani shine ita ma mace ce kamar ita, tasan dole wannan kalmar ta girgiza tunanin ta, abun duba kuma anan shine cikin da ke jikin ta, in har za ta iya fad'an gaskiya to duk abin da ta yi ya kamata ace an mata uzuri, dan ko ita ce ba ta san irin damuwar da za ta shiga ba idan aka ce haka ta faru da ita, bare Haseenah da ko wata takwas ba ta yi ba a gidan miji amma ace an sake ta da cikin fari a jiki, a hankali ta kalle shi tace "Amma Abban Bilal zan iya cewa wani abu?" Ba tare da ya kalle ta ba yace "In dai akan wannan yarinyar ce ba buk'ata, hukunci ne kuma na yanke, zan kula da komai daga yanzu har lokacin da za ta haihu, idan ta haihu kuma ta gama shayar da abin da ta haifa zan d'auko shi na dawo da shi kusa da ni, nasan banda matsala wajen samun wanda zai rik'e shi, ko ke za ki yi min wannan karamcin." Wani mamakin ne ya sake bayyana a fuskar ta ta na kallon shi, ganin haka ya sa ya mik'e yace "Ni zan fita waje, idan kin gama ki same ni saina aje ki asibiti." Da kallo kawai ta bishi har ya fita, ji ta yi abincin ya fita a ran ta ita ma sai kawai ta tattara ta shiga da shi madafa, juyewa ta yi a kwano ta fito da shi ta bawa Rabe, godiya ya mata kafin ta samu Usman suka wuce, babu mai magana har suka isa asibiti ya aje ta a bakin k'ofar, saida ta fito ta rufe k'ofar ta kalle shi tace "Allah ya kiyaye hanya, sai ka dawo." Kallon ta ya yi yace "Ameen, Allah ya sa." Da haka ta shiga ciki shi la ya wuce, sosai ta yi farin cikin ganin Bilal a zaune ya na shan koko mai d'umi, godiya ta yi ga Allah da ya sa yaron ta ya rayu kula har za ka iya cewa ma jikin shi da sauk'i fiy da jiya da ba za ka ce ya na raye ba, sai dai fatan Allah ya k'ara mi shi lafiya mai anfani. Haka su ka ci gaba da jinyar Bilal cike da kulawa, in da aka d'auke shi daga gidan gaggawa aka mayar da shi cikin asibitin, kullum 'yan uwa su na zirganiya a hanyar asibiti ganin Bilal, Khadija kuma da Usee suna farin ciki idan suka koma gida, har yanzu ba ta sake mi shi maganar Haseenah ba amma abun na damunta sosai, kullum tana auna hakan da kanta ta na ganin idan ita ce ya za ta yi? Ta na so ta sake mi shi magana amma da ta yi magana da Hajia sai tace kawai ta share ta kar ma tasa ran shi ya b'ace akan wata, shi ya sa ta d'anyi shiru amma ba wai ta hak'ura bane, dan abin da take tunani ba kowa bane ke tunanin shi, a haka suka kwashe *sati d'aya* a asibiti. *Kwana goma sha d'aya* aka sallami Bilal saboda jikin shi ya yi sauk'i sosai cikin hukuncin ubangiji, a lokacin kuma Haseenah rayuwa ta fara gara ta yanda take so... *Allah ka sa mu dace.* 13/03/2020 Γ 14:14 - πππ: ππππππππππ *KALLON KITSE* _(Ake wa rogo)_ ππππππππππ _SAMIRA HAROUNA_ *Litattafan marubuciyar* *1* _KAUSSAR_ *2* _D'AUKAR FANSA_ *3* _BA SO BANE_ *4* _AUREN HAD'I_ *5* _SANIN MASOYI_ *6* _JIHADI_ *7* _K'ANGIN RAYUWA_ *8* _ITACE K'ADDARARMU_ *9* _KAWU NA NE_ *10* _MAATA_ *11* _KALLON KITSE..._ *SADAUKARWA GA* _MATAN FARKO_ π§πΌ *(UWAYEN GIDA)* πΈπ¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S* _(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_π€π€ ```Fatan alkairi masoya``` _Bismillahir rahamanir rahim_ *39* Sabo da jar miya da cin abin da rai ke so ya sa Haseenah ba ta iya cin abincin gidan su, da yake ta na da 'yan kud'in da ta samu hannun Usman sai take anfani da su wajen siyan abin da take so, sannu-sannu kuma sai k'annan ta suka fara d'ora mata raini ta yanda ko aikensu ta yi ba sa zuwa, da k'yar wani lokacin za ta basu kud'i su tafi, wani lokacin kuma sai dai ta tafi da kanta ta siyo dan abu mai galmi da yaji, gaba d'aya a takure take jin kanta a zaman gidan nan, d'akin da suke kwana ita da k'annan su ga zafi ga rashin sarari, yau dai data tashi ta d'auko jakar yan kud'in ta da nufin siyo abin kari sai kud'i suka ce nemi in da ki ka aje, nan ta yi haukan nema amma ba ta gani ba, ta tambaya maman ta kuma tace to ita ina za ta sani, kuma ba kowa gidan sai su duk sauran su na makaranta, dole d'umamen tuwon da aka yi shi ta dank'ara tasha ruwa, ruwa ta kai ta d'auki kwandon sabulu dan yin wanka, amma sabulun sai kad'an ya rage wanda ba zai mata komai ba, cikin jin haushi ta kalli maman ta tace "Mama, wai yanzu shi ma sabulun da na saka saida wani ya d'auka?" Cikin sanyin hali tsohuwar tace "To Haseenah ba sai ki yi hak'uri ba, da kina gidan ki nan kowa ke wadace da sabulun, sun d'an saba ne da wanka da mai k'amshin shi ya sa da su ka ga naki su ka d'auke." "To amma Mama ni fa kad'an ne na taho da shi sabulun, yanzu haka ina ga bai wuce uku ba wanda ya yi saura, idan ya k'are sai mu yi ya kenan?" Duk ta yi maganar ne kamar za ta fashe da kuka, a tak'aice tace "Sai ku taru ku hak'ura." Tsaki ta yi ta shiga d'aki ta d'auko wani ta saka ta shiga ban d'akin, wanka ta yi ta fito ta shirya cikin doguwar riga, tsakar gidan ta fito ta d'auki waya da nufin shiga yanar gizo, sai dai ina babu sadarwar ta k'are kuma babu kud'i a wayar, kallon ta maman ta tayi tace "Haseenah, wai har yanzu mijin ki bai kira ba?" Cikin takaici tace "Mama bai kira ba, dama ai ba kira na zaiyi ba." "Kuma ke ba ki tab'a jaraba kiran shi ba ko?" Kallon maman ta tayi tace "Mama taya ni zan kira shi, ai ba d'auka zaiyi ba." Shiru kawai tsohuwar ta yi sai Haseenah da ta shiga duniyar tunani, sai lokacin ma ta tuna da waccen ranar da ya sake
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117