Chapter 35
Chapter 35
mana, me ka gani?" "Ka fad'a masa gaskiya, ka ce wajen amaryarka za ka koma, ba na so ka fara sawa yarona wani tunani na daban." Khadija ce ta yi maganar fuska a had'e, juyawa ta yi ta fita daga d'akin, kallon Bilal ya yi yace "Ka kwanta kaji ko, banda tambaya akan abin da bai shafe ka." "Ka yi hak'uri Abba." Ya fad'a ya na k'ara jan zanin rufarsa. Ya na shiga ya samu Khadija har ta cire rigar ta za ta shiga ta watsa ruwa, ta na ganin shi ta sa kai za ta wuce ban d'akin, da sauri ya rik'ota ta fad'a jikin shi ya na kallon fuskar ta yace "Me ye haka wai? Me ya ke damunki ne?" Da k'arfi ta ture shi daga jikinta ta na fad'in "Dallah ni rabu da ni, ka koma wajen amaryarka mana, nasan ai ta na can ta na jiranka, me ka zo yi mana anan? Saida safe? To mun gode Allah tashe mu lafiya." Ta na fad'a ta juya dan shiga ban d'akin ya sake rik'o ta, had'e fuska ya yi yace "Haseenah ta aiko mu ku da abinci, amma ba ku ci ba kin bawa mai gadi, ko me ya sa?" Cikin k'unar zuci da wani zafi da ke cikin zuciya tace "Eh, ba zan ci ba, kuma d'ana ma ba zai ci ba, sannan ka fad'a mata karta sake aiko min da abinci dan ba zan ci ba, tun da ai bata ga yunwa a tare da mu ba." Cike da mamaki yace "Khadijaaa, me ya sa ba za ki ci ba?" Rik'e k'ugu ta yi tace "Kai me ya sa ka daina cin abinci tare da mu? Ita ce ta buk'aci hakan ko? To ya yi kyau, amma ka sani ni ba sakarya bace da za'a rainawa hankali, kai da ita ku ci na ku tare, ni da d'ana kuma ta ware mana na mu, ma'ana mu kad'ai ne ake son bala'in ya samemu, to ba zai yiwu ba wallahi, abincinta har abada ba zan ci ba." A hankali ya zauna bakin gadonta dafe da kanshi ya kalle ta yace "Khadija a haka ki ka fahimci abun? Haba dan Allah, me ya sa ki ke haka? Karfa ina yabonki sallah kuma alwala ta gagare ki." "Sai me?" Ta fad'a har da hararan shi, zunbur ya mik'e ya had'a da jikinshi da k'arfi ya had'e ta da bango ya na kallon k'wayar idonta, k'asa tayi da idon dan haka yace "Kalle ni nan." Kallon shi ta yi kai tsaye kuma ta sake k'asa da idon ta, cikin daka tsawa yace "Kalle ni nan nace." A hankali ta d'ago ta kalle shi, hawayen da suka taho mata ne yasa shi cire mata gilashinta ya wurgar da shi akan gado, duk da ta na ganinshi tsaye a gabanta, amma ba ta iya ganin shi da kyau, sassauta murya ya yi yace "Khadija, tun da muke da ke kin tab'a ko da hararan baya na bare kuma gaba na?" Girgiza kai ta yi alamar a'a, k'ara tausasa murya ya yi yace "To me ya sa zuwan Haseenah gidan nan zai zama sanadin da raini zai shiga tsakanina da ke?" Shiru ta yi sai hawayen da suka sake bulbulo mata, ganin shirun ya sa yace "Me ya sa idan dare ya yi b'acin ranki ke nunkuwa ne? Wani abu na ke mi ki da ba kya so?" Da k'arfi tace "Eh, dubi can." Ta fad'a da nuna mi shi makeken gadonta da yatsa, kallo ya yi ita kuma tace "Na yi rashinka akan shinfid'a ta Abban Bilal, kwana hud'u ne kawai mu ka yi nesa da juna, amma jinsu nake tamkar shekara hud'u ne, Abban Bilal na..." Had'e bakin shi ya yi da nata, dan gaskiyar magana akan abin da take magana baida kalaman da zai iya tausarta da su, tun da bai isa yace bai kusanci Haseenah ba, bai kuma isa yace ba zai k'ara ba, kamar yanda ba zai iya cewa ya datse kwanan Haseenahr ba, tsayuwar ce ya ji ta gagare shi hakan ya sa ya gangara zai kwantar da ita, da k'arfi ta ture shi daga jikin ta ta kalle shi tace "Kar ka sake had'a jikinka da nawa, ba na buk'atar ka." Ban d'aki ta nufa tana goge bakin ta, shi kam fad'awa ya yi akan gado ido lumshe, ya yi iya k'ok'arin shi wajen gayyato nutsuwar shi amma ya kasa, haka ya mik'e ya fita daga d'akin amma har zuciyar shi ya na sha'awar kasancewa da Khadija, dan ita kad'ai ce ta iyashi yanda take samar mi shi da nutsuwa, ta na jin fitar shi ta fito ta zura farar doguwar riga mai kauri ta kwanta, kuka sai da ta ci ta k'oshi har ta godewa Allah, a k'arshe dai mik'ewa ta yi ta d'auki Qur'ani ta fara karatu, cikin k'ank'anin lokaci sai zuciyarta ta washe ta yi wasai da ita babu ko d'igon damuwa a tare da ita. Usman kam na shiga dama a rikice ya ke, har d'aki ya samu Haseenah ta shirya cikin arniyar rigar bacci, ta na jin an bud'a k'ofa ta juya, amma abin da ya fito shine ya d'auki hankalinta, a tsaye ya ke k'yam abun har ya bata tsoro saboda ba ta tab'a ganin irin haka ba a rayuwarta, kafin ta ankara ya cakumota jikin shi ya manne bakinta da na shi ha haura da ita kan gado, dama dai rigar wata d'ogal ce, dan haka baisha wahalar cire ta ba, ya na shirin kaiwa ga gaci Haseenah ta dakatar da shi ta hanyar sauka daga kan gadon, kallonta ya yi a raunane yace "L...afi..y.a?" Kayan ta ta bud'a ta d'auko riga ta zura, da sauri ya sauko daga kan gadon ya rumgumota ya sumbatar wuyanta, dan ba zai iya magana ba, d'an ture shi ta yi taja baya ta na kallon shi tace "Ka je kawai ka kwanta ka yi bacci." Kamar wanda ya sha kuka haka idon shi su ka yi jawur, girgiza mata kai ya yi da k'yar ya had'a kalmar "B...ba ...zan iya ba." Ba tare da shakka ko tunani ba tace "To ka je wajen wacce ta d'ora ka sai ta sauke ka." Banza ya yi da ita ya kumo janyota jikin shi, ture shi ta kuma yi ta kalli idon shi tace "Wallahi kaji na rantse ko ba za ka samu abin da ka ke so ba, a gaskiya ba zan iya d'aukar wannan wulak'ancin ba, haka kawai ranar kwana na amma kaje wajen wata har ka bari ta ribace ka, shine sai ka dawo min kamar kasha wani abu, to ba zai yiwu ba gaskiya." Ta na fad'a ta kwanta kan gadon ta ja zani ta rufa, kan gadon ya haura ya dinga shafarta ya na rarrashi, amma ko kallo bai isheta ba bare ta kalli idonshi ta tausayawa halin da yake ciki, duk da ranshi ya b'ace haka ya danne ya rumgume ta har baccin wahala marar dad'i ya d'auke shi. 😂😂😂 *Surukin sis Chappa fa yau ba kanta* Washe gari da safe haka Khadija ta gaggauta had'a sassauk'an abin karyawa, Haseenah ma haka shayi kawai ta had'a da k'wai sannan ta yi wanka, a tak'aice dai safiyar babu mai
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117