Skip to content

Chapter 60

Chapter 60

Kallon Kitse Book One Complete Hausa Novels 1,196 words 0 views Progress saved
Download Book

had'e, bud'e ido ya yi ya sauke akan Khadija da ke shirin kai loma a bakin ta, shiru ya yi ya na kallon kowa har suka kai bakin su suma, kasa had'ewa su ka yi suka furzar dan haka Khadija ta d'ago ta kalli Haseenah, murmushi ta mata cike da makirci tace "Ramawa ki ka yi kenan?" Zazzare ido Haseenah ta yi ta kalli Usman da ya kafe ta da ido ya na kallo, cikin in'i'na tace "... *Maganin biri karen maguzawa, waya fad'a mi ki barno gabas take.* 12/02/2020 Γ  21:57 - πŸ’‹πŸ˜˜πŸ’‹: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘ *KALLON KITSE* _(Ake wa rogo)_ πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘ _SAMIRA HAROUNA_ *Litattafan marubuciyar* *1* _KAUSSAR_ *2* _D'AUKAR FANSA_ *3* _BA SO BANE_ *4* _AUREN HAD'I_ *5* _SANIN MASOYI_ *6* _JIHADI_ *7* _K'ANGIN RAYUWA_ *8* _ITACE K'ADDARARMU_ *9* _KAWU NA NE_ *10* _MAATA_ *11* _KALLON KITSE..._ *SADAUKARWA GA* _MATAN FARKO_ πŸ§•πŸΌ *(UWAYEN GIDA)* πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S* _(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€› ```Fatan alkairi masoya``` _Bismillahir rahamanir rahim_ *23* "Wallahi ba ni bace, babu abin da na saka a abincin nan." Had'e fuska Khadija ta yi tace "Kinga Haseenah, ni da ke yanzu duk d'aya ne, tunda kin rama to komai ya wuce, kin fahimta." Cikin b'acin rai Usman yace "Yanzu miye haka? Me ku ke son mayar da ni to? Ke koma miye ai laifin ki ne tunda ke ki ka fara, ki na babba amma ko tsaya d'aukar raini ga k'aramar k'anwar ki, mtssss." Tsaye ta mik'e ta na kallon shi tace "Dakata Abban Bilal, ni nafi k'arfin na tsaya jawa kai na raini wajen wannan mutsitsiyar yarinyar, gata ka tambaye ta tsakani da Allah uban waye ya fara zuba gishiri ko sugar a abinci? Ita ce da kan ta, har ni za ta wa makirci, saboda ta baka ka kurb'a shine za ta dinga ja min magana a wajen ka ta hanyar lalata abincin da ta girka, me ta ke nufi da hakan? Tasan dole ni za'a zarga dama ba ita ba, shine ni ma na nuna mata mace ce ni kuma gaba na ke da ita ko a haihuwa." Zata fice ya mik'e tsaye yace "Dawo nan." Dawowa ta yi ta tsaya sai Haseenah da ta mik'e ta kalle shi tace "Wallahi k'arya ta ke min babu abin da na saka, kawai sharri ne ta ke so ta ja min, taya ma zan lalata abin da na girka da hannu na?" Kusanta Khadija ta matso cikin b'acin rai ta nuna ta da hannu tace "Wallahi ki ka sake cewa ina mi ki k'arya sai na fitar mi ki da jini a baki, marar kunya kawai fitsararriya, ke har ni za ki kalla ki ce ina mi ki k'arya? Wace ce ke dan Allah da zan mi ki k'arya?" Usman ma matsowa ya yi yace "Ta fad'a d'in k'arya ne, ko k'aryar ta mi ki ne ba ki aikata ba? To gata nan ki fitar mata jinin dan Allah, wallahi da na gaggauta d'aukar mataki a kan ki, kiji mace kai ki yi laifi kuma ki ce ba za'a mi ki magana ba, ke wace ce?" Cikin tafasar zuci ta kalle shi tace "Ni ce ma macen? To ta mace maka k'ofar d'aki, kuma na fad'a wallahi ta sake cewa na mata k'arya sai na kife ta da mari kuma a gaban ka." Ai fa abu ya yi k'amari, sai kawai Usman ya jawo Haseenah da k'arfi ya dawo da ita gaban Khadija yace "Ke fad'a mata ta yi k'arya na ga me za ta yi, kiji iskanci kai ki yi laifi kuma ki ce ba za'a mi ki magana ba, wacece ke da ki ka fi k'arfin a mi ki magana?" Idon ta ne suka rufe ta kalli Haseenah tace "Ki fad'a idan ke yar halak ce." Haseenah ta tabbatar babu abin da zai hana Khadija ta dake ta, dan haka ta koma gefen Usman ta na fad'in "Abban Bilal kaga, ni fa ba na son matsala, laifi ne ta aika ta kuma na yafe, dan haka kawai abar..." Ba ta k'arasa maganar ba Khadija ta kife ta da mari, cikin hargagi ta shak'o wuyan ta tana fad'in "Wa ki ka yafewa? Ni wai ki ke cewa kin yafe wa? To bari ki gani idan na ci uban ki gobe ko kud'i aka baki ba za ki sake shiga harka ta ba." Tuni Khadija ta yi fatali da ita a k'asa warwas, sosai ta shak'e wuyanta ta na jijjigata ta na fad'in "Za ki sake shiga harka ta, daga yau za ki sake rai na ni?" Duk abin nan da ake Usman na ta k'ok'arin raba su amma Khadija ta rik'e ta sosai, saida ya sa k'arfi sosai ya rumgumo Khadija ya d'aga ta daga jikin Haseenah, jefar da ita ya yi gefe in da ya kaiwa Haseenah d'auki ya kamota ta tashi, kallonta ya ke duk ta fita hayyacinta ido sunyi waje saboda wahala, ganin haka ne ya sa Usman juyowa cikin b'acin rai ya kashe Khadija da mari, gilashin ta ne ya k'arasa fita ya fad'i, dafe kunci ta yi ta d'ago ta kalle shi, cikin tsananin hushi ya nuna ta da hannu yace "Wallahi yau sai kin tafi gidan ku, ba zan d'auki wannan iskancin ba, haka kawai saboda kifi yarinya k'arfi sai ki dinga mata cin kashin da ki ka ga dama, to ba zai yiwu ba, kawai kije gida sai na nemi ki." Za ta yi magana Bilal ya sakaya hannun shi ta k'ugun ta ya na kallon Usman da ke rarrashin Haseenah ya nufi d'akin shi da ita, Bilal kam hannun ta ya kama yace "Mummy ki zo mu tafi, mu tafi gidan su Hajia kawai." Sunkuyawa ya yi ya d'auko mata gilashin ta ya d'aga hannayen shi da nufin saka mata, b'acin rai ne ya saka ta fizgar gilashin ta karya shi gida biyu ta jefar, hanya ta kama da nufin komawa d'akin ta amma sai ta yi karo da kujera, hannun ta Bilal ya kama bai saki ba har saida ya kai ta d'akin ta, su na Bilal ya sake d'auko mata wani gilashin ya saka mata kafin yace "Mummy, meya sa Abba ya daina son ki yanzu?" Kallon shi kawai ta yi ta mik'e ta d'auko akwatin ta ta zuba kaya, d'akin Bilal ta koma can ma ta had'o mi shi kayan shi kafin ta saka mayafi ta d'auki jakunkunan suka nufi k'ofar fita, a lokacin Haseenah ma sai kuka take ita wallahi gidan su za ta tafi kafin Khadija ta kashe ta, hakan ya sa lokacin da suka iso falon shi suka hangi Khadija da Bilal za su fita, da hanzari ya fito ya tare ta yace "Bilal d'ana ne, kuma ba da shi ki ka zo gidan nan ba, dan haka ki bar min yaro na." Fuska a had'e tace "Ni ma zan tafi da shi ne saboda ko da na zo gidan tare na same ku." Duk ya gane magana ce ta fad'a mi shi amma haka ya fizgo Bilal yace "Yana nan tare da ni, idan kuma da wanda ya isa ki aiko shi ya k'watar mi ki shi na gani." Tab'e baki ta yi tace "Hum! Wa ma zan aiko ya k'watar min shi? Ai sai marar kunya irin

Table of Contents

Chapters

117 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117