Chapter 16
Chapter 16
ku panke) saida ta bi duka yan uwanta biyar ta saka mu su a baki kafin k'awar ta *Kaltume* da *Salamatu*, haka aka gama shagali aka yi murna sosai aka watse. *Komai na da mafari a rayuwa*, matar Ashir da Bashir da mama sun gama waina, sai dai babu mai kaiwa, Habib kad'ai ke gari kuma shi ma ya na wajen d'aurin auren abokin shi a wani k'auye *Dak'oro*, hakan ne ya tilasta mama cewa Khadija ta shirya sai ta kai a kan moton ta, shiryawa ta yi tare da Kaltume da su ke kusa da juna suka tafi, Kaltume ita ke rik'e da kwanukan abincin a baya, sun isa lafiya su ka kai abincin, cikin ladabi su ka gaishe da dattawan, da kansu su ka wanke babban faranti suka zuba mu su wainar sannan suka d'aure kwanukan su ka mu su sallama, kasancewar akwai rairai kafin su hau titi ya sa Kaltume ba ta hau ba ta na jiran Khadija ta fita daga rairain, cikin rashin sa'a wani tsoho ya taho zai shiga shagon d'inkin shi, tana murd'awa sai kuwa ta bige tsoho ya fad'i, dukan su suka fad'i k'asa da azama aka kawo mu su d'auki, duk da masuburbud'ar zafi (shagama inji salim, salansa inji mak'obtanmu) ta tab'a ba bai dame ta ba, tsohon mutane data bige shine a gabanta, kuka take ta na tambayar tsohon bai ji ciwo ba, duk da k'afar shi da ta buga yaji ta na masa ciwo haka ma gwiwar hannun shi daya fad'a samanta, amma sai ya nuna ba komai kawai ta tafi, cikin abokan mahaifin nata ne ya lura da hannun shi har jini ya d'an fara fitowa ta cikin riga, nan aka ce a kai shi likita Khadija tace ita ma za ta je, da k'yar suka lallab'a ta dan ta tafi gida, amma duk ta d'aga hankalinta sosai sai hawaye take, wani daga cikin dattawan ne yace "Kinga Khadija ki daina kuka, zai samu sauk'i, kinga ciwon ai kad'an ne, Allah ne ya aiko dole hakan ta faru, yanzu kije gida ki huta, zuwa gobe sai kije godanshi ki dubo shi ko, hakan ya yi?" D'aga kai ta yi alamar eh, sai da ta hau moton Kaltume ma ta hau sannan tace "Ina ne gidan?" "Gidan ya na nan yan banana wajen masallacin ladan." Ta na shan majina ta wuce zuciyar ta ba dad'i ko kad'an, tun da suka je gida daf da magrib sun samu duk yan uwan ta sun dawo daga uzurirrikansu ban da Naseer dake karatu a *France*, yanda ta shigo tana kumboro baki ta na murzar ido ta cire gilashi ne ya sa Ashir zaburowa ya kamo hannun ta yana fad'in "Auta lafiya? Me ya same ki kike kuka?" Zaunar da ita ya yi ya karb'i gilashin ya maida mata ya kalli Kaltume yace "Umma waya tab'a ta?" Cikin taushin murya Kaltume tace "Wani tsoho ta bige, ita ma kuma ta fad'i, amma duk ta damu." Bashir da Mansur a zabure suka matso Bashir na fad'in "Subhanallah, auta ba ki ji ciwo ba?" Dukansu duba jikin ta suke ko sunga ciwo amma shiru, Mama na gefe tana kallonsu ta yi shiru, a hankali Khadija ta janye siket d'in ta ta nuna musu in da take jin zafi, wajen har ya yi bak'i ai sai suka zabura da ganin wannan d'an ciwo, da gudu Habeeb ya wuce d'akin shi ya d'auko maclean dan a shafa mata, tuni kuma Bashir da Ashir sun umarci matansu da su d'auko musu suma, sai ga abun wanke hak'ora har hud'u a gaban su, nan dai suka shafa mata akayita lallab'a ta har zuwa dare. Kwance take a d'akin ta cikin bargo yayin da suk yan uwan ke kewaye da ita sai kanta dake kan k'afafun mama, d'aya hannunta na sak'ale cikin hannun Habeeb ya na shafawa, sai mama dake shafar kanta Ashir kuma na karanta mata wani littafi mai sunan *magana jari*, lumshe ido take sosai ta na so tayi bacci, janyo hannun ta tayi daga hannun Habeeb ta tusa shi ta k'asan gilashinta ta murza idon ta tana turo baki gaba, ganin ta rufe ido ya sa Ashir matsowa kusan fuskarta yace "Auta." Bud'a ido ta yi ta kalle shi, cikin murya k'asa k'asa yace "Albishirinki." "Goro." Ta fad'a ta lumshe ido, d'orawa ya yi da "Na biya mi ki kujerar hajj, tare da Mama za ku tafi wannan karan insha Allah." Zunbur ta tashi zaune tace "Da gaske yah Ashir? Kai amma naji dad'i sosai, nagode." Da k'arfi mama ta maida kanta akan cinyar ta tace "Dan Allah ki kwanta ki yi bacci ko muma mun samu mu rintsa." Daddab'a ta ta ci gaba da yi har bacci ya d'auke ta, addu'a mama ta shafa mata Mansur ya cire mata gilashin ya aje mata gefenta kafin suka kashe mata wutar d'akin suka fita, har ga Allah wannan kulawar da suke nuna mata Mama tasan ta yi yawa, haka kuma matar Bashir da Ashir suna jin haushin hakan, saboda kai tsaye suna nuna musu farin cikinta yafi nasu, kulawar da suke nuna mata basa nuna musu kwatankwacin ta, shi ya sa mama ke fatan su rage ko dan kasancewar ta ya mace, dan ma ita d'in yarinya ce mai son aiki da kazar-kazar. *Allah ka k'ara mana k'oshin lafiya, sis Alawiyya Allah ya baki lafiya.* 12/01/2020 Γ 22:18 - πππ: ππππππππππ *KALLON KITSE* _(Ake wa rogo)_ ππππππππππ _SAMIRA HAROUNA_ *Littatafan marubuciyar* *1* _KAUSSAR_ *2* _D'AUKAR FANSA_ *3* _BA SO BANE_ *4* _AUREN HAD'I_ *5* _SANIN MASOYI_ *6* _JIHADI_ *7* _K'ANGIN RAYUWA_ *8* _ITACE K'ADDARARMU_ *9* _KAWU NA NE_ *10* _MAATA_ *11* _KALLON KITSE..._ *SADAUKARWA GA* _MATAN FARKO_π§πΌ *(UWAYEN GIDA)* πΈπ¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S* _(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_π€π€ ```Fatan alkairi masoya``` _Bismillahir rahamanir rahim_ *10* Washe gari da safe Khadija ta shirya su ka tafi tare da Habeeb ya kai ta gidan tsohon da ta bige, sai da aka mu su kwatance su ka isa gidan, a k'ofar gidan Habeeb ya tsaya ita ta wuce ciki ta na rabka sallama tun daga soro, kasancewar safiya ce kusan matasan gidan ba su riga sun tafi harkokinsu ba, dan wasu ma su na cin d'umamen tuwo ta same su, izini aka mata ta shiga ciki, gaba d'aya ta had'e tace "Ina kwanan ku." "Lafiya k'alau." Aka amsa mata, d'orawa ta yi da "Antashi lafiya." "Lafiya lau mu ka tashi." "Ya mai jiki?" Ta fad'a ta na d'an kallon tsohuwar, da fara'a tsohuwar tace "Mai jiki da dama." Da mamaki tsohuwar ta kalleta a nutse tace "Sannu ko yan mata?" "Sannu Mama." Ta fad'a da murmushin ta, tsohuwar ce tace " Sai dai kuma ban shaida ki, gashi na ji har ki na tambayar jikin malam ko?" Da k'ayataccen murmushi tace "Eh mama, na zo duba jikin su ne, ba za ku shaida ni ba dama, ni ce hatsarin nan ya faru tare da ita." "Ayyah! Sannu ko, mai jiki ai da sauk'i, yanzu ma haka fitowa ya yi zai fita shago, babban yaron na shi ne ya hana shi yace ya koma ya kwanta, ya na ciki, muje na rakaki ki gan shi." Ledar hannunta ta sake mayar da ita d'aya hannun saboda nauyin ta kafin ta wuce, ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117