Skip to content

Chapter 81

Chapter 81

Kallon Kitse Book One Complete Hausa Novels 1,203 words 0 views Progress saved
Download Book

wannan baiwar da ka min, Allah ka tabbatar min da alkairi." Saukowa ta yi daga kan gadon ta shiga wanka, da sauri ta k'arasa ta fito ta saka kaya ta yi sallah, gyalen ta ta saka ta d'auki jaka tasa takalma ta fito, da kallo Mama ta biyota tace "Ke kuma ina zuwa haka da rana patsal-patsal haka?" Kasancewar duk matan gidan na d'akin ya sa ta matsa kusan amaryar Ashir tace "Duk cikin nan ke ce babba, dan haka ke ce zan iya fad'awa dan ba na jin kunyar ki." Rad'a ta mata a kunne kafin ta fice daga d'akin da sauri, dariya amaryar Ashir ta yi ta kalli Mama tace "Mama wai kinsan me?" "Sai kin fad'a mana zan sani." Cewar Mama, saida ta jinjina kai tace "Ai Mama sai kin bani goron albishir kafin na fad'a." "Ita goron ki ka bata kafin ta fad'a mi ki? Ai naga kyauta ta fad'a mi ki." Dariya matar Bashir ta yi tace "To ai Mama shugaban k'asa ya hana aikin banza." Tab'e baki Mama ta yi tace "To can ku k'arata ku da shugaban k'asar na ku, ku rik'e sirrin ku ba na son ji." Dariya amaryar Ashir ta yi tace "Mama Khadija fa cewa ta yi ta na zargin ta na da juna biyu, yanzu ma za ta je asibiti ne a tabbatar mata da gaskiya." Waro ido Mama ta yi tace "Ke *Safiya* ba na son k'arya, da gaske ki ke?" "Wallahi kuwa Mama haka ta fad'a." Wani murmushin farin ciki Mama ta yi kafin tace "Allah ya tabbatar da alkairi, *wani hanin ga Allah baiwa ne*." "Hakane Mama." Suka amsa da shi. Khadija na fita cikin sauk'i ta samu adaidaita sahu ta kai ta *Clinique tattali*, kamar yanda ta yi tunanin kam hakane ta faru, dan kuwa ta samu k'awar ta ce akan aiki mai sunan *Maryama*, kasancewar babu mutane a asibitin ya sa suka fara tab'a hira kafin ta fad'a mata abin da ya kawo ta, nan ma saida aka sha wata hirar kafin ta mata gwajin fitsari, ko da ta duba dan ta ga sakamakon Khadija tace"Dakata." Kallon ta ta yi ita kuma tace "Kawai ki min murmushi idan har gaskiya ne tunani na, in kuma babu to ki had'e rai." Dariya Maryama ta yi tace"Kaga wani sabon gwajin ciki kuma, to bara na gani." Ta na dubawa kam ta ga ciki dai ya tabbata, haba wa ai sai ta washe mata hak'ora tace "Ke kiyi farin ciki, wallahi ciki ya tabbata, kai Khadija na miki murna wallahi." Rumgume juna su ka yi cikin farin ciki, ba ta jima ba ta mata sallama ta bar asibitin, daga nan kuma gidan k'awar ta ta wuce Kaltume dan sanar da ita, da shigarta gidan ta ji sun k'ara birge ta abun sha'awa, dan farko *Madina* kishiyar Kaltume ta so ita ma ta yi kalar nata iskancin, sai dai ina tuni Kaltume ta nuna mata ruwa ba sa'an kwando bane, sannan shi kan shi mijin na su *Alhaji Ibrahim* yasan da ya fad'a tarkon Kaltume da babu mai k'watar shi idan ba ubangiji shi ba, a k'arshe dai Madina ta fahimci tazara mai tsayi ce tsakanin su da ita dole ta hak'ura, musamman da ya zama babu mai iya bata shawara ga yanda za ta mu'amulanci rayuwar gidan ta, cikin sauk'i sai suka zauna lafiya kamar ba kishiyoyi ba, yanzun ma saida suka gaisa sosai ita da Khadija har suka fara tab'a hira kafin Kaltume tace su je daga ciki, nan fa ta fad'a mata ta na da ciki kar kuso suji bud'ar da Kaltume ta rabka har k'ofar gida, tsabar nuna farin cikin ta ya sa nan take ta bawa yara kud'i tace su siyo alawa mai tsada su rabawa yara, anjima kuma da yamma za ta yi fanke na sadaka da godiya ga Allah, Khadija dai kallonta kawai tale ta na k'ara k'aunar Kaltume, tabbas a rayuwa bata da yar uwa mace amma Kaltume ta zame mata komai, har kusan yamma kafin ta bar gidan saboda kiran ta da Mama ta yi, haka ta koma gida nan ma Mama da aka k'ara tabbatar mata gaba d'aya gida ya d'auka Bilal zai samu k'ane ko k'anwa, in da Mama ke binshi da gwalo ta na fad'in "Tuzurun wofi, yanzu dai sai naga k'afafun uban wa za ka hawa ko kuma wanda zaka wa shagwab'a, dama can rashin ganin wani ne a gaban ka ya sa ka wannan iskancin." Shi kam cewa ya ke to sai me, ai k'ane za'a mi shi dan haka bai damu ba, kuma idan ya na son hawan k'afafu ga nata nan zai hau, da haka har 'yan biyar su ka zo suma suka d'ora nasu farin cikin ana addu'ar Allah ya sauketa lafiya. *Mu ma dai munce ameen.* Kamar kullum Usman ya je gaishe da iyayen sa, kuma kamar yanda ya saba riska yau ma malam baya nan, sai dai ya bar sak'on wannan ruwan addu'ar a bashi ya sha, saida ya shanye Hajia ta fito daga ban d'aki tace "Tashi kaje ka yi wanka ruwa na nan na had'a ma ka." Kasa magana ya yi saboda mamaki da kuma rashin sanin abin da zai fad'a, saida ta maimaita da "Ko ba ka ji ba ina magana?" Saida ya gyara zama ya kalli jikin shi da kyau yace "Amma Hajia na yi wanka fa, wane irin wanka ne zanyi yanzu kuma?" "Ka tashi ka shiga lokaci tafiya yake." Marairaicewa ya sake yi yace "Amma Hajia wai dan..." Katse shi ta yi da "In za ka tashi ka tashi kafin ka b'ata min rai." Tashi ya yi kamar zai k'urma ihu saboda haushi, ya rasa irin wannan sabon al'amari na iyayen shi, haka ya tub'e kayan da ya sanyo yanzun ya yi wanka da wannan hakukuwan na magani, haka ya sanyo kayan ya fito duk ruwan jikin shi sun tsaya a kayan, ya na fitowa Hajia kuma ta bashi damammiyar fura da maganin jiya a ciki, saida ta masa jan ido yasha dan cewa ya yi jiya baiyi bacci ba, hakan ya sa ta bud'e mi shi ido sosai sannan ya sha, wata 'yar kwalba ta d'auko bak'a mai d'auke da maganin *jibda* a ciki, da kan ta ta lak'ato a hannu ta shafa mi shi a wuya zuwa kai da hannuwan shi har zuwa damatsenshi, bashi ta yi tace ya d'iba ya shafa a cikin shi har zuwa k'irji, kamar zaiyi kuka ya kalle ta yace "Hajia wai duk wannan na miye haka? Wannan abun nan amai zai saka ni, sam warin shi babu dad'i." Shiru kawai ta yi ba tace komai ba dole ya shafa yanda take so, mik'ewa ya yi yace "Hajia ko za ki bani magungunan sai ki nuna min yanda ake sha, ina ga kamar hakan zaifi ko?" Kallon shi ta yi tace "Alhaji, kai ka haife ni ko ni na haife ka?" Cike da ladabi ya rusuna yace "A'a Hajia ki yi hak'uri, ban fad'i haka dan b'ata ran ki ba." "To ka wuce ka tafi in da za ka je kawai, sannan ba na so ka fad'a wa wani ko wata batun magungunan nan, ko da kuwa matan ka ne ban yarda ba, kaji ni ko?"

Table of Contents

Chapters

117 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117