Chapter 96
Chapter 96
*11* _KALLON KITSE..._ *SADAUKARWA GA* _MATAN FARKO_ π§πΌ *(UWAYEN GIDA)* πΈπ¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S* _(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_π€π€ ```Fatan alkairi masoya``` _Bismillahir rahamanir rahim_ *35* "Zan d'an shiga ciki na kwanta ne saboda na gaji, ki ci abincin kawai dama ni na k'oshi." Sake juyawa ya yi zai wuce tace "Amma yau d'akin ka za ka kwana ne?" "Eh." Ya fad'a a hassale tare da juyowa ya na kallon ta ya ci gaba da cewa "Kuma ke ma ina so ki kwanta d'akin ki dan ba na son takura." Da mamaki tace "Takura kuma? Ni ce ma zan zama takura a gare ka? Babban mutum wai lafiyar ka k'alau." Ajiyar zuciya ya sauke irin ta takura masa d'in nan kafin yace "Lafiya k'alau, na yau kawai na ke so ki bar ni na kwanta ni kad'ai, ki yi hak'uri." Ya fad'a ya na wucewa ciki ya barta nan, mamaki ne ya kama ta sosai da tunanin ko lafiyar shi? Ita dai a saninta lafiya lau suka je gida, amma daga lokacin da ya shiga d'akin malam ba ta ma san da tafiyar shi ba sai da taji kamar su na waya da Hajia duk da dai ba ta da tabbacin da shi su ka yi wayar, ita ma d'akin ta ta nufa ta cire kaya ta yi wanka kafin ta ci abinci ta kwanta, sam ba ta samu wata damuwa ba wajen baccin ta, dan kuwa ba jimawa baccin ya d'auke ta. A wajen Usman kuma kasa bacci ya yi ya na tunanin abin duniya, da farko dai da kunya ce ke neman sa shi yin k'asa a gwiwa, amma kuma saiya duba ya ga ai ba a sanin shi bane komai ya faru, sannan bai saki matar shi ba bugu da k'ari ta na d'auke da cikin shi, da haka kuma sai ya ji ya ma k'agu gari ya waye ko ya sake komawa wajen Dije, ba kuma zai gushe ba har sai ta dawo gare shi, saboda fatan dacewa ya sa ya d'auro alwala ya shiga fad'awa Allah kukan shi tare da neman taimakon ubangiji. *Washe gari* da safe d'aurin aure, sammako sosai Usman ya yi ya hallara d'aurin auren bayan yace wa Haseenah ta yi k'ok'ari taje da wuri ita ma, haka ya fita kamar shine angon cikin babbar riga da 'yar ciki farare, ya na isa a k'ofar gida ya tsaya saboda mutanen da ya samu a wajen, nan su ka shiga gaisawa da mutane har lokacin da motar Naseer ta kutso cikin taron jama'ar, mazauni aka samarwa da motar kafin Mama ta bud'e ta fito daga ciki, Usman na ganinta ya tafi da azama dan kwasar gaisuwa sai ya ga Khadija ta fito a matsayin dreban da ta tuk'o motar, tsaye ya yi ya kasa k'arasawa saboda haushi, tabbas yasan ta na fita da gyale sai dai yau ne ya fara jin haushin haka, domin kuwa ta na fitowa gyalen ma a kafad'ar ta yake, duk da doguwar rigar shadda ce jikinta wacce ta fito da d'an cikin ta na wata biyar, amma dai baiji dad'i ba duk da ya ga sai gyara gyalen take, har saida su ka zo daf da shi kafin ya sunkuya ya gaishe da Mama ta amsa cikin sakin fuska, wucewa Mama ta yi shi kuma ya mayar da kallon sa kan Khadija da ita ma shi take kallo yace "Ke ba ka iya gaisuwa ba ne ko me?" Cikin tsiwa tace "Um ban iya ba, ko ka koya min ne?" Gyara tsayuwa ya yi ya na k'ara sab'a rigar shi a kafad'a yace "Uwar yarima wai yaushe ki ka raina ni ne haka?" Ta na kallon idon shi tace "Tun ranar da ka fara wulak'anta ni saboda ka yi amarya." Wani kallo ya mata kafin ya d'an saci kallon mutanen da ke wajen yace "Yanzu ko albarkacin mutanen nan ba zan ci ba na ga murmushin nan na ki mai saka ni bacci." 'Yar siririyar dariya ta yi tace "Toh fa Alhaji mai babbar riga, kai da za ka je d'aurin aure kuma me ya had'a ka da bacci? To ka farka idan mafarki ka ke, kai da sake ganin murmushin Nana Khadija kuma sai dai ko a lahira, a lokacin da aka min umarni da na shiga aljanna, to zan iya juyowa na kalle ka dan na ma ka bye bye, to fa zai iya yiwuwa a lokacin ne za ka ga murmushin." Shi maganar ta dariya ma ta bashi, da sauri ya rik'o hannunta ya matso daf da ita yace "Ki na so ki ce ni kuma zan zauna har sai kin riga ni shiga? Ko kuma nufin ki ni ba ma zan shiga ba?, ai k'afar ki k'afa ta insha Allahu, in kuma ba haka ba to sai dai ki same ni a ciki kewaye da sabbin mata na." Fizge hannunta ta yi tace "Ka na dukan nawa ne kuma ka ke tunanin za ka shiga aljanna." Wucewa ta yi ta bar shi nan tsaye ya na ta dariya shi kad'ai, Murtala ne ya k'araso wajen shi yace "Mijin Khadija lafiya ka ke dariya kai kad'ai?" Hararan shi ya yi yace "Ni kad'ai ka gani a wurin? Ba ka ga wacce na gani ba." "Na gani kam, ince dai kun sasanta za ta koma?" Kallon shi ya yi sosai yace "Da alama fa sai ka tayani bata hak'uri, ran 'yar aljanna ya b'ace sosai." Zaro ido Murtala ya yi yace"Wa? Ni! Sam ba dani ba, kai dai da ka mata laifi ka bata hak'uri amma banda ni." "Au! Yanzu ka na nufin ba za ka tayani ba kenan? To nagode, ai na d'auka zan iya yin zaune gida ma kai kaje har sai ka dawo min da ita, ashe ba haka bane." "A'a ni ba haka na ke nufi ba, kasan dai maganar nan ta manya ce ba iri na ba, kuma tsakanin ka da Khadija ma ai ba ta b'aci." Ba jimawa da shigar Khadija mutane aka fito dan tafiya wajen d'aurin auren, daga ciki har da Mama dan dama d'aurin auren take son samu, nan aka shiga motoci aka wuce d'aurin auren, Khadija na zaune d'akin Hajia Nura ya shigo da sauri ya na kiran sunan Hajia, ya na ganin Khadija yace "Uwar gida yane, ke ba ki je d'aurin auren ba?" Hararan shi ta yi tace "Wa? Allah ya sawak'e, me zanje na yi a d'aurin auren kishiya, ai ina daga nan ina aika mu ku da addu'a." "Yawwa hakan ma ya yi ai, addu'ar ita mu ke buk'ata ai." Cewar Nura ya na kallon Hajia da ta fito daga d'aki, cikin k'aguwa yace "Hajia takalma na da na baki jiya na ke nema." Ledar hannun Hajia ta mik'o mi shi tace "Dama nasan su za ka nema ka ke min wannan kiran." Bud'ewa ya yi ya saka takalman kafin ya juya zai fita yace "Hajia ku fara tausar min k'irjin ta kafin na dawo." Haka suka wuce wajen d'aurin aure gidan waliyin Choukra, kuma ba'a b'ata lokaci ba waken yin abin da ya kai kowa wurin, nan aka d'aura auren *Nura Ali* da amaryarshi *Choukra Sabi'u*, bayan taya juya murna da farin ciki ne abokan ango su ka nufi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117