Chapter 2
Chapter 2
ta ya kwantar da ita a kan k'irjin shi ya na ci gaba da shafa ta ya na fad'in "Abu d'aya da banji dad'in shi ba, shine rashin samun yardar ki, na yi mamaki da takaici da ki ka kasa fahimta ta, ban ji dad'in yanda ki ka rufe idon ki ba ki ka k'i saurara ta, na so ace kinfi kowa sanin mijin ki, na so ace kin fahimci zan k'ara aure ne ba dan na gaji da ke ba ko dan na wulak'anta ki ba, kamar yanda na sha fad'a mi ki kuma yanzu ma zan sake jaddada mi ki, Khadija ba na da burin had'a ki da wata mace a duniyar nan, kin gama min komai a rayuwa ta, kin mayar da ni cikakken namiji, kin bani farin cikin da duk na ke buk'ata, hankali na ya na kwanciya idan har ina tare da ke, idan har ki ka ga na yi aure to Allah ne ya tsare haka, kuma kinsan duka abin da Allah ya hukunta babu mahalukin da ya isa ya tsallake shi ko ya canza shi, amma tun da na ga kin kasa fahimtar hakan, maganar aure na rushe ta saboda farin cikinki, dan dama ba wai zanyi bane dan ina son haka d'ari bisa d'ari, zanyi ne saboda sunna ne, kuma ina sha'awar samun ladar da ake samu ta ciyarwa." _Me ku ka ce masoya, ta yi farin ciki? Ko kuma ta hak'uri ayi kawai?._ *Sai mun had'u a shafi na gaba.* 26/12/2019 Γ 11:32 - πππ: ππππππππππ *KALLON KITSE* _(Ake wa rogo)_ ππππππππππ _SAMIRA HAROUNA_ *Littatafan marubuciyar* *1* _KAUSSAR_ *2* _D'AUKAR FANSA_ *3* _BA SO BANE_ *4* _AUREN HAD'I_ *5* _SANIN MASOYI_ *6* _JIHADI_ *7* _K'ANGIN RAYUWA_ *8* _ITACE K'ADDARARMU_ *9* _KAWU NA NE_ *10* _MAATA_ *11* _KALLON KITSE..._ *SADAUKARWA GA* _MATAN FARKO_π§πΌ *(UWAYEN GIDA)* πΈπ¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S* _(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_π€π€ ```Fatan alkairi masoya``` _Bismillahir rahamanir rahim_ *2* D'agowa ta yi daga jikin shi ta na kallon shi a dishi-dishi, karb'ar gilashin ta ta yi da har yanzu ya ke hannun shi ta mak'ala a idon ta, tarau ta gan shi ta ciki dan haka ta kamo hannun shi ta na murzawa tace "Ka sa na ji kunyar kai na, Abban Bilal na hak'ura, ba zan so ka fasa aure ba a kai na, idan na yi haka na zama azzaluma kuma mai son kan ta dayawa, sannan fasa auren na ka zai iya janyo matsaloli da dama, daga ciki kuwa har da dangin ka, dan za su zarge ni, ni kuma ba zan so haka ba, dan haka na amince ka k'ara aure, na san ba za ka wulak'anta ni ba, duk da dai ina d'an jin tsoron yan matan yanzu, amma ina fatan ka mana zab'i na gari, ba zab'en tumun dare ba." Murmushin gefen labb'a ya yi yace "Na riga da na yanke hukunci, na san kin amince ne saboda kawai ki faranta min rai, ni kuma ba na son tursasaki a kan abin da ba kya so, dan haka ya wuce kawai." Da sauri ta gyara zama ta na fuskantar shi tace "Haba aljanna ta, ni fa na ce na amince, wallahi babu takura a ciki, wani k'aramin rashin fahimta ne, kuma sai ga shi cikin ikon Allah fasihi kuma nagartattacen miji na ya fahimtar da ni, dan haka in ba so ka ke na maka kuka ba kawai ka amince." Yanda ta k'arashe maganar cikin shagwab'a ya birge shi, dan haka ya rumgumo ta jikin shi ya na dariya, cikin so da k'auna ya ci gaba da rarrashin ta tare da saka mata albarka, tambayar ta ya yi "To yanzu ina so ki fad'a min duk abin da ki ke buk'ata, ni kuma insha Allah zanyi mi ki shi a matsayin tukuici da kuma fad'an kishiya." Kasancewar ta mace mai yawan shagwab'a da son jiki ya sa ta turo baki gaba ta kwanta a kafad'ar shi tace "Kaji ka da wata magana, ai ni yanzu ba kai ne za ka min hidima ba, ni ce ma zan bayar da tawa gudunmuwar." "Ban yarda ba, sai kin fad'a, in ba haka ba kuma zan kama ki ne." Yanda ya yi maganar cikin sigar rausaya ya sa ta tashi ta nufi d'akin ta ta na fad'in "Na k'i wayon, ka kamani d'in." Ya na jin haka ya tashi da gudu ya nufe ta, ita ma a guje ta k'arasa shiga d'akin, kasancewar Bilal na wajen kakannin shi (iyayen Khadija) ya sa su ka saki jiki sosai su ka more rayuwar su, dan dama kusan kullum haka su ke. *Washe gari* kamar kullum misalin *09:30* su ka gama shirin fita, har farfajiyar gida su ka isa tare, ita ma kuma cikin shirin fita ta ke, sai da ya shafi lallausan kumatun ta tare da sumbatar ta kafin yace "Ni zan wuce, ki kula min da kan ki, sannan ki gaishe min da su Mama, tun da ba za ki bani damar da zan kai ki da kai na ba bare na gaishe su." Masha Allah, duk da cikin gilashi ne ta waina idon ta, amma bai hana su d'aukar hankalin Usman ba, saboda girman idon da kuma farin su tamkar madara, cikin wasa da idon ta ne tace "Na shiga uku, da alama sai an shekara d'ari ka na min gorin wannan maganar." "Ai dole ne, dan na lura kamar ba kya so na je na kwaso albarka wajen Mama, sannan na sake mata godiya da ta bani ke." "Gashi kuma ba kya gajiya da godiya kullum." "Ni kam ina zan gaji da godiya, duk wanda ya baka yar sa ka aura ai ya gama ma ka komai, bare kuma mata irin ki Khadija, ai har duniya ta nad'e ba zan daina mu su godiya ba wallahi, dan na san sun fini sanin ki, amma kuma hakan bai hana su ka rabu da ke ba su ka bani ke, duk da kuwa sun san ba zan tab'a rabuwa da ke ba in ba mutuwa ce ta raba mu ba." Ajiyar zuciya ta sauke tace "Idan har na biye ma ka, to hak'ik'a zan tabbata anan ban tafi in da zan je ba, dan haka sai an jima, nima ka gaishe min da Mama na da Abba na, tun da ka k'i bani damar bin ka bare na gaishe su." Ta na fad'a ta juya ta na dariya shi kuma ya na fad'in "Au! Ramawa ki ka yi? Shikenan ai zan kama ki." Gwalo ta masa tace "Ka kamani d'in, kafin nan na san in da na kai." Wata tsandareriyar mota ta shiga bla (bleue) shi ma haka, sai dai ta shi bak'a ce, kowa hanyar da za ta sada shi da na shi iyayen ya nufa, dan su dama a *zarya* su ke, bayan masallacin *sahaba*, Khadija gaba ta yi saboda gidan su na gaban sabon gidan mota na *Rimbo*, shi kuma Usman gidan iyayen shi ya na nan *sabon gari* a 'yan *banana* (π€Έββaradu unguwar mu). Ko da ya isa mahaifiyar shi kad'ai ya samu a gidan, dan haka su na gaisawa ya d'auko maganar auren shi, tambayar da ta fara mi shi ita ce "Khadija ta sani?" "Eh Mama, ta sani, kuma ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117