Chapter 24
Chapter 24
Kabir ta sake saurin sunne kan ta cikin k'irjin shi ta cakumo rigar shi ta rufe fuska da ita, dariya su ka mata Kabir yace "Matar yaya wai ba dai sati biyu da ya yi baya nan ne ya saki wannan farin cikin ba kamar ya yi shekara?" Ita kam kunya ce ta sake rufeta ta kuma tusa kan ta cikin k'irjin shi dan ba za ta iya d'agowa su had'a ido ba, murmushi Usman ya yi ya na shafa bayanta yace "Dallah malam ka wuce ka yi abin da na saka ka, sai ka takura min yar..." Shirun da ya yi ya sa Khadija d'agowa ta kalle shi, had'a goshinsu ya yi wuri d'aya yace "Yar yarinya ta na ke nufi." Cikin dariya Kabir yace "To sai anjiman ku amare, sai ka shigo d'in, amma ni banga alamar za ta barka ka fito ba." "Saboda me?" Cewar Usman ya na kallonshi, shafa kan shi ya yi yace "Ai na ga ta yi kewarka ne sosai." Wannan maganar ce ta sa Khadija juyawa da k'arfi za ta koma d'aki Usman ya fizgota ta fad'a kan shi, dariya su ka saka Usman ya juyo ya kalli Kabir yace "Kai wai za ka fice min ko sai na raka ka ne?" Sosa k'eya ya yi yace "To ai ba ka ban tsaraba ta bane, ko ka manta yanda mu ka yi da kai kafin ka tafi?" Sakin Khadija ya yi ya aje jakunkunan hannun shi ya tunkari Kabir ya na fad'in "Ina zuwa, bara ka gani d'an hancin uwa kai." Maimakon ya fita daga gidan sai ya daka da gudu ya yi hanyar ban d'aki ya na dariya ya na fad'in "Amma fa sai da na fad'a maka banda mai a moto na, kace idan mu ka zo za ka ban kud'i na saka, ka bani kawai sai na tafiya ta na barku ku soyewar ku." Dawowa ya yi ya kama hannun Khadija ya sunkuya zai d'auki jakunkunan ta tu saurin karb'a ta na fad'in "Bara na shigar ma ka da su." Kabir ne ya sake fad'in "Dan Allah ka fito ka sallame ni kafin ka shiga d'akin nan, dan bansan me zai faru ba idan ka shiga." Juyowa ya yi ya kanne shi Khadija kuma k'arasa shiga ta yi saboda kunya, suna shiga Usman ya tsaya ya na k'arewa d'akin kallo, komai a d'akin kalar kayan d'akin ta ne ma'ana fari da maron, sai telebijin da k'aramin teburin tsakar d'aki ne kad'ai bak'ak'e, ajiyar zuciya ya sauke ya kalle ta yace "Duk wannan shirin na zuwa na ne?" Cike da kunya tace "Eh mana, sati biyu ba ka gidan ka, ya na da kyau ka tarar da sabon abu dama." Hannunshi ta kama tace "Muje ka cire wannan kayan ka yi wanka, idan ka fito sai ka zo ka ci abinci." "Na ci abinci ko ki ba ni abinci?" Ya fad'a ya na tsare ta da ido, murmushi ta yi ta kalle shi tace "Duk yanda ka ke so ai girman ka ne, ka cancanci fiye da haka ma." Wani basaraken murmushi ya yi ya nufi d'aki yace "Godiya na ke Nana Khadija." Zasu shiga d'akin Kabir ya d'aga murya daga waje yace "Kai fa na ke jira, wallahi yah Fodio kar ka manta da ni anan waje ka shiga harkar gaban ka, kasan dai nima matar ce da ni ko." Shima d'ago muryar ya yi yace "Naji me mata, amma aljihunka ba ka da kud'in da zaka saka mai a moto, to waye zai ciyar maka da matar kenan, ko dai hak'uri take ci?" K'arasa shiga d'akin su ka yi, k'amshin da ya daki hancin shi ne yasa shi lumshe ido, a hankali ya bud'a ido ya sauke akan gadon da shi ma zanin da aka shinfid'a sama fari da maron ne, kallon ta ya yi yace "Khadija kin wahalar min da kan ki dayawa fa." Murmushi kawai ta yi ba tace komai ba, zai fara cire kaya Khadija ta nufi wajen wata k'aramar jakar ta ta hannu ta d'auko ta fito, a tsakar gida ta samu Kabir ya na ta shawagi shi kad'ai, bud'a jakar ta yi ta ta ciro yan jikka jikka har guda biyar mik'akk'u ta mik'o mi shi tace "Gashi wai a baka." Da mamaki ya kalli hannunta yace "Inji shi?" "Eh." Ta fad'a da murmushi, jim ya d'anyi kafin ya karb'a, dan shi dai a iya saninshi Usman na k'ok'ari da su sosai wajen yi mu su buk'atunsu, amma kyauta irin haka dai ta shiga tsakanin shi da su gaskiya da wahala, saboda shi kan shi ma ai ba k'arfi bane da shi, da wannan mamaki yace "Ki masa godiya matar yaya, nagode sosai, ni na wuce." "Amma ai da ka jira shi sai ku ci abinci ko." Cike da zolaya yace "Me ki ka dafa ne? Kinsan ni fa ina son abu mai dad'i." Dariya ta yi tace "To ka tafi tafi kawai, dan nasan abin da na dafa ba lallai ya birge ka ba." "Da alama dai ba kya so na ci ne, to na hak'ura ma bana ci." Jin motsin Usman ya sa ta dawo ciki, da sauri ta karb'i abun tsane ruwan hannun shi ta d'auki kwandon sabulu ta kai ban d'akin ta dawo ta cika bokiti da ruwa ta kai mi shi, kallonta ya yi yace "To na shiga na yi ne? Ko kuma madam ce ke da wannan alhakin?" Dariya ta yi kawai ta kama hannun shi su ka nufi ban d'akin, shine ya fara shiga ita kuma ta tsaya baya tana tunanin ta mi shi wankan kamar yanda k'awar ta tace? Ko kuma dai ta bar shi ya yi da kan shi, wata zuciyar ce tace ma ta to ai mijin ki ne, ya sanki kin san shi, dan haka babu kunya a wannan fanni tsakanin ma'aurata, shiga kawai ta yi ta fara gurza shi soso da sabulu, haka su ka fito ta gama shirya shi cikin k'ananan kaya na kanti, sai dai la'asar ta matso ya sa shi yin alwala ya nufi masallaci ya fara sallah, ya na dawowa su ka ci abinci tare kamar yanda su ka saba, daga kan teburin ya kashe ta da wani kallo yace "Khadija." "Na'am." Ta d'ago ta na kallon shi, cikin taushin murya da nuna buk'atar shi yace "Kinyi kewata kuwa?" Da idon ta nan masu kama da na mai jin bacci ta kalle shi tace "Dan ba ka gan ka akan gado na bane ka fad'i haka?" Sai da ya d'an lashe baki yace "Da gaske? Kenan kema yanzu haka ki na jin abin da na ke ji?" Da gangan ta d'auki kofin (cup) lemun shinkafar da ta yi ta zuba a rigarta a tsakiyar maman ta tana kallon shi tace "Ya ma fi wanda ka ke ji." Taso da ita ya yi tsaye ya d'aga kan shi ya na kallon ta ya soma cire mata mab'allan rigar ta har sai da ya rabata da ita, rigar nonon da ta kamata ya cire ita maya jefar kafin ya sa harshe ya na lashe jikinta in da lemun ya zuba... *gyara kimtsi*. *Misalin* 05:54, su na kwance akan gado ya kalleta yace "Khadija, kin mayar da ni babban mutum, ina
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117